GYARAN JIKI, HANNU DA KAFA
Assalamu Alaikum muna godia da yabawa da
wannan gudummua da ake bamu Allah ya saka
da alkhairi ina son kayan gyaran jiki hannu da
kafa pls.
iRashyder
Wa'alakumussalamu warahmatullah....
GYARAN JIKI
Da farko dai shi gyaran jiki yana matukar bukatar
kulawa tare kuma da daukan lokaci. musamman
idan akace jikin is very dry. amma hausawa
sukace hakuri da dauriya shi ke kai mutum ga
samun nasara.
duk da cewa a farko zaki ga
kamar baya aiki amma duk inda kika dauki wata
daya, wata biyu, kina yi dole sai an ga chanji a
tare da ke.
akwai hanyoyin gyaran jiki kamar
haka
1-RUWA
Kamar yanda nasha fada shan ruwa da yawa yafi
komai muhimmanc ga rayuwan dan adam. rashin
ruwa a jiki yana sa jikin mutum ya bushe ya
tattare da wuri. rashin ruwa a jki yana sa saurin
tsufa da saurin kamua da cututtuka masu dama.
dan haka muke shawartan mutane da su rika
shan ruwa akalla kofi takwas zuwa goma a ko
wacce rana. sannan ruwan ya kasance
tsaftatacce.
2-WANKA
Yin wanka sau biyu a rana na daya daga cikin
manya manyan hanyoyin gyaran jiki
• Tsaftataccen ruwa, soso mai laushi, sannan a
yayin zaben sabulun wanka mutum ya nemi na
kalar fatar sa wato dry skin oily, normal skin ko
kuma for all skin types.
3- TAUSHIN FATA ( EXFOLIATE )
Yin wannan sau biyu zuwa uku a sati yana
kankare dattin jiki tare da kankare matattun cells
din dake saman fatan mutum wanda hakan ke
haifar da taushi tare da santsin fata. Zaki same
shi a shagon kayan kwalliya dauke da suna
kamar haka EXFOLIATING CREAM KO BODY
SCRUB sannan zaki iya hadawa a cikin gida
kamar haka:-
GA MASU YAWAN MAIKO A JIKI KO FUSKA
• Lemun tsami
• Suga ko gishiri
• Ki kwaba ruwan lemun tsami da suga kafin
sugan ya gama narkewa ki riqa deba gina goge
fuskan dashi.
• bayan minti 30 ki dauraye da ruwan sanyi. Sau
daya zuwa biyu a sati
GA MASU YAWAN BUSHEWAN JIKI
• Suga ko gishiri gwangwani daya
• Man zaitun ko almond ko man cika gida (castor
oil) rabin gwangwani
• Zuma kwatan gwangwani
• Lavenda oil ko wani mai kamshi chokali daya
• Ki hada su wuri daya bayan kin gama wanka ki
shafa shi ki dan dirje jikin ki dashi sannan ki jira
minti biyar ki dauraye da ruwa ki fito
• Wannan hadin zai kai tsawon sati biyu ba tare
da ya lalace ba.
GA WADANDA JIKIN SU IS NORMAL zasu iya
amfani da kowanne daga cikin wadannan biyun.
4-YAWAITA SHAFA MAI
Muatane da yawa basa son shafa ma ajikin su
suna ganin cewa ba wata damua to akwai
damuwa kokuma a shafa a kafa da hannu da
fuska kadai shi yasa lokuta da dama sai kaga
jikin mutum yayi dabbare dabbare ko ina kalarsa
daban. Please mu riqa amfani da man shafawa
masu kyau ban a bleeching ba. Idan kinyi amfani
da wannan baki ji dadin sa ba kar ki kuma sayan
irinsa ki nemi wani har sai kin samu wanda kka ji
dadin sa daga nan sai ki cigaba da siyan irinsa.
Sannan ya kamata mu san wannan:-
• BODY CREAM KO BODY LOTTION wannan a jiki
kadai ake shafawa banda fuska shafa shi a fuska
zai iya kawo matsala kamar na kunan rana,
kuraje, da sauran su.
• FACE AND BODY CREAM\LOTTION wannan
zaki iya amfani dashi a jiki da kuma fuska baki
daya.
• FACE \ FACIAL CREAM wannan fuska kadai
• Da sauran su. Al muhim dai mutum ya karanta
jikin mai sosai sannan ya duba kwanan watan da
man zai lalace wato expiring date kafin ya saya.
5-KARE JIKI DAGA RANA
Rashin shiga rana yana daga cikin abinda yasa
jikin yara yake da taushi da sheqi. Don haka duk
lokacin da mutum zai fita ya riqa yawan amfani
da sun protecting cream (SPF) ko kuma ki sanya
nikabi.
Musamman ga mata masu amfani da man
bleachin rana zai iya kona fuskar ta zama ja idan
basa neman kariya daga rana.
BONUS RECIPES
SANTSI DA SHEKIN FATA
• Aloe vera gel chokali daya
• Kurkum rabin karamin hakali
• Zuma chokali daya
• Madara chokali daya
Ki kwaba su gaba daya ki shafa daga fuska zuwa
wuyan kin a tsawon minti 20-30 ki wanke da
ruwan dumi.
NA BIYU ZAKI SAMU
• Gwanda ko kabewa dan kadan
• Garin sandal karamin chokali
• Zuma chokali daya
Ki kwaba sosai ki shafa na tsawon minti 20-30 ki
wanke da ruwan sanyi.
NA UKU ZAKI SAMU
• Ruwan rose (rose water)
• Bayan kinyi wanka da safe da daddare ki rika
shafa shi yana bushewa ajikin ki kafin ki shafa
mai
YANDA AKE HADA ROSE WATER
• Zaki samu fulawan rose ki tsitsigeta ta kai
kaman kwatan kofi sannan ki sa ruwa sama
sama ki dauraye ta
• ki dauko tafasashen ruwan ki da ya huce rabin
kofi ki tace ki zuba a roba mai tsafta
• sannan ki zuba furen acikin ruwan ki rufe ki
lullube shi ckin kaya mai duhu na tsawon kwana
uku
• ki juye a tukunya mai tsafta ki dafa har sa
kinga kalar furen ya bace sannan ki sauke ki
tace ruwan.
Ki bari yayi sanyi sannan ki fara amfani dashi.
Wannan hadin zai kai tsawon wata daya baiyi
komai ba matukar an hada shi da ruwa mai kyau.
A gaba zamuyi bayani akan amfanin rose water
inshaa Allah.
GYARAN HANNU DA KAFA
TAUSHIN HANNU
Ki nemi hand cream mai kyau ko kuma
• ki nemi man kwakwa ki ajiye a kusa duk lokacin
da kika gama wani akin gida ki daraye hannun ki
ki sha da daddare ma haka kafin ki kwanta.
• Ki nemi man zaitun ki kwaba da suga ko gisiri
ki riqa goge hannunki da shi sannan ki shafa mai
ki sa safan hannu ki fara aikin ki.
TAUSHIN KAFA
• Ruwan dumi kisa man kwakwa kadan a ciki ki
tsoma kafarki bayan ruwan ya huce sai tsame
kafar ki sa dutsen goge kafa sama sama kid an
goge fatar da suka taso sannan ki dauraye ki
goge da tawul ki shafa man kade ki kulle da leda
ki sa safa (musamman ga masu kaushin kafa)
• Yawaita shafa wa kafar mai har tafi zai taimaka
wurin lausasa ta.
ALLAH SHINE MASANI………. ALLAH YASA MU
DACE AMIN.