Gyaran Jikin cikin sauki

Tags

Assalamu alaikum un uwa


ADO DA KWALLIYA
Assalamu alaikum wa rahmatullah. Last week
mun fara magana akan Ado inda aka ce idan
mutum na so yayi ado to Abu na farko da ya
kamata Ya fara gyara wa ita ce zuciyar sa.
zuciya kua ita ce halin mutum domin idan zuciyar
ki bata da kyau zai nuna a halayen ki da dabi'un
ki komai daren dadewa wanda alokacin kyawun ki
bazai amfanar da ke komai ba.
Haka nan kuma idan kikayi wa zuciyar ki ado da
alkhairi komai tsanar da mutum zai maki dole
akwai sashi na zuciyar sa da take mutumta ki
shakkar ki da kuma daraja ki kuma take kishin ki
tana Jin dama itace ke domin halayen ki bana
mutanen banza bane. Allah ya sa mu dace Amin
ADON GANGAR JIKI
Uhmm..... Mata akwai aiki!
Kada ki zauna tibis! Wai ke kin iya makeup
(kwalliya ) sabda haka ke baki da matsala no no
no no! Natural beauty matters alot in fada maki a
matsayin ki na mace yana da matuqar
mahimmanci a iya banbance fatar ki da ta namiji
a kallo daya, amma mu kam sai a slow walh
wata ma da za'a samu makaho a miqa masa
hannun mace da namiji sai yace mijin ne macen
tou yaji abu kamar katako Jiki duk tabo.. qafar
nan tayi kwatsa kwatsa, gashin kan nan nata
kamar ka bude masai, haqora ba kyawun gani
kumba tayi baqi fuskar nan tata....... Haba yar
uwa yanxn baki da wani excuse birni ko kauye
da zai hana ki gyara jikin ki.
Sai aikin kallon idian films American films da
sauran su basa amfanar dake komai.... tou wai
ance maki a banza suke sa qananan kaya su bar
jikin su a waje? Me yasa ke idan kin sa baya yi
maki kyau? Shin kou kin taba ganin stretch Mark
(nankarwa) a jikin su? Kin taba ganin tabbai
barkatai a jikin su? Ko kuwa dai basa gyara
gashin kansu ne? Qafar su yaya take? Hannayen
su yaya suke? Tumbin su fa? Shin kin taba ganin
ance muguwa ita taci riba a film? Koda zata ci
riba tou kuwa sai ta chanza hali. Haka nan idan
kazamiya ce sai ta zama mai tsafta no be so?
Tou kema ki dauka kullum film din kike yi amma
ta hanyar Allah da Manzonsa.
Don haka akwai abubua da kike buqata kafin kiyi
wa jikin ki Ado
ABUBUWAN BUQATA
idan kina sou ki gyara gangar jikin ki abu ne mai
sauqi amma kuma mai matuqar wahala sannan
yana buqatar hakuri da naci farkon abinda zaki
fara yi shine
1) ki yarda cewa KE MAI KYAU CE
duk abinda mutane zasu fada game da kamannin
ki kada ki damu ke dai kawai ki yarda cewa ke
din kyakkyawa ce domin Allah baya abu Marar
kyau ko ba haka ba? Kar ki yarda wani ko wata
su kira ki da mummuna ki amsa domin ke ba
mummuna bace. Don haka ki yarda da kanki sai
mutane su yarda da ke domin dai yanxn duniya
yanda ka dauki kanka haka mutane zasu dauke
ka
2) ki kasance mai SON KI
Hakan ba wai ina nufin ki kasance mai son kai
bane a'a... Ina nufin ki qaunace kanki sosai duk
abin da kika San zai cutar da jikin ki komai dadin
sa ki guje sa haka nan duk abin da zai amfani
jikin ki komai rashin dadin sa In dai bai saba wa
Allah da Manzonsa ba Tou ki rungume sa. Am
telling you zaki ji dadin hakan.
Wannan sune abubuwan da kike bukata kafin ki
fara gyaran jiki kar ki zama mace wacce komai
ta samu bakin ta kawai ta sani babu aji acikin
yin hakan ba zai amfanar da ke ga komai ba.
Yanxn zamu lissafa abubuwa wa'enda suke
buqatar gyara a jikin mu domin dai kullum tsufa
muke yi ba zama yara ba.
ABUBUWAN DA GYARAN JIKI YA QUNSA
Gyaran GASHI
Gyaran FATA
Gyaran FUSKA
Gyaran BANGAREN JIKI TA SAMA
Gyaran TUMBI
Gyaran BANGAREN JIKI TA QASA
Insha Allahu next Zan fara Bayani akan ko wanne
daga cikin abun da na lissafa tare da remedies
dinsa (yanda zaki Kiyaye sa) idan so samu ne
ma har da videos. Wslm
AdoDaKwalliya