Kamar yadda ba kowacce Mace Namiji ke so
ba haka zalika ba kowana Namiji Mace ke so
ba.
Akwai wasu siffofin nagari dake tattare da
Mijin da kowacce macce ke so:
1.Mijin dake son matarsa bayan aurensu
fiyeda yadda yake sonta a layi.
2.Miji mai kishin matarsa. Domin Annabi
Sallallahu alaihi wasallam yace: “duk wanda
baya kishin matarsa bazai shiga Aljannah
ba”.
3.Mijin da ya dauki aure a matsayin Ibadah,
ba wai abin wasa ba ko kuma abin jin dadin
rayuwa kawai ba.
4.Wanda ya dauki matarsa a matsayin
abokiyarsa, kanwarsa, almajirarsa, kuma
abokiyar shawararsa.
5.Shine wanda baya zagin matarsa, baya cin
mutuncinta, baya cin zalinta, baya ha’intarta
koda a bayan idonta ne
6.Shine wanda yake zaune da iyalinsa cikin
amana da gaskiya da kyautatawa ba cuta ba
cutarwa. Wanda idan ya fahimci halayen
matarsa, yake hakurin zama da ita tare da
kyautatawa domin neman rahamar Allah
Ta’ala.
7.Shine wanda idan zai yi magana da
matarsa, zai fadi gaskiya babu yaudara ko
karya acikin zancensa.
8.Shine wanda ya dauka a zuciyarsa cewa:
Iyayen matarsa, Iyayensa ne. ‘Yan uwanta
ma ‘yan uwansa ne, kuma dangin matarsa
danginsa ne.
9.Shine wanda yake daukar cewa farin cikin
matarsa shine farin cikinsa kuma matsalar
ta, itama tasa ce.
10.Shine wanda ke kokarin kiyaye sirrin
matarsa, kuma yake kokarin kare mata
mutuncinta koda a wajen ‘yan uwansa ne,
tare da hikima da fahimtarwa.
11.Shine wanda baya fifita matarsa akan
‘yan uwansa, kuma baya tauye mata
darajarta. Yana bawa kowanne gefe nasa
hakkin kamar yadda shari’ah ta tanadar.
12.Shine wanda ya tanadi ruwan afuwa da
hakuri a cikin zuciyarsa domin kashe wutar
tashin hankali da bacin rai a duk lokacin da
hakan ta faru tsakaninsa da matarsa.
13.Shine wanda a kullum yake kokarin
tarbiyyantar da iyalinsa akan rayuwar addinin
Islama ba rayuwa irin ta yahudu da nasara
ba.
14.Shine wanda yake zaune da matarsa
komai dadi komai wuya ba zai dena nuna
mata soyayya ba wai
don tafara yankwanewa ko kuma karfinta
yafara raguwa.
15.Shine wanda yake bawa matarsa yabo a
duk lokacin da tayi kwalliya ko kuma tayi
girki komai rashin dadinshi. Miji nagari baya
raki baya ihu don yaji abinci yayi yaji ko
gishiri yayi yawa. Sai dai yace: “uwargida
abincin nan yayi dadi iyaka, sai dai gishiri
yayi mana shisshigi a ciki”
Allah Yasa mazaje su gane,su sauke
hakkinsu na kulawa..Ameen
Mijin Da Kowace Mace Ke So
SHUGABA MATAR SARKI Page 6,7
SHUGABA🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕MATAR SARKI🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀
Pg 6
BAYAN WATA DAYA!!!
Ikram da ta yarda da karatu a jami'ar da ta samu suka shirya tare da Boiler sai Abuja!
Alh Sharehu da yayi iya yinsa Malama ta ki ta hakura ta bar yarinya ta horu a makarantar gaba da secondary ma.
Ya je Abuja ya kama musu hayar gida a wani housing estate cikin jama'a a unguwar Lugbe kusa da makaranta!
Ikram ta zabi yar aiki daya,mai iya daukar raini!
Sauran Yan aikin kuwa suka dinga yimata jaje!
Bello kuwa yana ta fada!
Wannan sakarci na Ikram har yaushe?
Yarinya ta sangarce kamar tsumma a ruwa?
Ita kuma Boiler ta lalata yarinya kamar ba a duniya ake ba?
Haka fa sukayi da ta sami gurbin karatu a boarding house,tsohuwar nan ta dinga zuwa kullum tana bala'i Sai an aske ma yarinya gashi!
Waye bai San tsarin karatun state dinnan ba??
Anas ya bushe da dariya!
Wannan abu Yasin kamar drama!
Ai dai kun tuna lokacin da Boiler ta je har can makarantar ta aske wa malamar kai!
Sanadiyyar koro Ikram daga boarding house kenan!
Gaba daya suka bushe da dariya
[6/20, 5:15 PM] Bar Rahma: Wallahi baba ne ai ya ba Boiler dama in ji Anas da ya tarfa a karon farko!
Shine mana Umar ya karba!
Su je su gani in zaman Abuja easy ne!
Labaran da ya ga damar tanka musu a karon farko yace,ai su kam zasu ji dadin zaman!
Don ita Boiler tunda akwai kudi a hannun ta, sai tayi ta kara shagwaba wannan yarinyar mai kai kamar na Akuya!
Ai da kayi joining dinsu,don ban ga dalilin da zaka ki karatun ba inji Umar!
Kai kenan!
Labaran ya tabe bakin sa.Bana son karatu a Nigeria!
Uwa uba school daya da Boiler da Ikram! These re the two sets of annoying things in my life!
Kai dai baka sa wayo ne!
Bello kenan!
Kai da zaka je ka nemi ilmi,meye na zabe?
Labaran ya daga yatsa daya.
One,course din da nake so ma basa yi.
Ya daga na biyu,two bana son zama da mutanen nan.
Sannan three,a irin dukiyar baba,a hada da zubin kwakwalwata wallahi na girmi karatun Kasar nan!
Inda dai kake katoton kuskure kenan!
Mu ma nan sai da Boiler ta zabar mana jami'o'in da muka yi.
Kai ka gode Allah ma private university zaku yi?
Mu fa lokacin mu?
Boiler tace bata yarda a kashe mana kudi ba mai yawa kan karatu!
Yanzun ma da ka ci albarkacin yar gata Ikram!
Don bana cire tsammanin saboda ita ne ta amince da private university!
Hmmm!
Allah Sarki in ji Labaran!
Ashe Ku CE Boiler ta Dade tana mulkin kama karya! To nidai bata isa ba wallahi!!
Bello ne ya bushe da dariya.A'a wallahi mu kam munsan ta Isa!
Tunda baba dai babu abinda Zai yi bai shawarceta ba.
Gasu can dai sun tafi,kai kuma ga ka anan zaune!
Labaran da ran sa ya kara dugunzuma ya baci ya ka dogon tsaki!
It is not over yet,infill its over!
Zan nuna mata cewa ba itace karshe ba a gidan nan!
Allah ya bada Sa'a inji Anas.
Mu da muka yi accepting defeat ba gashi mun yi har an wuce wurin ba?
Ai shine suka amsa lokaci daya!
Umar yayi dariya.Amma fa akwai drama.Inama bani da aikin yi in bisu Abuja in sha dariya?
Ta Yaya Ikram zata yi karatun Law?
Yarinya ta gama shagwabewa?
Ai kuma ba daga nan ba inji Anas!
In dai tana da juriya sai Ku ga ta iya.
Juriya a ina fa in ji Labaran?
Bata da komai in ba majina ba da ruwa cike fa wannan katon kan nata!
Bello yayi dariya.
Ni kuma kullum burina in ga namijin da Zai kwashe su ita da boiler!
Wai!wai!!wai!!! Ai bazata auru ba inji Umar!
Wa Zai aureta?
Labaran yace kai Ku tsaya Ku ji tsegumin da na jiyo muku.
Wallahi na ji da kunne na,Boiler na son hada ka kai Umar! Da ita auren zumunci!
Umar bai San lokacin da ya zabura ya mike tsaye ba!
Tir! Ai da in aure ta, gara na nemi kabailar tiv na aura,masu daura ganye zuwa kasuwa!
Shiru suka yi suna jinjina zancen!
Ai bai ma dace ba inji Bello!
Amma ko da an cuce ka inji Anas!
Mutum ya budi ido da boiler, sannan auren ka ma ka ganta zaune a gidan ka!
Wayyo rashin yanci!
Wannan zancen banza ne Umar ya baro cike da fushi!
Haba!Sai kace mata sun kare!
Ai ko mata sun kare gara na mutu a gwauro da in auri IKRAM!!?
RAHMA
08061608583
SHUGABA🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕MATAR SARKI🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳
Pg 7
A yau Labaran ya shirya,ba tare da ya sanar da kowa ba ya nufi garin da Talatu Maman sa ke aure mai suna mutum biyu!
A kan hanyar sa yake sake sake a ransa!
Ina ma tana da dukiya?
Ya samu ya kashe haushi.
Ya ja tsaki!
Tsakin da yasa mai motar ya waiwaye shi!
Lafiya dai ko?
Ina Ruwan ka da da ni?
Na biya ka ka kaini garin 'mutum biyu ne? Ko na biya ka ne don ka dinga sauraren zancen zuci da nake yi?
Driver yace kayi hakuri.
Na gan ka ne a cikin manyan kaya.Da gani da n attajiri ne kai.Ga ka bahauahe Dan uwa na,bazan so in ganka a cikin damuwa ba!
Labaran ya bashi umurni,ja mu je Malam kalli gaban ka!
Sa ido bai yi ba,haka ma shiga shirgin mutane ba aji bane!
A dalilin shiga sharo ba shanu ne malama ta shiga tasku na!
Allah ya sutura inji driver mai son zance!
Wacece Malama?
Hala dai budurwar ka?
Kallon bana Labaran yayi masa.
Wallahi in ka kara cewa tak!Tak! In ka furta a bakacen kudin ka.kuma duk bala'in da za'a yi forget it!
Bazan biya ka ba.
Driver da Labaran ya dauke shi chata akan kudi mai tsoka,ya ja bakinsa yayi shiru.Ya kika hannu ya kuna rediyon mota!
Labaran ya daka masa tsawa!
Pls my friend kashe mun wannan noise din,bana son jin muryoyin bunch of loosers a Kunne na!
Ya cigaba da zancen zuci!
Suna tafe har kofar gidan da Talatu ke aure!
Ya ba driver umurni ya tsaya!
Ka jira zan fito mu koma tare.
Ai yana shiga akayi rashin Sa'a!
Talatuwa kwance a kofar dakin ta, tana lullube da tsohon bargo tana rawar Dari!
Masassara ne ya dirar mata kwana biyu tana ta fama!
Labaran ya karasa da sauri.
Allah Sarki! Tana jiwo kamshin turaren sa ta fara kokarin tashi!
Ya ji ransa ya baci.A yadda ya ga rigar jikin ta da jirwaye!
Kuma shi a rayuwar sa baya son ya ga nonuwan mace a zube!
Ya lura da ita ya kawar da Kansa.
Sannu da zuwa ta fada a cikin muryar zazzabi!
Yawwa sannu!
Ta sadda kai kasa don Dan fari ne shi,tana jin nauyin sa!
Da kyar ta iya tambayar sa,ko ka kawo mun 'kunun kanti'??? Wato custard take nufi!
Labaran da ya saba yo mata provisions duk zai zo gaishe ta ya ji ransa ya dugunzuma ya baci!
Wato kullum Talatuwa kara zama bakauya take yi? Kunun kanti????
Ban kawo miki komai ba yau,na zo karba ne nima yau!
Talatu ta daure ta gyara zama!
Ba dai Matsala ka samu da malama ba ko??? Yaya na ganka haka rai a bace!
Babu komai. Don Allah zaki gaskanta zance na idan na gaya miki cewa Boiler malamar tsabta,tsohuwar kawai algunguma ,azzaluma ta dauki Ikram wawuya mummuna sun tafi karatu Abuja? Ni kuma ina zaune a gida?
Talatu ta ji zazzabi yayi sauki!
Ta gyara zama tare da tagumi.
Amma daga yau ka daina ambaton Malama da irin wadannan sunaye!
Ka kuwa San a yanzu duniya bani da kamar ta? Banda tana kakar ka,nima baba ta CE!
Labaran ya gyada kai cike da bacin rai!
To Gaskiya zan gaya miki mama,baki yi sa'ar uwa,ba.Wannan uwar taki uwar kankanba CE!
Babu ruwa na da ita Sam! Sam!!!!
To me yayi zafi haka? To Ai shine nake so ki shirya mu je,kiyi ma baba sharehu kuka akan nima ya saka ni a makaranta!
Kinga yanzu kanwa bata nan balle ta hana shi.Tana can tare da Ikram suna karatun lauyanci!. Ikram da kowa yasan takwala ce ,dakikiya ta kin karawa!
Shine ni dinnan da kwakwalwata ke aman Basira,kaina na daukar karatu kamar ni nayi kaina,shine wai za'a hana ni karatu!
Talatu ta fara zub da kwalla.
Ya lura da hakan ya cigaba, da mahaifi na na da rai da ba haka ba!
Suna zaune shiru,sai ga maigidan Talatuwa ya dawo dauke da sasaken maganin zazzabi!
Ya nuna farin cikin ganin Labaran!. Shima Labaran ya gayar dashi a babu yabo,ba fallasa!
Malam ina Neman alfarmar tafiya da mama ta,don akwai hudimar da zata yimun.
Malam ko yace a'a.Kai baka ga bata da lafiya bane?
To zo zamu yi magana Labaran ya CE.
Bai zo din ba sai da ya gama hada magani a kwanon sha,ya dama kunu ya zuba maganin a ciki ya kawo gaban Talatuwa ya ajiye!
Ki Sha wannan kafin anjima wancan ya jiku ki kara sha!
Labaran yayi masa kallon raini.A haka zata warke da wadannan jike jiken ba zuwa asibiti?
Zai yi magana ya daga masa hannu!
Hold it!
Abinda yasa nace zan tafi da ita,ina shirin zan je Turai karatu,ina Neman tallafin kudi,ko zaka shiga ka fito mun da rancen miliyan 5 zuwa 10 haka,ko kuma ka bani mama ta,ta je ta roka mun inda zan samu.
Kallon kallo suka tsaya yi.Shi maigidan Talatuwa yana ganin labaran yayi masa mugun cin fuska da wani bil Adama bai taba yimasa ba,don ko maganin naira dubu 5 baya yi.Ya kuma San Labaran ya San da haka Kwarai, don sau tari shi ke kawo musu abinci!
Bani da wannan kudin Labaran. Amma kayi hakuri Maman ka ta sami lafiya!
A cikin yamutsa fuska yace,to ta ina zata sami lafiya da wannan daci da kake dura mata?
Na gano wayon ka,ka aure ta daga makurdi,ka kawo ta nan ne don ka kashe ta ka ci gado!
To bata da komai.Tana nan talaka futuk tamkar beran coci!
Mai gidan Talatuwa ya hasala wai zai mari Labaran!
Labaran ya kama yatsun sa biyu ya murda su,suka karye!
Talatuwa ta fara kuka!
Labaran bai tsaya anan ba ya dauki maganin da,Talatuwa ke sha,ya juye a tsakiyar kan mai gidan ta!
Gobe ka kara daga hannun ka mai datti,kace zaka mari mai kama dani.
Talatuwa na kuka ya fizgo ta ya nufi mota da ita babu ko mayafi!
Driver ya ja suka kama hanyar makurdi!
Heekma
SHUGABA MATAR SARKI Page 2,3,4
SHUGABA🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕MATAR SARKI🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀
Pg 2
MAKURDI,JIHAR BENUE!!!
Ikram ta fito a cikin kyakyawar shiri!
Boiler na biye da ita rike da jakar ta!
Labaran da yayi tsayuwar zuba hannayen sa a cikin aljihu yayi fito!
Baby da boiler an hadu,har an chure!
Yau mutanen garin nan zasu sha kallo!
Boiler dai ta dake,bata CE dashi ci kanka ba!
Ikram CE tace Yaya dai gayu?
Gayu mutanen Allah!
Yaya shan panadol?
Ka dai gasa goshin ka,ka kuwa ga Zai yi kululu!
Labaran ya Shafa kansa!
Boiler kallon banza ta wurga masa a yayin da ya tsugunna har kasa yana gaishe ta cikin izgili!
Gafara!
Kaima kasan ba damuwa nayi da gaisuwar Ku ba.
Nidai in wayi gari in ji Ikrama lafiyar ta kalau!
Me kuma nake nema banda wannan?
Labaran ya tashi tsaye yana fadin ,ko in zo in kai Ku inda zaku ne?
Kafin Ikram ta amsa boiler ta karbe,A'a!
Kayi ta zaman ka a gida,tare da masu zaman gida!
Ina zan yarda ka tuka mu,ka je ka yar damu riba benuwe?
River Benue ake cewa,ba riba benuwe ba!
To na ji sarkin iya yi!
A daidai nan sa'adu comrade ya ci karo dasu,ya tsugunna har kasa ya gayar da malama!
Yau ba'a fita bane? Ta tambaya cike da kulawa!
Muna nan tukun ya amsa,batare da ya dauke idon sa Daga kan Ikram ba!
Malama tace to Allah yayi jagora!
A dai daure ana Neman halaliya!
Ai kuwa wannan ya zama dole ya amsa!
Kasancewar gidan na da tsawo yasa suka cigaba da tafiya,a yayin da suke ta haduwa da Yan aikin gidan!
Sai da suka kure gida,suka yi kwana,sai ga su a wani katon falo!
Alh.Sharehu na ganin mahaifiyar sa,ya taryo ta!
Malama an fito!
Eh! Zan raka ikrama siyayya ne!
Yara ne maza su uku samari zazzaune gaban Alh.
Babban mai suna Bello ya gayar da ita!
Bana cin mike! Gaisuwa sai na roka,a matsayina na uwar ubanku??
Umar ma ya gaishe ta.Ta amsa tana fadin,kai nayi maka uzuri saboda kana da kulafuci in ka ga dama,amma kun ga wancan Anas din mai kai kamar ya dau gammo?
Kai ko ka gaishe ni bazan amsa ba! Haka kuwa akayi,ya gayar da ita,ta kawar da kanta!
Sai dai sun yi shiru da magana har sai da Alh.sharehu ya sallameta da kudi masu kauri!
Ya mikawa ikram nata!
Sai da ta duka a gaban sa,ya gaishe shi tukunna ta karbi kudin!
Malama na kallon ta cike da sha'awa! Yawwa ikrama ai haka ake so!
Amma yara ace Baku da da'a? Ai zama kudu bai yi ba.
Inama Kano ka tura su,su kiyi kyawawan halayya!
Nan dai akayi shiru har ta FIta.Saboda kowa na mugun tsoron malama!
Kwas! Kwas!! Kwas!!!
Labaran ne mai tsokana!
Sai malama
SHUGABA🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕MATAR SARKI🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀
Pg 3
DAKIN TARO!!!!!
Bayan sati daya!
Bello,Umar, da Anas suna zaune a layi daya a kasa cikin sadda kai kasa!
Boiler tana zaune saman kujera,a yayin da Ikram na zaune kasa a gaban ta, tana rike da hannun ta!
Shi kuma Labaran yana zaune can Daga bakin kofa,ya sha babbar Riga da ta sha aiki aska biyu!
Banda irin rana ta yau da yake wankin kayan sa,babu abinda ke hada shi da wannan hamshakiyar rigar!
Ko irin yau din ma,don korafin boiler da take yi cewa kada ya sake ta ganshi da Riga vest da boxers! Don ita bata marmarin ganin tsiraicin sa!
Irin zaman da Labaran yayi ne ya tabbatar da cewa babu komai a jikin sa in ba gajeren wando ba!
Kowa ya nutsu!
Sai Alh.yayi musu sallama! Gaba daya suka amsa!
Alh sharehu ya kalle su daya bayan daya!
Abinda yasa na Tara Ku,don in yi muku godiya kan hadin kan da kuke bani koda yaushe!
Kowa yayi tsit!
Sai Labaran ne yace,AI dole mu baka hadin kai!
Don kayi ne wallahi!
Oh! Boiler ta rike baki.
Wallahi har yau ban San inda Talatuwa ta samo wannan da ba!
Zaka yi shiru ubanka yayi magana? Ko dai kai ka tara mu anan?
Labaran ya gyara bakin sa, tare da hararar boiler ta kasan ido,Wanda yake sako ne Daga ita sai shi!
Ai kuwa Daga can ta wurga masa dakuwa!
Labaran ka ci gidan Ku!
Na CE ka ci kundun ubanka!
Alh.sharehu ya ba malama hakuri.
Duk da dai kowa ya zaci ba abinda akayi mata!
Masifar ta ke cin ta as usual!
Ikram da abin ya kona mata rai tace ina zuwa!
Ko dai in raka ki?
Lokaci daya Umar da Anas suka kalle su!
Boiler tace dasu ,Ku kuma me kallo ke so?
A'a malama jira ina zuwa yanzu!
A hanyar fitar ta sami hannun Labaran ta take shi!
Ya maza ya janye yana yarfarwa!
Eyya! Sorry pls Ashe a hanya ka zauna,na taka ka!
Bayan ta dawo ne Alh.sharehu ya cigaba da bayanin sa!
Abinda yasa muka taru anan kan karatun yaran nan biyu da suka rage basu sami shiga jami'a ba!
Wato Labaran da Ikram!
Ina mai farincikin shaida muku cewa,dazu ake sanar dani cewa sun sami gurbi a jami'ar nan da nake nema musu wato Nile!
Malama tace Alhamdulillah!
Allah na gode maka.
Ikram ta kankame malama cikin jin dadi!
Yaushe zamu tafi ne inji malama?
Alh.sharehu cikin murmushi ya amsa,to ke malama da ke za'a yi rakiyar ne?
Rakiya? Ta tambaya tana mai dafe kirji!
Ai karatun lauyancin dungurungum da ni za'a yi!
Bari ka ji sharudda! Dole ne ma ka kama mana gida!
Sannan ikrama ta zabi yar aiki daya da ta yarda da ita mu tafi tare!
Lallai Ashe abin babba ne in ji Alhaji!
To ke Ikram haka zaki tafi makaranta da kakar taki?
A cikin shagwaba ta amsa,ai baba haka ne kam!
Ni bazan ko iya karatun ba inba malama kusa!
Alh.sharehu ya kada Kansa!
Bello da ya ga alamar zance ya zauna,sai yace,wai Ku da gaske kuke ko wasa?
Ke Ikram kin ko San abinda kike yi?
Wannan wane irin abu ne? Zaki tafi school da malama?
Ikram ta labe bayan Malama ta murguda masa baki!
Ke! Ashe baki da kunya?
Malama ta tashi tsaye tana gyara daurin zani!
Ai Kaine babban marar kunyar!
Ina Ruwan ka da ikrama?
Ina Ruwan ka da rayuwar ta?
Ko Goya ni zata yi tayi ta yawo meye naka a ciki?
Alh sharehu ya shiga ya ba Malama hakuri!
Shi kuwa Labaran da tun da akayi albishir din samun admission bai CE komai ba sai yanzu ya yi Gyaran murya tare da sallama!
Gaba daya aka amsa!
Sai ya taso ya zo tsakiya ya tsaya!
Banda Alh.sharehu,kowa na hango boxers dinsa ta cikin babbar rigar da ya saki don tsabar hasala!
Don Allah tambaya zan muku!
Tun da na shiga makaranta na gama,kun taba ganina ina karatu ko bita ,don jarrabawa ko wani abu??
Masu amsawa suka CE a'a!
Yawwa! Ko kun taba ganin na yo na biyu ,ba na daya ba a aji fisabilillahi!
Nan ma akace a'a
Baba in baka manta ba,ni ke zuwa best student a duka darussa!
Alh.sharehu ya gyada Kansa.
To ban yarda in yi karatu a Nigeria ba wallahi?
Don bazan iya hada hanyar makaranta da su ikram ba!
Ko a nema mun gurbin karatu a Turai,ko a barshi in zauna da jahilci na!
Dama jahilci ba hauka ba inji hausawa!
Kowa ya saki baki yana kallo,tare da sauraren Ikon Allah!
Bello ne ya daka masa tsawa!
Kai! Baka da hankali ne? Har yaushe za'a samo maka gurbin karatu a private university kace bazakayi ba sai a kasar waje?
Waye sa'arka da zaka kafawa hujja anan?
Umar murmushi yayi,shi da ya dau abin hauka tsabage!
Shi ko Anas yace,karatu ne baka tashi ba!
Ikram gwalo tayi masa!
Ya kufula,ya hasala yana huci!
Malama boiler ta kalli danta Alh.sharehu!
To kai ka ji,ga ka'idar da danka ya gidanya maka kan karatun da Zai amfani rayuwar sa!
Alh.sharehu dayake mutum ne shi mai sanyi kamar ruwa,ya gyrmara zama yace,to ni bani da Matsala!
Ka je can kai da kakar ka,duk abinda kuka yanke shi zan muku!
In karatu anan din ne,ko karatu a can din!
Boiler tayi murmushi, har hakorin makkan ta ya bayyana!
To bari ka ji hukunci na Labaran! Ba na daya kake dauka a makarantun da kayi ba,ba kuma wai ka ciyo ma ubanka kyautukan yabo ba,ko kwakwalwar ka na aman albarussai,tare da harsasan wutar kokari da hazaka,to bazaka tafi kasar waje karatu ba!
Wanna kenen!!!
Heekma!
08061608583
SHUGABA🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕MATAR SARKI🏇🏇🏇🏇🧝♂🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇🏇👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀👳♀
Pg 4
SHIMFIDA!!!!!!
Malama Rukayya jajirtattan mace CE mai rayuwa a garin Kano!
Tana tsugunne a wani karamin gida a cikin tsakiyar garin Kano,inda Mijin ta ya mutu ya bar ta da yara uku!
Maza biyu,da mace daya!
Dama shi Mijin ta Dan kasuwa ne mai karamin zarafi!
Ita kuma malamar tsabta CE,irin wadanda ake kira Duba gari a da!
Anan ne ta samo sunan ta malama,haka mutanen gari ke kiran ta,haka yaranta suka tashi suna kiran ta!
Rasuwar maigidan ta dole ya sauya musu rayuwa!
Amma dayake jaruma CE,kuma a jajirce take,da dangin Mijin ta suka taso zasu raba mata yara tamkar gumbar sadaka,sai ta taso da halin wato masifa tace bata yarda ba!
A dalilin haka ne babban Santa Sharehu ya kama kasuwanci,tun kafin ma ya kammala karatun sakadire!
Daga bisani ma watsar da karatun yayi,ya nufi jihar Benue Neman kudi!
A wancan zamanin Abokin sa Sa'ad,Wanda aka fi Sani da comrade, shi ya fara muna masa FIta Daga kwaryar Kano,zuwa wasu birane kasancewar sa Dan boko ,da yawon duniya!
: Malama ta sami sauyin rayuwa!
A dalilin babban danta Sharehu da ya sami nasibi akan harkar hada hadar kasuwanci!
Sai dai ita mace CE mai kwadayin ilmin zamani!
Amma tayi tayi da danta ya koma matar boko ya ki,shi dai yafi ganewa kasuwanci!
A haka ta ba sauran yaran ta biyu ilmi.
Mai bin Sharehu shine baban Labaran jikan ta,da take fama dashi a yau!
Baban Labaran bai yi tsawon kwana ba Sam!
Don bayan an masa auren zumunci da Talatu,bai bar karatun boko ba har suka haifi Labaran!
Rana daya aka kwana dashi,ba'a tashi dashi ba a sanadiyyar ciwon ciki da yayi ajalin sa!
Ita kuma kanwar su,da ta isa aure soyayya ta kullu tsakanin ta da aminin Sharehu wato sa'ad comrade!
Ba jimawa akayi musu aure!
Anan Kano ya barta kusa da gidan malama,inda ya cigaba da yawon sa na duniya da Neman ilmi!
Itama ta sami juna biyu,ta zo haihuwa ta haifi Ikram ta mutu ta barta!
Daga wannan lokacin rikon yaran ya dawo hannun malama!
Da Alh.Sharehu ya ga haka sai ya dawo da ita garin Neman kudin sa MAKURDI jihar Benue!
A wannan lokacin Alh sharehu na da mata biyu.Su ne suka haifi Bello,Umar da Anas!
Sai dai ba kowace irin mace bace ke iya zama da malama ba!
Tsabar masifar ta,da takura yasa Matan ke tafiya a wancan lokacin!
Amma a yanzu da ya yi maganin abin ,yayi mata sashin ta daban!
Matan da yake tare dasu su biyu yanzu,basa ko shiga shirgin ta!
Asalin suna Boiler ya samu ne a daga bakin Labaran!
Amma sauran yaran su ma suna kiran ta Boiler, amma a boye!
Shi kuma dayake yana da karancin kunya ,a gaban Alh ne kadai baya amabaton ta da Boiler!
Babu kuma abinda ya haddasa wannan rashin shiri tsakanin boiler da Labaran irin yadda yake ganin Malama bata bashi cikakken kula yadda take ba Ikram!
Don a ganin sa ba fin sa tayi da komai ba!
Don me zata fi shi a zuciyar Malama???
: Tun daga ranar da akayi meeting dinnan!
Labaran ya koma yiwa Boiler ladabi da biyayya!
An dai yi na sati biyu!
Rannan ranar jumma'a!
Ya sha wanka ,ya je Masallacin jumma'a ya dawo jikin sa sanye da babbar Riga!
Duk wannan kwalliyar domin Boiler!
Yana dawowa kuwa ya tsugunna har kasa ya gayar da ita kamar gaske!
Ta amsa tana mai kare masa kallo!
Ya bata ledar hannun sa!
Ga tsarabar Masallaci malama.
Ah!to!
Yau me na samu?
Tana budewa daidai Ikram na sallame salla,ta leko kanta kallon tsaraba!
Zuma,dabino,yogurt da turare!
Ikram ta bushe da dariya.
Labaran ya daure bai kula ta ba!
Ta dau dabino ta fara ci!
Dama zancen karatu na ne,nake so kiyi wa baba magana!
Ikram ta kwashe da dariya,kace kayan da ka sanya,da kuma wadannan abubuwan da ka siyo na introduction ne kan zancen school abroad?
Hmmm! Wonders sha never end!
Kawai hararar ta da yayi,da kuma cewa yayi ina Ruwan ta?
Boiler ta hasala tace ya fita.
Labaran ya tashi tsaye yana fadin,duniya babu adalci!
Shikenan don bani da uba sai a dinga wulakanta ni???
Ya dauki ledar da ya kawo ya kama hanya!
Bazan bar muku kaya na ba,ya nufi wajen Ikram ya kama mata baki ya matso dabinon da take taunawa!
In kin isa ki ci abina shege nake!
Yar nema mummuna bakar shagwababba!
Boiler ta yo Kansa da sauri,ya cire rigar sa ya wurga mata a fuska!
Kukan Ikram yasa ta kyale shi,ta je ta kamo ta ta rungume tana bambami!
A bakin kofa ya karasa tube kayan sa,ya zama daga shi sai boxers yayi mata gwalo ya wuce!
Barr Rahma
SHUGABA MATAR SARKI Page (1)
SHUGABA 🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🎠🧕🏾🧕🏾🧕🏾🧕🏾🧕🏾🧕🏾🧕🏾🧕🏾🧕🏾🧕🏾MATAR SARKI🏇🏽🏇🏽🏇🏽🏇🏽🏇🏽🏇🏽🏇🏽🏇🏽🏇🏽🏇🏽🏇🏽🏇🏽🏇🏽🏇🏽🏇🏽🏇🏽👳🏽♀👳🏽♀👳🏽♀👳🏽♀👳🏽♀
Page 1
Boiler da Ikram suka kwanta suna jin dimin jikin juna!
Ikram CE ta fara datse musu shirun!
Idan na koma karatu Yaya zan yi? Bazan dinga ganin ki ba?
Wa? Ai tare zamu je!
N
Shiyasa kika ga na dage da koyon turanci ingilishi!
Kinsan turancin zamanin mu daban da na yanzu?
Don haka ma mu cigaba da darasin mu,tunda mun kori Labaran!
Ikram ta tashi zaune tana mai lalabo kokon kanta!
Malama ki biya na jiya in ji!
To ikrama!
Boiler tace cewa kika yimun,kwam! Shine zo!
Go! Kuma tafi!
Am am hanguri kuma, ina jin yunwa!
Kika kuma CE Sit ,shine zauna!
Sitand! Kuma tsaya!
Shin sai me?
Ikram tace to clap for yourself!
Malama ta tafa wa kanta!
Tace to duk kika yi tafi kice,myself I love you!
To!
Malama ta daddage tace,,malsef I loba u!
Sai ki kara cewa,I love you ikram!
Malama ta kara cewa,I loba u Ikrama!
To shikenan!
Yau abinda nake son ki koya Sabo shine, I hate you Labaran!
Malama ta bata rai!
Ke bar ambato shedanin yaro cikin karatun arziki!
A'a!
Ke dai ki koya,ai Zan gaya miki ma'anar sa!
To amma yanzu na Gaji,sai daiRahmatullah
wantawa suka kara yi,suna ta labarin sabuwar rayuwar da zasu shimfida in har Ikram ta sami gurbin karatu a wata jami'a mai zaman kanta a Abuja!
Zuwa wani lokaci sai ga mai aiki ta kawo abinci!
Boiler ta umurceta da ta Bude su gani.
Sai ga hadaddiyar shinkafa,da gasashen Neman kaza!
Boiler inda duk ranta yake a bace!
Ke zo nan ,ki bani kokon kanki,ki zo da akushin nan don ubanki!
Don gidan Ku,abinda Ikeama tace zata ci kenan?
Ko don dai kuturun wulakanci irin na Yan iska?
Yar aiki da ta ba shekaru talatin baya ta fara matsawa baya!
Nan fa aka kira ki don shedanci aka CE fa kiyi mata taliya da miya,amma don kin raina sarkin garin Ku zaki kawo ma mutane shinkafa!
Yar aiki da tsugunna,tare da Daga hannayen sa sama!
Wallahi su Hajiya ne suka CE inyi shinkafa!
Ungo!
Boiler ta aika mata dakuwa a fuska!
Ba Hajiya ba hajijiya!
Da ke,da Hajiya duk Baku isa Ku ture zancen ikrama ba wallahi!
Ki je ki gaya musu maza a dafa mata abinda take son ci,in ba so kuke Ku kwana a waje ba yau!
Boiler ta karasa bada umurni cikin masifa ,tare da gumi mai yawan gaske!
MAKURDI,JIHAR BENUE!!!
Ikram ta fito a cikin kyakyawar shiri!
Boiler na biye da ita rike da jakar ta!
Labaran da yayi tsayuwar zuba hannayen sa a cikin aljihu yayi fito!
Baby da boiler an hadu,har an chure!
Yau mutanen garin nan zasu sha kallo!
Boiler dai ta dake,bata CE dashi ci kanka ba!
Ikram CE tace Yaya dai gayu?
Gayu mutanen Allah!
Yaya shan panadol?
Ka dai gasa goshin ka,ka kuwa ga Zai yi kululu!
Labaran ya Shafa kansa!
Boiler kallon banza ta wurga masa a yayin da ya tsugunna har kasa yana gaishe ta cikin izgili!
Gafara!
Kaima kasan ba damuwa nayi da gaisuwar Ku ba.
Nidai in wayi gari in ji Ikrama lafiyar ta kalau!
Me kuma nake nema banda wannan?
Labaran ya tashi tsaye yana fadin ,ko in zo in kai Ku inda zaku ne?
Kafin Ikram ta amsa boiler ta karbe,A'a!
Kayi ta zaman ka a gida,tare da masu zaman gida!
Ina zan yarda ka tuka mu
River Benue ake cewa,ba riba benuwe ba!
To na ji sarkin iya yi!
A daidai nan sa'adu comrade ya ci karo dasu,ya tsugunna har kasa ya gayar da malama!
Yau ba'a fita bane? Ta tambaya cike da kulawa!
Muna nan tukun ya amsa,batare da ya dauke idon sa Daga kan Ikram ba!
Malama tace to Allah yayi jagora!
A dai daure ana Neman halaliya!
Ai kuwa wannan ya zama dole ya amsa!
Kasancewar gidan na da tsawo yasa suka cigaba da tafiya,a yayin da suke ta haduwa da Yan aikin gidan!
Sai da suka kure gida,suka yi kwana,sai ga su a wani katon falo!
Alh.Sharehu na ganin mahaifiyar sa,ya taryo ta!
Malama an fito!
Eh! Zan raka ikrama siyayya ne!
Yara ne maza su uku samari zazzaune gaban Alh.
Babban mai suna Bello ya gayar da ita!
Bana cin mike! Gaisuwa sai na roka,a matsayina na uwar ubanku??
Umar ma ya gaishe ta.Ta amsa tana fadin,kai nayi maka uzuri saboda kana da kulafuci in ka ga dama,amma kun ga wancan Anas din mai kai kamar ya dau gammo?
Kai ko ka gaishe ni bazan amsa ba! Haka kuwa akayi,ya gayar da ita,ta kawar da kanta!
Sai dai sun yi shiru da magana har sai da Alh.sharehu ya sallameta da kudi masu kauri!
Ya mikawa ikram nata!
Sai da ta duka a gaban sa,ya gaishe shi tukunna ta karbi kudin!
Malama na kallon ta cike da sha'awa! Yawwa ikrama ai haka ake so!
Amma yara ace Baku da da'a? Ai zama kudu bai yi ba.
Inama Kano ka tura su,su kiyi kyawawan halayya!
Nan dai akayi shiru har ta FIta.Saboda kowa na mugun tsoron malama!
Kwas! Kwas!! Kwas!!!
Labaran ne mai tsokana!
Sai malama
[6/15, 1:43 PM] Aisha Humaira: Malamar tsabta Boiler uwar daukar zafi!!
Malama dai bata ko kalle shi ba.
Ikram CE ta jefe shi da wani kallo.
Wallahi Labaran ka kiyayi duniya,komai iskancin ka ka rika tuna matsayin malama a tare da kai.
Wannan Hali naka babu abinda Zai haifar maka sai musiba!
Mtssss!
Good for nothing!
Labaran yayi shewa kamar mace,a cikin kishi yace da ikrama!
Sannu ke mai da'a!
Banda makalewa da kike bayan boiler kamar kaska,me kika iya??
Dallacan je kiyi brush mai kiba kamar agwagwa!
Malama ta yo kansa kuwa da gaske,ya maza ya shiga daki ya kulle kofar yana gwalo ta window!
Uwaka Talatu nace.Uwaka!
Sa'ad comrade ne ya sha ado Zai wuce!
Haba malama yau ke da Mutumin naki kuma?
Tsabar haushin sa da Ikram ke ji yasa ta juyar da kan ta!
Banda dai darajar baban ta da Mutumin nan ke ci,ko kadan bashi da farin Jinin ta!
Sai kuma boiler da take wani bashi girma kamar Mutumin kirki!
Bar ni dashi dai ta amsa wa comrade!
Shi a dole Dan zamani!
Sai nayi maka illa! Abinnan dai da kake Nema bazan bari ka samu ba.
In sha Allah!!!!
Ikram ta bushe da dariya!
Allah Sarki!
Wani bazai je abroad karatu ba!
Dole mutum ya yi karatu anan ko baya so!
Boiler ta taya Ikram dariya,tare da riko hannun ta!
Anan Labaran ya ji hawaye na zubo masa.
Rai kenan,da abinda yake so!
Rahmatullah
Barkanmu da sallah Allah ya maimaita muna👏🏽
ZUCIYA Complete
Hanyoyi 60 Da Zaka Dawwamar Da Soyayyar Matarka
Hanyoyi 60 Da Zaka Dawwamar Da Soyayyar
Matarka
1. Ka zamo mai tausasa zance a gareta, kar ka
zamo mai yawan fada.
2. Idan ka shiga gida kace ‘Assalamu Alaikum’,
sallam tana korar Shedan daga gida
3. Annabi SAW yace mata kamar kayan qarau ne
saboda haka kula dasu sosai, ka tuna akwai
alkhairi a cikinsu saboda haka sai a tarairayesu.
4. Idan zaka bata shawara ko zaka yi mata fada
ya zamo a cikin sirri, wato alokacin da kuke ku
kadai, kada ya zamo a cikin mutane dan yin
hakan muzantawa ne.
5. Ka zama mai kyautatawa matarka, hakan yana
qara soyayya
6. Idan tazo zata zauna ka tashi ka bata wurin
zamanka, hakan zai tausasa zuciyarta.
7. Ka guji yin fushi ta hanyar riqe al’wala a koda
yaushe. Annabin Rahma SAW yace idan kayi
fushi to idan a tsaye kake sai ka zauna, idan a
zaune kake sai ka kwanta.
8. Ka rinqa yin ado kana sa turare saboda ita.
9. Karka zamo mai tauri, Annabi SAW yace :
‘Nine mafi kyautatawa zuwa ga iyalina’, idan kayi
tauri da yawa baza ka samu kusanci zuwa ga
Allah ba, haka kuma baza ka zamo namiji jarumi
ba.
10. Ka dinga sauraron duk abinda matarka zata
gaya maka koda kana ganin abin bashi da
muhimmanci, hakan zai sa ta san ka damu da
ita.
11. Ka kaucewa cin musu da matarka, yana kawo
rabuwar kai.
12. Annabi SAW yace ku kira matanku da sunaye
masu dadi, sunan da suke so suji ka kira su
dashi.
13. Ka riqa yi mata tsarabar bazata, idan tana
sha’awar wani abin marmari sai ka sayo mata ba
tare da ta sani ba.
14. Ka kula da harshenka zuwa gareta, wato ka
guji abubuwan da zasu sa ta fushi.
15. Mutum tara yake bai cika goma ba, kayi
haquri da duk wani aibun da take dashi sai Allah
SWT ya sa albarka a cikin auren naka.
16. Ka dinga nuna mata yabo da godiya idan tayi
maka abu mai kyau.
17. Ka dinga taimaka mata wajen ganin ta kula
da dangantakar ‘yan’uwanta da iyayenta.
18. Ka yawaita janta da hira akan abinda take
so.
19. Idan kaga ‘yan’uwanta suna kusa, ka dinga
yabonta, kana kambamata, kana tabbatar musu
da kirkinta da kyautatawarta.
20. Ku dinga yiwa junanku kyaututtuka. Manzon
Allah SAW yace kyauta tana qara soyayya.
21. Idan kayi mata laifi sai ka samu wani abu ka
kyautata mata dashi dan ya goge laifin.
22. Ka rinqa kyautata zato a gareta, banda zargi!
23. Karka dinga kulawa da qananan laifukanta,
kayi kamar baka gani/ji ba. Yana daga cikin
‘dabi’un Sayyidina Aliyyu (RA).
24. Ka nin-ninka haqurinka da ita musamman a
lokacin da take jinin al’ada.
25. Ka ringa sauraron zuwan kishinta, kuma ka
ringa yabon kishin nata, ko manta Manzon Allah
SAW suna kishi!
26. Ka zamo mai qasqantar da kai, idan ka zamo
mai tunani to ka tuna cewa tana kula da
‘ya’yanka, itace mai kula da gida!
27. Karka dauki abokanka sama da matarka!
28. Ka ringa taimaka mata da ayyukan gida.
Manzon Allah SAW ya kasance yana taimakon
matansa.
29. Ka taimaka mata wajen girmama iyayenka,
baza ka iya takura mata taso su ba amma zaka
iya taimaka mata dan ta cimma hakan.
30. Ka dinga nuna mata cewa itace irin matar da
kake ta addu’ar ka samu.
31. Karinga tunawa da matarka a cikin
addu’o’inka, hakan zai qara qarfin soyayyar taku.
32. Kada ka dinga tunawa da baya, babu abinda
hakan zai jawo sai damuwa, abinda ya riga ya
wuce a barwa Allah.
33. Karka taba nuna mata cewa taimaka mata
kake idan kana mata wani abin kamar sayan
abincin gida, saboda a zahirin gaskiya mu ‘yan
aikatarwa ne kawai, Allah shine yake azurtawa da
ciyarwa. Wannan kuma wata hanya ce ta
qasqantar da kai ga Allah SWT da kuma gode
masa.
34. Ka gane cewa Shaidan maqiyinka ne amma
ba matarka ba, wani lokaci idan mata da miji
suna magana idan suka samu sabani sai Shaidan
ya shiga tsakani. Kayi iya qoqarinka wajen ganin
Shaidan bai shiga tsakaninka da matarka ba.
35. Ka ringa bata abinci a baki, Annabin tsira
SAW ya koya mana hakan, abincin ba wai iya
cikinta zai tafi ba idan ka bata a baki, har zuwa
cikin zuciyarta.
36. Ka kare matarka daga duk wani sharri ta
hanyar yi mata addu’o’in neman tsari.
37. Ka zamo mai yawan yi mata murmushi.
38. Ka guji duk abinda bata so ko mai
qanqantarsa, idan baka kula ba ta haka ne zai
girma har ya zama babba.
39. Ka guji yin fushi da fada a gareta, yin hakan
yana rage shaquwa.
40. Ka dinga yin maraba da shawarta.
41. Ka taimaka mata wajen samun nasara a
harkokinta na rayuwa.
42. Kullum ka zamo mai qara kusantuwa zuwa
gareta.
43. Ka taimaka mata wajen kula da yara. Wasu
mazan suna ganin kamar ba aikin su bane kula
da yara, basu san cewa yin hakan ne ma zai sa
su qara kima da daraja a idon matan da yaran
ba.
44. Ka ringa yi mata dadin baki da magana mai
taushi.
45. Ka ringa cin abinci tare da ita.
46. Duk lokacin da zaka yi tafiya ka sanar da ita,
haka kuma ka gaya mata rana da lokacin da zaka
dawo.
47. Kada ka fita daga gida a lokacin da kuka
samu sabani.
48. Gida yana da sirri kala-kala, idan ka zamo
mai fadan sirrin gidanka a cikin mutane to kana
yi wa kanka zaqon qasa ne. Sirrin gida ya tsaya
a cikin gida.
49. Ku dinga qarfafawa junanku wajen yin ibada,
ku dinga shirya zuwa Hajji ko Umrah a lokacin da
kowa bai takura ba (misali a lokacin da bata da
ciki kuma bata shayarwa) idan Allah ya baku iko.
50. Ka kula da haqqoqinta na aure
51. Allah SWT yace : « ku zauna da matanku
cikin kyautatawa », ka dinga riritata kamar qwai.
52. Idan aka zo kwanciyar aure kada kayi mata
‘hawan qawara’, kuyi wasan tayar da sha’awa
tukuna.
53. Idan kun samu sabani da matarka, kada ka
gayawa kowa, idan kayi haka kamar kabar ciwo
ne a bude quda ya hau.
54. Ka nunawa matarka cewa ka damu da
lafiyarta. Lafiyar matarka lafiyarka ce. Idan ka
kula da lafiyarta hakan ya nuna kana sonta.
55. Karka dinga tunanin ko yaushe kana da
gaskiya, mutum tara yake bai cika goma ba.
56. Ka ringa sanar da ita lokacin da kake cikin
matsala, farin ciki ko damuwa.
57. Ka dinga yafe mata idan tayi ba dai dai ba.
58. Kake yawan tuna cewa kaine bango wajen
jinginarta a lokutan wahala ko qa-qa nakayi
59. Ka karbi matarka da duk halin da take tashi,
Mazon Allah SAW yace an hallicci mata ne daga
qashin qirji tanqwararre, idan kayi qoqarin ka
tayar dashi zai karye!
60. Ka zamo mai kyakykyawan zato ga matarka a
koda yaushe, Allah yana kula da niyyarka zuwa
gareta a koda yaushe. Allah madaukaki yace:
“Kuma daga ayoyinsa ne cewa ya halitta muku
matanku daga gareku, kuma ya sanya qauna da
tausayi a tsakaninku, haqiqa a cikin wannan
akwai ayoyi ga masu zurfin tunani” (Q. Rum 21)
Ya Allah ka bamu abokan zama nagari, masu
tsoronka da yi maka da’a, kuma masu kyawun
gani.
WASIKA ZUWA GA MATASA MASU AIKATA ISTIMNA'I
WASIKA ZUWA GA MATASA MASU AIKATA ISTIMNA'I
ma'anar ISTIMNA'I shine= fitar da mani ko sha'awa da gangan ta hanyar da bata dace ba.
Matasa Maza da mata, suna neman taimako akan illolin da suke samu a jikunansu sakamakon Istimna'i wato Masturbation. An kawo hujjoji
gamsassu daga Al-Qur'ani da Sunnar Ma'aikin Allah (saw) da fatawoyin Amintattun Malamai duk akan HARAMCIN ISTIMNA'I, Amma duk da haka wasu matasan basu yarda sun dena ba.
Wasu kuwa sunji tsoron ALLAH sun riga sun dena, bubban dalilin da yake janyo musu afkawa cikin
wannan bala'in shine :
1. Kallon Fina-finan batsa.
2. Shiga shafukan internet na batsa.
3. Yin zantukan batsa tsakanin
saurayi da budurwa.
4. Kusantar zina ta hanyar kallo da
shafa, ko zance da dai sauransu.
Wasu kuma suna aikata hakan ne
dan gudun afkawa ZINA, basu san cewa shi d'inma ZINAR bane!!
Idan kun Qi bari domin Allah, to ku dubi irin illolin da yake haifar muku ajikinku mana!!!
1. MUTUWAR IDANU.
2. MUTUWAR AL'AURA.
3. CIWON BAYA.
4. BUGAWAR QIRJI.
5. RIKICEWAR TUNANI.
6. YAWAN MANTUWA.
7. KARANCIN 'YA'YAN MANIYYI.
8. SAURIN INZALI.
9. SHAFAR ALJANU, ETC.
Wad'annan 'yan kad'an ne daga cikin Matsalolin da ISTIMNA'I yake haifarwa. kuma duk wanda bai tuba ya dena ba, idan ya mutu a haka zai je ya tarar da hisabi.
DAN GIRMAN ALLAH!! Matasa ku kiyayi zina da duk dangoginta, ku Qaurace ma duk wani abinda zai rinQa motsa muku sha'awa, idan
da hali kuje kuyi aure, idan kuma babu hali, to ku yawaita azumi.
ALLAH YA SAUWAQE.
Don Allah 'Yan uwa MAZA DA MATA,
DON ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar Sharing a FACEBOOK, TWITTER, BBM WHATSAPP, da sauransu. Insha Allahu wasu da yawa zasu amfana.
Manzon Allah (s.a.w) yace: "WALLAHI IDAN ALLAH YA SHIRYAR DA MUTUM GUDA TA
DALILINKA, YAFI ALKHAIRI GAREKA FIYE DA ABAKA JAJAYEN RAQUMMA"
Wani mutum yazo wajen manzon Allah S. A.W. ya ce: Yah-Manzon-rahma zan tambaye ka rayuwar duniya da ta lahira.
1. Yah Manzon Allah ina son in zama mafi sani a cikin mutane?
AMSA
Sai ya ce "Ka ji tsoron Allah ka bi dokokin Sa."
2. Ina son in zama mafi arziQi a cikin mutane?
AMSA
sai ya ce "Ka zama mai wadatar zuci."
3. Ina son na zama Wanda yafi kowa acikin mutane?
AMSA
Sai ya ce "Ka zama mai amfanarwa."
4. Menene zai kare ni daga wuta?
AMSA
Sai ya ce "Ka zama mai yawan yin Azumi."
5. Ina so in zama mafi adalci a cikin mutane?
AMSA
Sai ya ce "Ka so ma d'an uwanka abin da ka ke soma kanka."
6. Ina son in zama mafi amfanin mutane a wajen Allah?
AMSA
Sai ya ce "Ka yawaita tuna Allah."
7. Ina son imanina ya zama ingantacce?
AMSA.
Sai ya ce "Ka gyara halayen ka."
8. Menene yake huce fushin Allah (S.W.T.)?
AMSA
Sai ya ce "Ba da zakka a boye da kyautata ma 'yan uwa."
9. Wani zunubi yafi muni awajen Allah?
AMSA
Sai ya ce "Mummunar hali shine rowa"
10. Ina so in zama mafi biyayya ga Allah?
AMSA
Sai ya ce "Ka bi umurnin Allah za ka zama mafi rinjaye a wurin Allah."
YA ALLAH Ka sa mu gama da Duniya lafiya.
INA ROQON MAI KARATU dan GIRMAN ALLAH DAN SON ANNABI kayi Qokari ka tura wani group d'in domin tunasarwa.
LABARI MAI BAN TAUSAYI......
LABARI MAI BAN TAUSAYI......
Wata rana wani yaro dan shekara 10 yana
zaune
a wani bangare na Masallaci tareda wata
kanwarsa Karama.
Yaron yana ta rokon Allah Ta'ala babu
kakkautawa . Mutane suna ta wucewa babu
wanda ya lura da yaron balle ma yasan dashi a
wajen.
Sai wani Mutum bako yazo wucewa ya lura da
wannan yaron wanda yake sanye da wassu
matattun sutura a jikinshi amma kuma a wanke
suke fes. Mutumin ya lura duk fuskar yaron ta
yi
ca6a-ca6a da kwalla.
Har yazo kusada yaron yaron bai lura dashi ba
domin ya shagaltu da rokon Allah Ta'ala.
Mutumin sai yakama hannun yaron ya ce dashi:
"yaro menene kake nema haka a wajen Allah?".
Sai yaron yadaga kai ya kalli mutumin yace
dashi: "Mahaifina baya duniya, ina rokamar
Aljannah awajen Allah ne. Rashin mahaifin
nawa
ya kan sanya mahaifiyata kuka a Kullum, shine
itama nake roqon Allah Ya bata hakurin rashin
nasa.
Kullum kuma wannan kanwar tawa tana kukan
rashin sutura, itama ina rokon Allah Ya bani
kudi
domin na dauki dawainiyarta.
Sai mutumin ya tambayi yaron: "kana zuwa
makaranta kuwa"?
Sai yaron yace: "eh"
Sai mutumin yace: "a wane aji kake karatun?"
Sai yaron yace: "bana zuwa makaranta domin
karatu, sai dai kawai ina zuwane domin yin
talle.
Mahaifiyata takan yi Awara sai nakai
makarantar, yara da dama sukan saya daga
wajena idan nakai, kuma ta hakan muke samu
mu samu abun rufawa kanmu asiri"
Mutuminnan sai jikinshi duk ya mace kamar an
zubamar ruwan Sanyi. Sai yace wa yaron:
"bakuda wassu dangi ne a garinnan?
Sai yaron yace: "Mamana takan fadamin cewa:
talaka bashida dangi".muddin bakada kudi
aduniyannan to Kai marayane Koda kuwa
kanada iyaye balle Kuma ace sun rasu! Mamana
takasance ko
yaushe bata mana karya gaskiya takan fada
mana. Amman wani lokacin idan tasa mana
abinci nida Kanwata sai muce mata muci tare
sai tace mana tagama cin nata kafin mudawo
gida. A wannan wajen ne kawai nakan ga bata
fada mini gaskiya domin nasan bata ciba domin
kawai mu koshi take fadan haka".
Sai mutumin yace: "Idan wani ya dauki nauyin
karatunka zakayi?"
Sai yaro yace: "ai hakan ba zai ta6a yiyuwa ba,
domin yawancin yan Boko sun tsani talakawa.
Babu
wani Dan Boko daya da yadamu da yayi mana
magana balle kuma ace ya taimaka mana.
Dukkannin mutanen wajennan da kake gani sun
san mahaifina amma sam basuson su Nuna sun
sanmu".
Yaron yana kuka ya kara gayawa wannan
mutumin cewa: "uncle lokacin da mahaifina ya
mutu duk wadanda na sani sun dauke mu
kamar
wadanda basu sani ba, tamkar mu wasu
baqi ne".
Mutumin nan take shima ya fara zubar da
kwalla.
Da wannan nake Kira GA al_ummar annabi da
mudinga taimakawa Yan uwanmu marayu
sabida idon muka rasu muka bar "ya" yanmu
bamusan WA zai taimakamusuba. ALLAH
yataimakemu duniya da lahira.
SIRRIN DAREN LAILATUL QADRI*
*SIRRIN DAREN LAILATUL QADRI*
*
*
Wannan Dare ne Mai Albarka Wanda Kowa Yanaso Allah ya bashi dacewa da samun wannan Dare Tare Da Samun Alhairan da yake cikinta.
*
*
Yadda Yazo A hadisai cewa Wannan Dare a nemeshi aciki kwanakin Goman Karshe Na Wannan Wata Na Ramadhan, 21, 23, 25, 27, ko Kuma 29.
>> hikiman da yake cikin Hakan domin Anaso Mutum Ya Kara Ninka ibadun da yakeyi domin ya sami sirrin ko wace Dare Mai Albarka.
*
*
Amma akwai Sirrin Sanin Haqiqanin wace Darece Wannan Dare Daga Manyan Waliyya Da Kashifai Bisa Ittifaqi Toh Wacce kenan daga cikin wadancan dararen??
*
*
Tana Kasancewa Daren 27 Ranar 26 da daddare
(Hakan Shehu Tijjani ma Ya Fada)
*
*
Sanna Kuma Bayanin Da Yazo Na Sirrin Da yake Cikin Suratul Qadri, Tanada Kalmomi guda 30,
Amma Kalmar “هي” itace Kalma Na 27, Shine Isharan Tana Kasancewa ne daren 27
*
Sanin hakan da kayi Bashi ne ya baka daman ka shantake kace baza kayi wani ibada ba sai wannan Daren,
AA a duniya ake neman Duniya Kuma Acikinta ne ake neman Lahira
*
*
Mu Kuma A Wannan Daren Ne Ake Gudanar da Karatun Jauharatul Kamal Anan Zawiyya Kusfa , Ana Gayyatar Kowa da kowa
*
*
Allah Ka Bamu Sirrin Da Yake Tattare da Daren Lailatul Qadri
*
*
(c) Zawiyya Kusfa
_ITTAKAFI DA HUKUNCE-HUKUNCEN SHI_*
*_ITTAKAFI DA HUKUNCE-HUKUNCEN SHI_*
Ma'anar ittakafi itace lazimtar masallaci da manufa ta ibada, ko kuma zama a masallaci da kudurin yin hakan a matsayin ibada ga Allah. Sabanin yanzu, inda irin wadannan wurare malamai sun jaza matan aure sa iya shiga su yi ittakfin su, tsofaffin mata kuwa akwai inda akan ware a masallatan juma'a don sallar mata, suna iya zuwa nan. Babu ittakafi akan yarinya budurwa a masallaci ko bazawara mai kuruciya a tare da ita.
*_Tsawon Lokacin Yin Ittikafi_*
Malamai sun yi sabani a kan muddar yin ittakafi malaman Malikiyya sun ce mafi karancinsa kwana daya, watau wuni daya da darensa, saboda kuwa sun sanya yin azumi sharadi ne daga cikin sharuddan ingancinsa. Wasu malaman Malikiyya sun ce mafi karancin ittikafi shi ne lahaza, misali da mutum zai shiga masallaci ya zauna yana kirdadon sallah tare haka ya yi niyyar ittikafi don neman kusanci ga Allah, wannan ya isar masa ittikafi saboda su ba su sharadanta yin azumi daga cikin sharadin ingancinsa ba.
Tsawon kwanakin ittikafi abisa maganarcin zance ba shi da iyaka, ba a gwargwaje shi ba. Musulmi ya iya shardanta wa kansa shiga ittikafi na tsawon shekara a rayuwarsa, ba zai yanke ittikafinsa ba sai a kwanakin da aka hana yin azumi. Amma wannan ga wanda ya sa azumi yana daga sharadin ingancinsa.
Amma jamhurun malamai sun karhanta yin ittakafi sama da kwanaki goma, a wasun su kuwa sun karhanta shi idan ya wuce fiye da wata daya.
*_Mustahabban Ittikafi_*
1. An so ga mai ittikafi ya yawaita nafilfili da karatun Alkur'ani da ambaton Allah (zikiri).
2. Ga wasun Malikiyya an so yawaita nazarin Hadisan Annabi (S.A.W) da litattafan Fikhu da Tafsiri.
3. Ana son mai ittakafi ya dauki tanadinsa tare da shi kamar tufafinsa abincinsa da sauran abin bukata kamar magani, wanda ba sai ya bukaci fitowa ba.
4. Ba a son yawan Magana ko hira ga mai ittakafi – ba laifi in sulhu zai yi ko wani horo da alheri ko hani ga mummunan aiki.
5. Ana son mutum ya zabi babban masallaci saboda saukin makewayi da taron jama'a salihai haka ana son mutum ya zabi goman karshe don gabatar da ittikafi shi.
6. Ana son mai ittikafi ya tsananta ibada a daren 'Lailatul kadri' idan ya ga inda zai bi wata sallah ta 'Lailatul kadri' wadda ba a tsayar da ita a inda yake ba ya iya fita ya bi wannan tsayuwar, daga baya ya komo.
*_Abubuwan Dake bata Ittikafi_*
1. Yin jima'i da rana ko da dare, koda a wajen masallaci ne.
2. Inzalin maniyyi alhalin ido biyu, sakamakon sumba ko shafa ko tsawon tunani, don wannan duk suna cikin hukuncin jima'i.
3. Cin abinci ko abin sha da rana.
4. Zuwan haila ko nifasi.
5. Canja ra'ayi ko niyya fita daga ittikafi.
6. Fita daga masallaci bada wani uzuri ba.
*_Hanzarin Da Ya Halastawa Mutum Fita Daga Masallacin Yayin Ittikafi_*
1. Hanzarin na dabi'a kamar fitsari da wanka da kashi da habo da juma'a inda yake, da sharadin in an idar da sallah ya koma kan ittikafinsa ba a hira a hanya.
2. Hanzari na tilas kamar fitowa don kashe gobara, ko kau da wani kamar makaho ko yara daga abkawa rijiya, ko tsamo wanda ya fada ruwa, wannan fita ba ta bata ittikafi.
*Ramuwar Ittikafi*
Wanda ya shiga ittikafi na tadawwu'i sanan ya yanke shi don wani uzuri, an so ya yi kara'insa a kowane lokaci ya sami yalwa.
Allah ya maimaita mana, ya karbi idadunmu.
Rubutawa:- Ãbûbäkår Êkâ.
Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
______________________________________
» Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp).
Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta whatsApp.
IDAN KAWUCE ..... KAYI BABBAN RASHI
IDAN KAWUCE ..... KAYI BABBAN RASHI =======================
KAMAR YADDA YAZOMANA.
> Watarana Annabi Musa Alaihissalam zaije ganawa da Allah Madaukakin Sarki sai ya gamu da shaidan la'anatullahi alaihi akan hanya. Sai shaidan yace dashi: "Idan ka isa domin ganawa da Allah, ka nemamin gafara mana a wajenSa".
.
Sai Annabi Musa Alaihissalam yayi gaba yaje yagama ganawa da Allah Madaukakin Sarki ammana bai isarda saqon shaidan la'anatullahi alaihi ba.
.
Sai Allah Madaukakin Sarki da KanSa yace ga Annabi Musa: "Ya musa, ka tuna da saqo, ka tuna da alqawari".
.
Sai Annabi Musa Alaihissalam yace: "Ya Ubangiji! Shaidan ya aikoni akan cewa na nema masa gafara a wajenKa.
.
Sai Ubangiji Ta'ala yace: "na yarda zan masa gafara, ammana da sharadin sai yaje kabarin Annabi Adam yayi masa wannan sujudar dayaqi yin lokacin da aka halittashi".
.
Annabi Musa Alaihissalam yadawo yafadawa shaidan saqon da'aka bashi xuwa gareshi.
.
Sai shaidan yafara ququni yana cewa: "Yana da rai ma banyi masa sujuda ba sai yanxu daya mutu zanwa gawarsa, sam ina hakan bazai yiyuba".
.
Bayan yagama ququnin nasa sai yace: "kamar yadda kayimin alfarma a wajen Ubangiji, nima zan fada maka sharruka guda uku domin ka kiyaye.
.
Don Allah Idan Ku karanta ku turawa wasu domin suma su karu kuma su amfana.
.
1. Ka kiyayi fushi, domin duk lokacin da kayi fushi, nine a xuciyarka, nine idanunka, nine a cikin jikinka, nine a bakinka, zaka fita daga kamanninka na mitanen kirki, zaka koma siffar kare, zaka iya fadar maganar da sai kadawo hayyacinka zakayi nadama alhali babu lokacin yinta. Don haka ka kiyayi fushi domin inada sharri a wajen.
.
2. Ka tuna dani a duk lokacin da musulmai da kafirai suke gwabza yaqi. Inada sharri anan, Sai nazo ina rayawa mutum cewa: "kana mutuwa wani zai aure matarka, yayanka zasu shiga kunci na maraici, Anan mutum na juyawa da niyyar zai gudu shikenan makomarsa wuta kaga nasamu karuwa kenan.
.
3. Duk ranarda namiji baligi da mace baliga suka ke6ance, zan zamto nine na ukunsu. Zan qawata soyayyar juna a xukatansu. Bazan barsuba harsai sun afka alfasha. Kayi hankali da wannan ma.
.
Malamai sunyi bayani cewa:
.
Wadannan abubuwa da shaidan yafadawa Annabi Musa Alaihissalam darasine kuma nasiha ce ga al'ummar duniya baki daya har xuwa ranar sakamako.
.
Don ALLAH katurawa Share/Copy 'Yan Uwa don su Amfana batare daka canza komai ba.
.
Ya Allah Ya Ubangijin Musa da Haruna da soyayyar dake tsakaninka da annabi Muhammad (s.a.w)
Ka samu cikin masu hadiye fushi, Kasa muna cikin masu samun babban rabo duniya da lahira......,,,
Daga yasir Umar Jega
Barka da warhaka
KARIN GASHI YAYI TSAYI SANNAN KUMA YAYI YAWA GAMI DA BAKI.
ABIN BUKATA
1. Kwai Danye.
2. Roba mai Kyau mai dan fadi
YADA ZAKIYI
Kisamu wannan kwan naki saiki dauko wannan
roba taki saki fasa wannan kwan saiki cire
kwaiduwar kwan ma'an wannan yallon abin na
ciki ki ajiye gefe daya.
Saiki juye farin ruwan kwan a wannan roba
taki.
Idan gashin naki da dan yawa saiki fasa
kwan kamar uku-kodai yada yasamu.
Saiki dinga diban wannan farin ruwan kwan
kina shafeshi a gashin naki, har saikin
tabbatar cewa ruwan kwan ya ratsa ko ina
cikin gashin naki.
Saiki barshi tsawon mintuna 20 ko 30 saiki
wanke kan naki da sabulu mai kyau kina iya
amfani da sabulun Allo berra.
Kada kimanta cewa gashi yakan sanya mazaje
kara kaunar matayensu.
ALLAH ya temaka.
YADDA AKE HADA MAN GASHI
YADDA AKE HADA MAN GASHI
ABIN BUKATA
1. Ap Oil
2. Man Shafawa
Yadda Zaka/ki Hada
Asamu Manshafawa mafi kankanta wato mai
araha sai a juye kwalbar ap oil gaba daya sai
asami wani abu a juya sosai sai a rufe bakin
tsawon minti biyu {2} ko uku {3} shikenan ya
hadu.
DOKOKIN AMFANI DA SHI
1. Mutane 2 Basa Tabawa.
2. Baa Barinsa A bude
3. Baa Amfani Da Manshafawa Mai Tsada
Sai [Locak One]
4. Baa Sawa Da Rana Sai Gari Yayi Duhu
Zaku iya yin tambaya.
YADDA AKE HADA TURAREN DAKI
Abubuwan da ake Bukata
* itacen kuskus kilo daya
* misik
* garin sandal
* farce
* madarar turaruka masu kamshi kamar
takwas
* farce da lafinta kamar roba daya
* jawil baki
YADDA AKE YI
Xa a samu kasko a dora a kan wuta a xuba
jawul
bayan an daka shi sai a dinga juyawa xai
narke
yayi baki sai a xuba itacen a dinga juyawa
har sai
ya hadu amma ba a cika wuta sosai baya
baya sai
a sauke idan ya huce sai a xuba garin
sandal
misik da farce da kuma madarorin turarenki
sai a
juyasu su hadu sosai sai ki juye a kwalba ki
rufe.
MATSALOLIN MUTUWAR AURE, BANGAREN MATA
Mata suna da matsaloli dayawa wanda yake
kawo masu rabuwar aurensu, daga cikin
matsalolin ga wasu kamar haka:
A -Kwadayi
B -Rashin biyayya
C -Rashin godiya
D -Rashin kula da dukiyar miji
E -Gasa
F -Daukar shawarar banza
G -Wulakanci
1-KWADAYI
Da yawa daga cikin mata sukan auri mutum
don kwadayin wani abu dake hannusa ko kuma
ya mallaka ko zato/saran ya mallaka, wannan
abun shine dalilin dayasa sukayi aure, bayan
anyi aure sunje gidan mijin, zasu tsaya su
tabbatarda cewa wannan abun da sukeso suna
samunshi, idan kuma yazama basu samu, to
zasu tada hankali akan cewa sai an sakesu,
wasu kuwa koda suna samu to duk sanda
akace wannan abun babushi ko kuma ya kare
to haka suma zaman su dakai yakare domin
abinda yakawosu yakare.
2-RASHIN BIYAYYA
Babban abinda mace zatayi tazauna gidan miji
hankali kwance shine biyayya, ita kuma
biyayya ta kunshi abubuwa da yawa. na farko
mace tasani cewa ta shirya yin duk abinda
mijinta keson tayi matukar bai saba ba,
sannan kuma tabar duk abinda mijinta bayaso,
sannan kuma tayi tunani da kuma kula da
dukkan abinda tasan zaisa mijinta farin ciki.
Mata dayawa basu da biyayya wanda shi kuma
namiji yake bukata, sakamakon haka dolene
aure ya rabu saboda rashin zaman lafiya.
3-KWALLIYA
Rashin iya kwalliya da kuma ado yana kawo
rabuwar aure, saboda shi namiji yanason yaga
matarsa cikin kwalliya a kowanne lokaci, zaka
samu cewa miji yakawo duk abinda ake bukata
na kwalliya amma ita kuma matar batayi, to
sai kaga yafi bukatar zama a waje fiye da
cikin gidansa domin sai matarsa tadaina
birgeshi, daganan sai yawan fada, sai kuma
rabuwa wanda wannan laifin matane.
4-ABINCI
Da yawa daga cikin mata ba’a koya masu girki
a gidajensu wanda sai sunyi aure sannan abun
ya zamar masu matsala, rashin iya girki
babbar matsalace a zaman aure wanda zaka
samu cewa duk abinda mace ta dafa babu
dadi ko kuma ba’a iyaci, shi kuma mai gidan
yana kawo duk abinda ake bukata wajen girki
amma babu biyan bukata wajen girki wanda
daga karshe idan yagaji sai kaga ya sakate
wanda wannan matsalar mace ce.
5-IYA MAGANA:
Wasu matan basusan yanda za suyi Magana
da mijinsu ba, sai kasamu cewa ga matar da
matukar kyau amma mijin baya gani saboda
rashin iya Magana, sai yaje waje ya biyewa
wadda batakai matarsa komai ba amma ta’iya
Magana, sai ta dauki hankalinsa wanda daga
karshe zaiji yagaji da ita wannan matar tashi
kuma saiya saketa ya kawo wata. Wannan
matsala ce ta mata.
6 -TSAFTA
Tsafta tana daga cikin abinda zaisa mijinki ya
soki, kamar tsaftar mahalli, da kuma yara,
namiji yanason yaga koda yaushe gidanshi da
kuma yaransa da tsafta amma wannan yayi
wahala a matan hausa/Fulani, wanda rashin
tsafta zaisa yagaji dake kuma ya tsane ta.
Cikin wani hadisi daga manzon Allah saw.yace
mana; Tsabta yana daga cikin Imini
(( Annazifatu minal Iman)) intaha".
7 -RASHIN GODIYA
Wasu matan na kasar hausa/Fulani basu da
godiyar akan irin kokarinda mijinsu yake masu,
kullum yana bakin kokarinsa amma basa gani
kuma basa godewa, wannan kuma yana kawo
matsala daga karshe daga karshe kaga anrabu
saboda yagaji.
8 -RASHIN KULA DA DUKIYAR MIJI:
Dukiyar miji tanada matukar mahimmanci
komin kankantarta, amma dayawa daga cikin
mata basa gani, sai subar dukiyar mijinsu ta
lalace suna gani wanda shi kuma mijin bayan
jin dadin haka, idan yayi iya kokarinshi bata
daina ba, karshe saiya saketa.
9 -SON GASA DA WASU
Wasu matan suna da gasar cewa duk abinda
akayi wa wata mace suma sai anyi masu
batare da kulawa da cewa mazajensu ba
karfinsu daya ba, zata matsama mijinta sai
yayi mata duk irin abinda tagani a wajen wata
macen wanda idan yagaji ko kuma bashi da
hali, to sai dai su rabu da ita.
10 -DAUKAR SHAWARWARIN BANZA
Wata macen bata da matsala da mijinta amma
tana daukar shawarar banza daga ‘yan uwa da
abokai, sukan bata shawarar banza akan
abinda zata yima mijinta ta cutar dashi ko
kuma ta hanyar sanya shi abinda baya iyawa
wanda idan dai baiyi suba sai dai ya saketa
11-WULAKANCI
Mata dayawa sukanso suringa wulakanta
mutanen da suka shafi bangaren mijinsu,
kamar iyayenshi, yan’uwanshi da kuma abokan
arzikinshi domin damar data samu ta zama
matar dansu, dan’uwansu ko abokinsu wanda
wasu mazan basa yarda da wannan to idan
har macen bata daina ba to sai su saketa,
12-MATSALAR AURE, BANAGAREN IYAYE
Iyaye suna da matsala wadda daga karshe
suke mayarda diyarsu jawara, su kuma
wannan matsalolin sune kamar haka:
• Auren Dole
• Kwadayi
• Rashin bincike
13-AUREN DOLE
Iyaye suna haddasa matsala wadda daga
karshe take kawo saki wato itace matsalar
auren dole, wasu iyayen suna takurawa ga
yayansu kan cewa sai sunyi masu auren
zumunci ko sunaso ko basuso wanda yin
hakan yanada matsala sosai don zakaga cewa
babu zaman lafiya bayan anyi auren domin
basu son juna ko kuma daya bayaso to babu
zaman lafiya wanda akarshe dole sakinta zaiyi.
Sannan wani auren dolen kuma bana zumunci
bane amma saboda iyayen suna tare ko abokai
ne saisu hada ya’yansu aure akan basa so
kuma karshe dole zai saketa.
14-KWADAYI
Sannan na karshensu shine auren dole domin
kwadayin abin duniya, don ganin cewa wanda
zai aureta yanada abin duniya kuma suna
ganin idanta aureshi zata samu kuma suma su
samu, to sai suce dole saita aureshi wanda shi
kuma yasan dalilinda dayasa aka bashi ita, to
duk ranar da yagaji da ita kawai sakinta zaiyi
domin dama yasan bata sonshi.
15 -RASHIN BINCIKE
Wasu iyayen basa bincike akan wanda yake
neman diyarsu ko kuma diyarda dansu yake
nema, sai azo ayi neman aure har a daura
aure batare da cikakken bincike ba, sai bayan
anyi auren sannan asami babbar matsala
wanda dole zasu rabu ya sake ta.
DAGA KARSHE:
Bincike a kotunnan gargajiya ya nuna cewa
duka ana samun kowa da laifi amma wa’anda
sukafi laifi sune mata wanda suke da kashi
arba’in da hudu (44) cikin dari na laifin
mutuwar aure, su kuma maza suna da kashi
talatin da daya (31) na laifin mutuwar aure, su
kuma iyaye suna da kashi Ashirin da biyar (25)
na laifin mutuwar aure a kasar Hausa/Fulani.
*A short story* *True life story*
*Ummee mukhtar*
*A short story*
*True life story*
*YAFARU DA GASKE* *4DAYS AGO*
*19 GA WATAN RAMADAN*
*MUTUWAR BANKWANA*😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭
Wani yaro ne wanda shekarunsa 13 kwance yake akan k'afar mahaiiyarsa wacce suke kira da inna, ta zuba hannayenta biyu a fuska tayi tagumi da alama akwai abinda ke da munta, ibraheem ne wanda yad'ora kansa a cinyarta ya juyo yana kallonta , yace inna menene meke damunki? Nan hawaye suka zubomata ta share fuskarta tace bakomai nan ya tashi zaune yace inna kifad'i gaskiya kode bashishshikan da ake binkine suka dameki? tace a 'a yace tokiyi hkr insha Allah idan na girma nai kud'i zansiya miki babban gida keda babana da k'anne na zan kaiki makkah zan dibo miki masu yi miki aiki kinji inna ki dena damuwa komi ze wuce.
Nan tai murmushi tajawoshi jikinta tace ibraheem kana sona kana tausayina gakade qarami amma kanada hankali Allah yaimaka albarka yace ameen inna
Qannensane suka shigo da gudu suna wasa 'yar autarsu ce ta dubeshi tace kai kaullum kana kan qafar inna koni bana hawa sekai dariya yayi yace to ai ban hanaki hawaba .
Nan yaran suka shiga daki suna wasa
Ya qara kallon inna yace inna ki hkr kinji zamuji dadi anan gaba Insha Allah ,yace yauwa inna jiya kinsan mafarkin danayi ? Da murmushi a fuskarta tace a a gayamin
Gyara kansa yayi kan qafarta yace inna jiya nai mafarki wai gani a wani waje me girma na zama kamar balarabe se ciye ciye nake kayan kuma ga dadin wallahi
Dariya tayi tace gidan zeyi na makwaftammu....? Yace a'a inna shifa wannan gun bangama farkonsaba bare qarshensa gurin me girma ne inna amma ina farkawa naganni anan . Dariya takumayi tace lalle ibaraheem to baka ganni a wajenba.? Yace inna bake awajen ni kadaine amma ingafa kuma kuna gidan kawai a zuwan kuntafi unguwane
Ai batasan sanda ta qara yin dariya ba shima dariyar yake yace inna ran yaushe aka haifeni .? Tace juma'a
Yace kuma yau juma'a ko? Tace eh.
Yace inna kozaki qara min yawan awaran danake siyarwa danya tinda kinga azimine kuma ina ciniki
Tace a'a wannan kwano 1 ma Allah yasa mata albarka yace da kin qaramin .
Tace a'a kai hkr yace to bari nakai niqan ko
Bayan ya dawo dg kai niqa yace zetayata aiki tace a a yaje yadanyi wasan sa da abokansa tinda tallan se anjima.
Yace shide seya tayata tace a a yace to harze fita tace niko ibraheem da gobe karkai azimin nan tinda akafara fa bakasha ko daya ba yace inna ai sena kai 30 cif tace aiko sekasha so kake kayan sallah su maka yawa ?
Yace ni daba a dinkamin bama ai wa qanne na tace bakoso yace kawai bana dokin sallar ne
Inna sena dawo tace to karka jima.
Yace to yana fita yaga abokansa zasu wanka rafi yace ina zaku sukace wanka yace sekun dawo
Sukace bazaka ba nan yai shiru kamar karyaje yace sekuma yace bazamu jimaba?
Sukace eh nan suka tafi wanka rafi
Wani qaton kududdufi ne wanda aka fara aikinsa amma sanadiyyar sace daya daga cikin turawan da suke aiki awajen se suka daste ruwan yazamana cewa ya taru waje daya nan yara suke wanka
Bayan 2day aka sako baturen bayan ambiya masu garkuwa da mutanen kudi
Suna isa suka fara wanka yazamana cewa kowa daga shi se gajeran wando da ike ruwan ya rabu 2 susecen sukai wani 6arin yayinda ibraheem yai wani 6angaren da ban .
Nan suka gama wankan suka tafi yayinda suka manta dashi .😭
Watace tazo wucewa anan taga gawar ibraheem ta ruga da gudu taje ta fad'a agidansu .
Nan mahaiiyarsa da babansa suka rude se kuka take da gudu ta nufi kogin yayinda aka bugawa yan kwana kwana waya akazo aka fidda ibraheem daga ruwa a sanqame amma idan ka kalle shi sekaga kamar yana murmushi Allah sarki rai yayi halinsa
Ibrahim ya mutu ran juma'a
Yana me dauke da azimi abakinsa
Yayi mutuwar shahada acikin ruwa
Sannan yazo duniya ranar juma'a bayan sakkowa daga masallacin juma'a aka haife shi😭
Tabbas inna ta shiga tashin hankali domin shika daine a yaranta yake nuna mata soyaiya da tausayi da alqawari kala kala najin dadi daze nuna mata idan ya girma.
Yau kwana 4 da mutuwar ibraheem muna addu'a Allah yajik'ansa yasa ya huta mafarkin da yai Allah yasa yazama gaske 👏🏻
Allah yasa mucika da kyau da imani yasa mi kyakykyawan qarshe ameen.👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻😭
HUDUBAR ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM WANDA YAYI A KHUDUBAR RANAR TARA GA WATAN ZUL-HIJJAH, SHEKARA TA GOMA DA HIJIRA A DUTSEN ARAFAT (RANAR ARFA KENAN
*HUDUBAR ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM WANDA YAYI A KHUDUBAR RANAR TARA GA WATAN ZUL-HIJJAH, SHEKARA TA GOMA DA HIJIRA A DUTSEN ARAFAT (RANAR ARFA KENAN).*
*ANNABI (SAW)YA FARA DACEWA:*
```“Ya ku mutane ku bani hankalinku, domin mai Yiwuwa bazan sake kasancewa da ku bayan wannan shekaran ba, saboda haka ku saurari abinda nake gaya maku da kyau, kuma (ku isar da abinda zan gaya maku) ga wadanda basa wannan wuri a yau.
Ya ku mutane kamar yadda kuka riki wannan wata, (na hajji) da wannan rana (ta arfa) da kuma wannan gari (na Makka) da girma kuma abin tsarewa, to, haka kuma ku riki Ran Musulmi da kuma Dukiyoyinsu da girma abin kuma karewa, ku maida wa Mutane kayan da suka baku Amana. Kar ku cuci kowa, saboda kar wasu su cuce ku, ku tuna fa, hakika ALLAH zai yi sakayya akan ayukakanku, ALLAH (SWT) ya hana cin riba,(wato kudin ruwa) saboda haka, duk abin da aka kulla ta kudin ruwa sai an warware shi.
Ku yi hattara da shaidan, domin kiyaye Addininku. Yanzu kan ya fidda ran batar da ku akan manyan abubuwa (na sabo) saboda haka ku guji binshi akan kanana.
Ya ku jamaa hakika kuna da hakki bisa matayenku, amma suma suna da hakki bisa kanku, to hakkin su ne akanku da kuciyar dasu, Kuma ku tufatar dasu akan jin kai. ku bi dasu kyakkyawan biyarwa, ku kuma tausasa musu domin su majibintan al amurran kune, kuma mataimakan ku, Hakki ne akansu da kar su yi abota da duk wanda ba kwa so, kuma su nisanci zina.
Ya ku jama'a kuyi kyakkyawan bauta ga ALLAH (SWT) ku tsaida salloli biyar(5) na farilla, Ku Azumci Watan Ramadan ku Kuma bada zakka. Ku aikata aikin hajji in har kun sami daman yi. KU SANI FA, ko wane musulmi dan uwan musulmi ne. Dukkan ku dai dai kuke. Ba wanda yake da fifiko saman wani sai ta tsoron ALLAH, da aikata kyawawan ayyukka.
Ku tuna fa(ya ku jama'a) wata rana za ku tsaya gaban ubangijinku, domin sakamakon ayyukanku, saboda haka ku yi hattara kada ku yi sake da hanya madaidaiciya bayan na kau.
Ya ku jama'a ba wani annabi ko manzo da zai zo bayana kuma babu wani addini da zai zo (bayan addinin musulunci), saboda haka kuyi tunani sosai akan wannan magana dana gaya maku, kuma ku fahimce ta (sosai).
Zan bar maku abubuwa guda biyu (2); ga (alkur ani) ga kuma (sunnah) ta. In kun bi wannan ba za ku ta ba bata ba. Duk Wanda ya ji wannan sako to ya jiyar da wadansu, suma su jiyar da wasunsu, kuma sau da yawa wadanda za su ji magana daga karshe sufi masu ji na yanzu fahimtar abinda nake fada.
YA ALLAH ka zamo shaida agareni, cewa na isar da aikenka zuwa ga bayinka.” Yan uwa ku watsa wannan KHUDUBAR ga yan uwa musulmi wanda kamar yau akayi ta!!!
Allah duk wanda ya tura wannan khuduba ya Allah ka sadashi da annabin MuhammadMuhammad (saw) ya Allah kabiya masa dukkan bukatunsa na alkhairi```
TAMBAYA
TAMBAYA
========
👇
Assalamu Alaikum Malam ya azumi Allah ya sa mudace ameen, Malam inada tambayoyi guda biyu
1. Malam macce ce budurwa ke ciyon mara koda ba lokacin al'adarta ba to shi ne Malam ko mi yake kawo wannan matsalar.
2. Malam Dan'uwana yana raba zakka dai dai wannan lokacin yana baiwa yan uwanshi to yanzu sai masuyin garkuwa da mutum sunka kama Dan uwanshi suka ce sai anbasu miliyan biyu da dubu Dari uku to Malam zai iya yin amfani da wadannan kudin na zakka da yake rabawa domin ya kwato Dan uwanshi a hannun wayannan azzalumai? kuma Malam muna Neman addu'a Allah ya kwato muna shi a hannunsu ya dawo gida cikin koshin lafiya.nagode.
AMSA
=====
👇
1. Aure zakuyi mata, wannan shine matsalarta, wato Rashin Namiji yana haddasawa mace irin Wannan matsalar.
Sabida haka Ku daure kuyi mata Aure, insha Allahu zakuga ta sami sauki.
2. Wannan kuma bai Halatta a dauki kudin Zakka a baiwa masu garkuwa da mutane ba, sabida Allah bai sanya masu garkuwa da mutane a cikin jerin wadanda za'a baiwa zakka ba.
Abu na biyu kuma, yaya zaiyi inda Ace ba lokacin da zai bayar da zakka bane? Sai yace bazai fanshe shi ba, har sai lokacin fidda zakka yayi zai bayar ya fanshi dan uwansa kenan?
A takaice dai gaskiya bai Halatta ba.
Ita zakka ana bayar da ita ne ga mutanen da Allah yace a baiwa, Wato Talakawa, Miskinai, wanda yayi aikin fitar da zakkar, wanda ake tsammanin zai iya shiga musulunci idan an masa kyautar kudi, matafiyi, da wanda Wata mummunar Hasara ta sameshi, kamar gobara ko aka masa sata ko ya dauki nauyin biyan bashi kuma bai sami dama ya biya ba.
Allah Shine Masani
✍
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAXA MATA 08108605876
ADDU'AR DA AKE YIWA WANDA YA SANYA SABUWAR TUFA
*Addu'ar da ake Wa wanda ya sanya sabuwar
tufa.*
" ﺗُﺒْﻠِﻲ ﻭَﻳُﺨْﻠِﻒُ ﺍﻟﻠﻪُ ﺗَﻌَﺎﻟَﻰ "
Tublee wayukhliful-lahu ta'ala
Allah ya sa ka mayar da ita tsumma, kuma Allah
madaukaki ya mayar maka da wata (tufar).
" ﺇِﻟْﺒِﺲْ ﺟَﺪِﻳﺪﺍً ﻭَﻋِﺶْ ﺣَﻤِﻴﺪﺍً ﻭﻣُﺖْ ﺷَﻬِﻴﺪﺍً "
Ilbas jadeedan waAAish hameedan wamut
.shaheedan
(Allah ya sa) ka sanya sabo, kuma ka rayu kana
abin yabo, kuma ka mutu kana shahidi (wanda
aka kashe a tafarkin Allah).
___________________________________