Hira Mai Ratsa Zuciya Daga Majalisar Annabi (SAW)

Tags

Hira Mai Ratsa Zuciya Daga Majalisar Annabi (SAW)

Wata rana Manzon Allah (SAW) yana zaune tare da Sahabbansa, sai ya fara tambayar su daya bayan daya, sai ya fara da Sayyidina Abubakar 'yantaccen wuta

Yace: "Yaa Abubakar! Me kake so a duniya?

Sai Sayyidina Abubakar yace: abinda na fi so a duniya_

1: zama a gaban ka,

2: kallon ka,

3: ciyar da dukiya ta gare ka

Sannan Manzon Allah ya koma wajen Sayyidna Umar dan Khaddabi mai abin mamaki

Manzon Allah (Saw) yace: yaa Umar! Me ka fi so a duniya?

Sai Sayyidna Umar yace : abinda na fi so_

1: a mini umurni da kyakkyawan aiki ko da a boye ne,

2: a mini hani da mummunan aiki ko da a bayyane ne,

3: da kuma fadin gaskiya ko da tana da daci.

_Sannan manzon Allah ya koma wajen Uthman dan Affan, yace masa: "yaa Uthman! Me kafi so a duniya?_

_Sai Uthman dan Affan yace: abinda na fi so a duniya_

1: ciyar da abinci ga mabukaci,

2: yada sallama,

3: yin sallah cikin dare a lokacin mutane suna bacci.

  _Sannan Manzon Allah (Saw) ya koma ta wajen Aliyyu dan Abi Daalib, yace masa: "yaa Aliyyu! Me ka fi so a duniya?_

  _Sai Sayyidna Aliyyu yace: abinda na fi so a duniya_

1: Azumi a lokacin rani,

2: Karrama bako,

3: yakar abokan gaba da takobbi.

_Sannan Manzon Allah (Saw) ya koma wajen Abaa zarril Gifaari, ya ce masa: "yaa Abaa Zarri? Me ka fi so a duniya?_

  _Sai Abaa Zarri yace: abinda na fi so a duniya_
1: yunwa,
2: jinya,
3: mutuwa.

  _Sai manzon Allah (Saw) yace: "sabida me yasa kake son su?_


Sai Aba zarri yace:
*ina son yunwa ne don zuciya ta tayi laushi,
*ina son jinya ne don zunubi na yayi sauqi,
*ina son mutuwa ne sabida saduwa da ubangiji na

_A wannan lokacinne Mala'ika Jibrili ya sauqo zuwa majalisar Manzon Allah (domin hirar ta su ta birge shi ), sai yace: ni kuma ina son abubuwa uku a duniyar ku_
1: isar da sako,
2: bayar da amana,
3: son nakasassu.

_Daga fadin haka kuma sai ya tashi zuwa sama Sannan ya sauko a karo na daban sannan yace Allah madaukakin sarki yana karanta muku sallama Hirar manzon Allah da sahabbai tayi dadi, harma Allah yana gaishe su sannan Allah yace yana son abubuwa uku a duniyar ku_
1: harshe mai ambatonSa,
2: zuciya mai tsoronSa,
3: jikin da aka jarrabce shi da balaa'i kuma yayi hakuri#.

_Tsarki da godiya sun tabbata ga Allah Girma da tsarki sun tabbata Allah_

Adu'o'i guda uku kada ku manta su acikin sujjadarku..

"Ya Allah ina rokonka kyawawan halaye".
"Allah ka azurta ni da tuba zuwa gareka tabbatace"

"Ya ALLAH mamallakin zuciyata ka tabbatar da ita akan addininka"

Lalle wannan ya cancanta ku tura zuwa ga waninku domin ya amfana.

Dauki darasin ka a cikin wannan hadisi, ka aikata shi, za ka yi nasara.

Majalisar Manzon Allah makarantar mai imani ne, yi kokari ka fita a sahun farko na daliban makarantar.

SHAN ZUMA DOMIN RAGE KIBA

SHAN ZUMA DOMIN RAGE KIBA

******************************* *

Zuma na taimakawa wajen taso da sinadaran da suke sanya kiba, wadanda ke kwance a cikin jiki, tana fito da su ne don su bi jiki a lokacin da a ke aikin karfi, raguwarsu a jiki zai sanya kiba ta rage.

A lokacin da za a sha zumar ya kamata a gauraya zumar da ruwan zafi, sannan ana so idan har za a sha zumar, to a sha da sanyin safiya, idan an tashi sallar asuba ko kuma lokacin da aka farka daga barci.

Kuma idan aka gauraya zuma da ruwan zafi da kuma lemon tsami, sannan aka sha za su taimaka wajen rage kiba da kuma nauyin
Jiki
CIN AYABA DOMIN RAGE KIBA.

SHAN ZUMA DOMIN RAGE KIBA

*******************************

Cin Ayaba guda 3 duk safiya kanfin Mutum yaci abinci haka ma da dare in za'a kwanta na matuqar rage kiba a wata daya zaka ga cenji a jikinka.

HADA KANKANA DA CITTA DOMIN RAGE KIBA

********************************************

A samu kwallon kankana kamar guda biyu haka sai a markade su su zama ruwa a zuba garin citta, sai a dan sa ruwa sai a markada har sai yayi laushi Sai a ringa sha in rana ta yi zafi.




ABIN LURA ANAN
--------------------------
Yana da kyau a kula cewa kiba bata raguwa sai an rage cin abinci mai maiko sannan duk aka ci abincin rana kada a zauna a dan samu ayi wani aiki kona 15 mint ne

YADDA AKE HADA MAN KWAKWA

YADDA AKE HADA MAN KWAKWA

Duba da dumbin amfanin da man kwakwa ke da shi wajen kula da lafiyar jiki, gyaran gashi da kuma fata, yana da amfani sosai a san yadda ake fitar da shi a gida, yadda ako da yaushe mutum zai iya kasancewa da shi a saukake.

Abubuwan da ake bukata
Kwakwa kamar guda uku ko fiye da haka
Ruwan mai dan zafi, ba zafi sosai ba
Yadda ake hadawa:-

-1. Za’a samu kwakwa a fasa ta a bambare ta daga kokonta, sai a wanke sosai a yayyanka kanana kanana yadda injin nika zai iya markadawa a saukake

-2. A dafa ruwan zafi, amma kar yayi zafin da zai iya kona jiki, kuma ya fi ruwan dumi zafi. Amfani da ruwan zafi na taimakawa wajan fitarda mai da yawa.

-3. Daga nan sai ki zuba yankakken kwakwan a cikin Blender ki kwara ruwan zafin, sai ki markada shi har yayi laushi. Idan kwakwar da yawa sai kin raba kamar gida biyu ko uku.

-4. Idan ya markadu, sai ki tace shi da rariya, ki mayarda dusar cikin Blender din ki kuma kara zuba ruwan zafi ki markada don ki samu karin madarar kwakwar.

-5. Ki kara tace madarar da rariyar laushi ko abin tace shayin domin fitar da kamu kamun dusar da ta ki fita da fari.

-6. Daga nan sai ki saka ruwan da kika tace a firji ya kwana. Da safe zaki ga man ya yo sama yayi fari sal a daskare abun sha’awa. Zaki ga ya raba kanshi da sauran ruwan kwakwan.

-7. Zaki tsame man sai ki tace sauran ruwan domin tabbatar da cewa duka man ne ya fita (kar ki zubar da ruwan, zaki iya dafa shinkafa da shi).

-8. Ki sanya man a cikin tukunya ki dafa shi na tsahon awa daya da kamar minti ashirin akan wuta mara zafi sosai (low heat). Zaki na yi ki na juyawa, kar ki bar gurin har sai ya yi.

-9. Idan yayi, zaki ga man ya rabu da dusar. Ki tace ci a cikin kwalba da dan karamin abun mataci. Idan bai tacu ba da fari, ki sake yi.

Za ki iya amfani da man kwakwarki wajen yin giki, gyara fata ko kuma gyaran gashi, ko kuma ki yi na sayarwa.



Danneman Karin bayani:- 08065444595

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

HANYOYIN MAGANCE KURAJEN FUSKA

Duk da cewa maza da mata kan samu matsalar kuraje a fuska, mata su suka fi damuwa da su fiye da maza, domin su suka fi aiko da tambayoyi a kan yadda za a magance su:

kurajen taya-ni-muni pimples: kurajen pimples a turance ko acne bulgaris a likitance suna daya daga cikin larurori masu addabar samari da ’yan mata. Suna fitowa ne a daidai lokacin girma, domin a daidai lokacin ne sinadarin nan na testosterone ke yawa a jinin samari maza da kuma wasu kadan daga cikin mata.

Wannan sinadari shi ke da alhakin sa maiko ya rika taruwa a fuska. Idan maiko ya taru a fuska sai kwayoyin cuta su zo su taru a wurin su kawo kurji.

Hanyoyin kariya su ne kiyayi taruwar maiko da kwayoyin cuta a fuska da kirji. Wannan kan dan yi wahala amma ta wadannan dabaru za a samu nasara:

1-Rage maiko a cikin abinci. Misali, idan aka soya wani abinci, yana da kyau a tsane mai da mayanin kitchen wipe mai tsabta kafin a ci. Idan an yi haka an rage man kusan da kashi hamsin cikin dari ko ma fiye.

2-Yin amfani da sabulu mai kashe kwayoyin cuta wajen wanke fuskar safe da yamma.

3-Shan kayan itatuwa da cin ganyayyaki a kai-a kai yakan tsane maikon cikin jini ya kara karfin garkuwar jiki wajen yakar kwayoyin cuta.

4-Ga wanda wadannan dabaru ba su yi musu aiki ba, za su iya zuwa su nemi man shafawa a fuska da kirji mai dauke da sinadarin benzoyl perodide na shafawa safe da yamma bayan an wanke fuska.

5-Idan hakan ta ki wadatarwa sai an je asibiti an hada da karbar magungunan kashe kwayoyin cuta.
6-Ga wadanda wannan ma bai yi aiki ba, akwai dai magunguna masu karfi har ila yau irin samfurin bitaman ‘A’ da ake kira isotretoin da ake rubutawa a asibiti. Akan samu nasara sosai idan aka jarraba wadannan. Amma ba a bawa mai juna biyu shi.

7-Ba a so a rika matse kurajen saboda hakan kan iya jawo tabo, an fi so a bar su su fashe da kansu sai a wanke wurin

@ 08143484943

GYARA KANKI KICI MORIYAR MIJINKI

*GYARA KANKI KICI MORIYAR MIJINKI*

☘KI ZAMA KAMAR HAKA:

☘1. MAI YAWAN TUBA: A duk lokacin da kika sabawa Allah (S.W.T), kika samu kanki cikin nadamar laifin da kika yiwa Ubangijin ki, to ki yawaita tuba gare shi har Allah ya yafe miki. Domin istigifari ruwa ne wanda yake wanke zuciya, ya kuma gusar da kazantar zunubi.

☘2. MAI BIYAYYA GA MIJI: Ki kasance mai biyayya a wajen mijinki, abinda yace kiyi masa kiyi, wanda yace ki bari to ki barshi. Indai har umurnin ko hanin bai shiga hurumin addinin ki ba.

☘3. MA'ABOCIYAR KARATUN ALQUR'ANI: Ki kasance mai karatun Qur'ani, domin karanta shi waraka ne daga dukkan cuta, Qur'ani yana daukewa mai karanta shi dukkanin damuwa na duniya, sannan karanta shi yana 'karawa mutum tsoron Allah, karanta shi yana koron shaidanun Aljanu wainda zasu addabi rayuwar auren ki.

☘4. MAI YAWAN IBADA: Ki zamanto mai yawan yin ibada, mai yawan yin Nafila, kada ki zama raguwa, ke kullum kece koma baya wurin ibada. A'a ki tashi daddare ki roki Allah bukatunki, kiyi azumi in kin sha ruwa kiyi addu'a.

☘5. MAI JURIYA DA HAKURI: Ki kasance mai juriya da kuma hakuri a dukkanin al'amuran ki, domin nasara yana tare da hakuri, shi kuma hakuri sai ka jure, kada ki zama fitinanniyar mace mai neman ayi tashin hankali dake. Mai hana mijinki samun nutsuwa a cikin gidansa.

☘6. MAI ALKUNYA: Ki zamo mai kawaici da alkunya a cikin al'amurranki na rayuwa, domin ita rayuwa ta kan jefa mutum cikin abubuwa daban-daban. To kada ki zama fitsararriya, ki zama shaddar kasuwa, ko ballagaza mara kamun kai a unguwa.

☘7. MAI BIN SUNNAR ANNABIN MU MUHAMMAD (SAW): Ki kasance wadda kike koyi da abinda Manzon Allah (S.A.W) yazo dashi. Allah Madaukakin Sarki yace:" Abinda Manzo (SAW) yazo muku dashi, ku rike shi da kyau, abinda ya hane ku, ku hanu daga aikata shi". Don haka kada ki zama 'yar bidi'a.

☘8. MAI KWADAYIN ALJANNAH: Ki zamo mai kwadayin rahamar Allah, ki nemi tsari a wurin Allah don ya nisantar dake daga azabarsa. Lallai Allah mai rahama ne, kuma mai jin kai.

☘9. MAI RIKE SIRRIN MIJINTA: Ya kasance duk runtsi duk wahalar da zaki shiga ki rike sirrin mijinki, ki dogara ga Allah, ki zama duk yadda wani yabi 'kididdigi domin yasan sirrin gidanki kada ki yarda ya san wannan sirrin. Akwai hatsari ga matan da suke yada sirrin mijin su, masu baza abinda hatta ke faruwa a shinfidarsu.

☘10. KI ZAMA MAI TSAFTA DA KWALLIYA DA IYA GIRKI GA MIJINKI: Ya zama duk sati ko duk sati biyu akwai gyaran jiki na musamman da kike yiwa jikinki, akwai turarukan da kike turara jikin da dasu wanda zasu ratsa dukkanin sassa na jikinki, mai kula da tsaftar kanta domin akwai wacce kanta tamkar shekar angulu, bata yin kitso kuma bata gyara shi yayi laushi yayi kyau, yadda zai rinka fisgar hankalin mijinta. Ita dai kullun tana nan tana tsami tana yin masa magana yana kauda kansa saboda bata gogye bakinta. Yana daga cikin tsafta yanke gashin wurare guda biyu na jikin ki. Ki kuma zama kin iya girki mai dadi.

☘11. KI ZAMA MACE MAI AMANA: Wacce idan mijinki yayi tafiya ko idan ya fita zaki kiyaye masa amanar kanki dana gidansa da dukiyarsa da 'yan'yansa.

☘12. KI KASANCE MAI TAUSAYIN MIJINKI: Kada ki zama muguwa, wacce bata tausayin mijinta, wadda kullun burinta taga tayaya zata yi ta sanya ran mijinta ya 'baci, a'a ba aso ki kasance haka, so ake yi ki rinka tarairayan mijinki, ki zama mai nuna kulawa da nuna lafiyayyar soyayya gare shi.

☘13. KI KASANCE MAI IYA MAGANA: Dayawa daga cikin mata basu iya magana ba, shi fa maigida ya banbanta da sauran mutanen da kike mu'amala dasu, shi wani mutum ne mai daraja da 'kima, komai da zaki yi masa dole sai kin tace sa kin duba kinyi tunani, da magana kawai da kalaman soyayya sai ki mallake zuciyar mijinki, inma yana da mata dayawa sai ki zama tauraruwar cikinsu.

☘14. KI ZAMA MACE MAI SAUKAKA "KISHI": Hakikanin gaskiya ba zai yiwu ba ace mace tabar kishi, kuma duk wanda yace mace tabar kishi to yana 'batawa kansa lokacine kawai, sai dai ace ta saukaka kishin, kada kishin ya kaita ga yin mugun abu ga 'yar'uwarta. Kada kishin ya kai ta ga shirka, Saukaka kishi yana taimakawa ga mace ta samu 'kima da daraja a wurin mijinta.

☘15. KI ZAMA MAI KYAUTATAWA UWAR MIJI DA 'YAN'UWAN MIJI: Yin rashin mutunci da wulakanta 'yan'uwan miji bai dace ba, domin zaki jawoma kanki bakin jini. Kuma kin same shi da yan'uwan sa ba daidai bane ki shiga tsakanin su.

☘ *'Yar'uwa ku Sadeeya Lawal Abubakar.*

☘ *MARKAZUS SUNNAH*

☘ *Zaku iya shiga group din ta wainnan numbers din 08034643244 08089074217*

YIN RAKA'A GUDA 2 BAYAN FITOWAR ALFIJIR

YIN RAKA'A GUDA 2 BAYAN FITOWAR ALFIJIR

DARASI NA FARKO

Yana daga cikin nafilolin Manzon Allah ﷺ na yau da Kullum wanda yake yinsu kowane rana koda yana halin bulaguro,*Yin Raka'a biyu bayan alfijir ya fito,kafin sallar Assuba*yin hakan sunnance mai karfi.

*FALALAR WANNAN NAFILA*

Wannan Nafila tana da falala mai girma wanda Manzon Allah ﷺ ya bayyana falalarta da bakinsa da kuma aikinsa.

*Yin Raka'a biyu bayan fitowar alfijir yafi duniya da abinda yake cikinta falala da alkhairi*

Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Yin Raka'a guda biyu bayan fitowar alfijir na nafila,yafi Alkhairin duniya da abinda yake cikinta)*

@رواه مسلم.

*Babu wata nafila da Manzon Allah ﷺ yake tsananta kiyayeta kamar Raka'a guda biyu bayan fitowar Alfijir*

Daga Umar Masu Imani Mai gaskiya yar Mai Gaskiya shugaban Matan masu Ilimi baki daya wato,Nana A'isha رضي الله عنه tana cewa;
*"Manzon Allah ﷺ babu wata nafila da yake tsananta kiyayewa kamar raka'a guda biyu bayan fitowar alfijir"*.
@رواه مسلم والبخاري.

*WANNAN NAFILA TA SAMU WASU ABUBUWA GUDA 5 MASU KEBANTATTU MASU MUHIMMANCI FIYE DA SAURAN NAFILOLI*

الشيخ محمد بن صالح العثيمين رحمه

الله؛-
Yana cewa;-
Wannan nafila ta bayan fitowar alfijir ta samu wasu abubuwa kebantattu kamar haka;-

NA FARKO
*An shar'anta yinta alokacin bulaguro da lokacin zaman gida*

NA BIYU
*Ladarta yafi Alkhairin duniya da abinda yake cikinta awajan Allah*.

NA UKKU
*An sunnanta saukakata wajan karatu da sauran aiyukan sallah,ba'a tsawanta karatunta ko sujada da ruku'u,Amma da sharadin cikasa wajibin sallah da rukunnanta*

NA HUDU
*Ana son a karanta wadan nan surori bayan FATIHA acikinta*

Raka'a ta farko bayan FATIHA;-
*قُلْ يَاأَيُّهَا الْكَافِرُونَ*

Raka'a ta Biyu bayan FATIHA;-
*قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ*

KO KUMA;-

Raka'a ta farko bayan FATIHA;-
*قُولُوا آمَنَّا بِاللَّهِ*
@البقرة : 136.

Raka'a ta Biyu bayan FATIHA;-
*قُلْ يَاأَهْلَ الْكِتَابِ تَعَالَوْا إِلَى كَلِمَةٍ سَوَاءٍ بَيْنَنَا*
@آل عمران: 52.

NA HUDU
*Ana ramata idan ta wuce ga wanda ya makara*.

@الشرح الممتع (4-71).



HUKUNCIN WANNAN NAFILA



Allah ne mafi sani

MU HADU A DARASI NA GABA INSHA ALLAH.

Zikirai guda bakwai (7) mafi tsada a rayuwar Musulmi

Tags

1- Mafificin ambaton Allah

_Laa ilaha illallaahu  wahdahu lā shariyka lahu lahul-mulku wa lahul hamdu wa huwa alā kulli shay'en Qadiyr_

2- Mafificin tasbihi

_Subhanallaahi wabihamdihi, adada khalQihi, waridā nafsihi, wazinata arshihi, wa midāda kalimatihi_

3- Mafificyar Addu'a

Rabbana ātina fiy-dduniyā hasanatan -wafil akhirati Hasanah, waQinā azabanNār_

4- Mafificin Istigfari

Allaahumma anta rabbiy lā ilaha illā anta khalaQ-taniy, wa'ana abduka, wa ana alā aHdika, wa-wa' dika masta-'da at, a-uzubika min sharri ma sana'atu, abū Ulaka bini'-matika ãlayya, wa-abu'u bizambiy, Fagfirliy fa-innahu Lā yagfiruz-Zunuba illa ant_

5- Mafificin neman kariya da tsari

Bismillaahilladziy Lā yadurru ma-asmihi shay'un fiyl-ardhi walā fiys-Samā' , wa huwas samiy'un alaiym_

6- Mafificin zikirin neman yaye damuwa da bakin ciki

Lā ilaHa illa anta subhānaka inniy kuntu minaz-Zālimiyn_

7- Mafi zikirin dogaro ga Allah da sallamawa a gareshi

Lā haula wala Quwwata Illa billaahil aliyyil aziym_
Allah ya sa mu dace
Allahumma Ameen.

YADDA AKE MAGANIN ZAZZABI AJIKIN DANADAM

YADDA AKE MAGANIN ZAZZABI AJIKIN DAN
ADAM

KASHE KASHEN ZAZZABI:-
(1) malaria fever
(2) typhoid fever
(3) lassa fever
(4) ebola fever etc

MAFITA  MAFITA
ludufin Allah akan warkar da zazzabi ya
bayyana acikin
SHUWAKA
Likitocin fannin ci da sha wato

NUTRITIONISTS)
Sun bayyana shuwaka amatsayin magani
Daga cikin Magugunan zazzabi kowane iri...
(1) Abu na farko shine; ta bayyana cewa idan
kana cin shuwaka koda sau biyu ne a sati, to
ba zakayi zazzabi ko wane iri ba!
(2) idan kuma kanada shi, to ko awane
mataki ya kaika zaka warware ba tareda
shan magani ba! Saboda acikinta akwai
kowane nau'in sinadari me warkar da zazzabi

(3) SHUWAKA tanada amfanarwa akan duk
matsalar da zata sa ka yi anfani da
(amoxaciline)
(ampiculox)
( paracetamol)
(Clarithromacilin)
SABODA HAKA
duk lokacin da larura ta sameka ko kuma
wani naka, yazama lalle daya daga Cikin
wadannan magugunanne za abashi to ka
sani cewa duk aikin da zasuyi to shine
SHUWAKA zatayi Maka.

WANDA YAJI TO YAYI KOKARI YA AIKATA

Kuma yasanar da makusanta; don kubutar da
jama'a gameda hadarin ciwon.

AMFANIN MAN TAFARNUWA GA YARA KANANA

AMFANIN MAN TAFARNUWA GA YARA KANANA

idan yaro yakai wata uku da haihuwa
anabashi man tafarnuwa rabin karamin
cokali sau uku arana kwana uku zairabashi
da danshi da tafiyar ruwa da cutar tamowa
amma arinka hadawa da abinda zaisha kuma
shafawa yaro man tafarnuwa a dasashinsa
yana saukaka fitowar hakorin jariri mace mai
goyo idan batada isashshen ruwan nono sai
tasamu hantar karamar dabba tasoya tacinye
zatasamu karin nono amma azuba cokali
daya na man tafarnuwa acikin man suyar,
idan yaro yana kurga ,(wata tsutsace da take
fitowa a dubura) ko in yana kuka marar dalili
sai abashi man tafarnuwa rabin cokali sau 2
arana, idan anaso yaro yakasance cikin
kuzari da koshin lafiya sai tarika zuba man
tafarnuwa karamin chokali a abincinta...

MAGANIN CIWON MARA %%CIWON MARAR MAI HAILA%%

Tags

MAGANIN CIWON MARA
%%CIWON MARAR MAI HAILA%%

Mafiya
yawa daga cikin mata na kuka da ciwon
mara wanda kan hanawa wasu rawar gaban
hantsi. So dayawa xakaga mace na xullumin
tsayuwar wata domin tasan irin axabar
datakesha duk adalilin ciwon mara. Ciwone
dakan tsananta agurin wasu yakuma
galabaitar dasu wasuma har amai xakaga
sunayi yayin da wasu numfashinsu ke dauke
yakaisu ga suma. La'akari dahakan yasa
nima nafadada bincike domin kawo ma 'yan
uwa mata wasu daga cikin hanyoyin
daxasubi dan ganin Allah yasauwake yakuma
basu lafia. 1.kisamu dabino masu kyau
sabbin tsinka guda bakwai, kici dasafe kafin
kici komai. 2.kisamu xogale kadan da
tsamiya kisa akofi, sannan kisamu
tafasashen ruwa kixuba akofin idan yadan
huce kishanye alokacin. Kiyi haka har sau
uku. Insha Allahu xaki samu sauki 3.kisamu
dauwa kamar rabin mudu kijikata akwano
natsawon kwana biyu sannan ki mutssiketa
kitace sannan kisha. Yana maganin ciwon
mara sosai yanakuma tsinka jini gawadda
ciwon yadameta jini baixoba idan dai tai
hakan jinin xaixo ciwon yayi sauki. Allah
yabama masu fama da wannan matsalar
lafiya ameen.

AMFANIN MAN TAFARNUWA GA MAZA (1)

AMFANIN MAN TAFARNUWA GA MAZA
idan namiji yanajin kaikayi a marainansa ko
a azzakarinsa to sai yasamu garin farar
kanwa cokali 1 adafa da ruwa kofi 2 idan ya
tafasa sai azuba man tafarnuwa cokali 2
inyahuce sai yawanke gabansa da ruwan
zaisamu sauki insha allah

AMFANIN MAN TAFARNUWA GA MATA (2)

AMFANIN MAN TAFARNUWA GA MATA

Gaeme da matarda bata taba haihuwaba
idan tanaso tagane zata iyasamun ciki? Ko
a,a? To sai tasamuwa mai dumi da sabulu
tawanke gabanta sosai sannan tasamu
auduga maikyau sannan tazuba man
tafarnuwa cokali daya akan audugar sannan
tayi kunzugu da audugar har tsawon awa 2,
intaji warin tafar nuwar abakinta, zatasamu
ciki lokacine baiyiba kokuma matsalar daga
mijinne inkuma batajiba to sai dai allah
yasawake, amma ana maimaitawa har sau
uku domin kara tabbatarwa.. YAWAN
LALACEWAR CIKI KO YAWAN BARI; asamu
kwan agwagwa asoya da man tafarnuwa
abaiwa matar taci sau 2 arana kwana 7.
TSAWON GASHI DA HANASHI KAKKARYEWA;
Asamu man kwakwa ahada da man zaitun da
man tafarnuwa arinka shafawa akai, amma
man tafarnuwa 50% za,asa sauran kuma
100&... Allah yasa mudace...

ZAITUN DA AMFANINSA

ZAITUN DA AMFANINSA
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
ZAITUN DA AMFANINSA
🌿🌿🌿ZAITUN 🌿
Hakika zaitun yana daga cikin itatuwa masu
daraja domin allah s. w. t yayi rantsuwa da
zaitun acikin al-qurani maigirma 📖

1- GAME DA MAI FAMA DA KARANCIN JINI
AJIKINSA
sai yasamu yayan zaitun arika cin guda 6
arena.

2- GAME DA MAI FAMA DA BASUR
asamu zaitun ahada da sassaken danya
arika sha anono ko kunu ko ma aruwa

3- GAME DA CHIWON MARA NA MATA
Asamu man zaitun ahada da ruwan tsamiya
arika sha za, asamu sauki insha allah.

4- GAME DA SANYIN KASHI
Asamu man zaitun ahada da man
habbatussauda  arika sha ana shafawa
awajen da yake ciwon.

5- GAME DA GYARAN FATA TAYI LAUSHI DA
KYAU
Arika wanka da ruwan dumi sannan in an fito
ashafe jiki da man zaitun ✅✅✅

Amfanin Abarba (pineapple) a jikin danadam.

Amfanin Abarba (pineapple) a jikin dan
adam.

Musamman ma kare jiki daga kamuwa
da ciwon zuciya.

Abarba na daya daga cikin yayan itatuwa
masu amfani a jikin dan adam.
Abarba na da matukar amfani a jikin dan
adam saboda tana dauke da muhimman
abubuwa;

fibres,menirals.vitamins.Nutrient
da kuma Anti.Oxidant. Wadanda ke da
matukar amfani ga rayuwar dan
adam.sannan takan kare jiki daga
cututtuka.Ga kadan daga amfanin Abarba;

√ 

1.tana dauke da sinadarin
magnees da calcium wanda ke kara karfin
kashi

2.tana dauke da anti.oxidant wanda ke kara
ma jiki lafiya da kare jiki daga saurin tsufa.

3.tana maganin mura da sanyin kirji.

5.tana kara ma garkuwar jiki lafiya da kare
shi daga cututtuka

6.tana maganin kamuwa da ciwon zuciya ta
hanyar rage cholesterol a jiki.

7.tana kara lafiyar dasashi da kare hakora.

8.tana saukaka yawan laulayin ciki, da
yawan amai da yawan tashin zuciya.

10.tana maganin tsutsar ciki.

11.tana kara ma idanu lafiya

12. Tana kara lafiyar ciki da saukaka bahaya

13.tana maganin kumburi da maganin ciwon
ga babuwa
da fatan zamu rinka shan abarba akai akai.
Kuma Allah temaka mana amin

MAGANIN SANYI NA MAZA

MAGANIN SANYI NA MAZA
Shi wannan sanyin gaskiya yana da wahalar
jin magani. Domin kuwa wadancan abubuwan
da ka ambata a baya, mutane da yawa sun
jarraba kuma sun samu waraka da yardar
Allah.
Amma ga wasu nan ga jarraba:
1. Ka nemi Man Habbatus sauda dan Misra
ko Algeria ko Hemani. Ka gaurayashi da man
Tafarnuwa Original tare da Man Albabunaj.
Sannan ka rika dafa 'danyar chitta (Ginger)
da ruwa kofi guda. idan ya dafu sai ka sanya
wancan Man chokali guda aciki, sannan ka
sanya zuma daidai gwargwado, sannan
kasha.
In dai sanyi ne, kowanne iri ne in sha Allahu
zaka samu waraka.
Ka samu Furen Albabunaj (chamomile flower)
ka rika dafa cokali guda kana sha kullum da
safe. In sha Allah Wannan zai wanke maka
Qodarka da mafitsararka, Kuma zai magance
maka Matsalolin ciwon sanyi.
WALLAHU A'ALAM.

MAGANIN CIWON SANYI NA MATA

MAGANIN CIWON SANYI NA MATA
**************************************
Hakika ciwon sanyi na mata yana daga cikin
cututtuka masu wuyar magani, kuma mata da
yawa suna shan fama dashi.
Ga wata fa'idah nan daga ZAUREN FIQHU ku
jarraba, In sha Allahu za'a samu waraka.
Anemi :
1. Garin Tafarnuwa.
2. Saiwar Raihan (Doddoya - Rai dore)
3. Garin Kanumfari da citta.
4. Saiwar Zogale.
Wadannan abubuwan gaba daya ahadasu
adakesu waje guda, sannan arika diban
cokali guda ana dafawa ana sha kullum safe
da yamma.
Sannan adebi wani ahada da barkono ayi
yaaji dashi arika cin abinci. In sha Allahu
koda sanyi yayi shekara arba'in ajikinki ko
fiye da haka, zaki warke.
Hakanan Mazaje masu fama da matsalar
Sanyin mazakuta, Idan sukayi wannan hadin
zasu samu waraka da izinin Allah (SWT).
Tukwicin da za'a bani shine ayi Salati guda
goma bisa Masoyina, Shugabana, abin
koyina, Muhammadur Rasulullahi (Sallal
Laahu alaihi wa aalihi wa sallam).