HausaNovel: KE DUNIYA Complete

👉🏻 🌎 *KE DUNIYA* 🌎👈🏻




*Written &  story by*
*Zee Elkaseem (Mmn khady)* 😘




page 1---5



*Just a short story*




*Amincin Allah ya tabbata A gareku masoyana Aduk inda kuke* 🙏🏻

💃🏻 *Allah yanufeni nayi dawowa dawata tsaraba dan faranta Ranku masoyana*❤





✍🏻 Zaune take kan kujera a faffad'an tsakar gidanta ta buga uban tagumi da hannu biyu, ba abinda take tunani sai yanda Halin mijinta ya canca cikin kwanakin dabazasu wuce kwana 30 ba,

Maganar arzi'ki bata had'asu kullum cikin tashin hankali suke, fitinar yau daban ta gobe daban, duk iya 'ko'karinta na ganin ta kaucema rigimarsa amma abin yaci tura.

"Assalamu Alaikum" 'yan'matan suka had'a baki gurin yin sallama, ganin Maman tasu tsakar gida zaune kuma bata amsa sallamarsuba, bai basu mamakiba, dan sunsan cikin halin damuwar datake ciki.

Hafsa ce tanufi d'aki dan ajiye jikkar islamiyyarta, tare da cire zundumemiyar hijab d'inda ke jikinta, itama Amina bin bayanta tayi Al'qur'anin dake hannunta ta ajiye itama ta cire hijab d'inta tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, suma 'yan'matan kallo d'aya zakayimasu ka tabbatar da suna cikin damuwa.


Tare suka fito zuwa tsakar gidan har yanzu mamansu tana inda suka barta, wannan karon hawayene sharkaf a fuskarta,

Cikin tsananin tashin hankali suka iso gareta, suna gogemata hawaye, Hafsa cikin muryar kuka take magana "Mama kiyi ha'kuri dan Allah, ki d'auki wannan amatsayin kaddara, kuma inshaAllah kome zai wuce kamar ba'ayiba"

Girgiza kai mamantasu tayi tare da jawo 'ya'yan nata ajikinta ta rungumesu hawaye na suntiri akan fuskarta cikin sheshshekar kuka tace  "Hafsa nagaji da Halin mahaifinku, nayi bakin 'ko'karina na ganin na kaucema duk wani rashin jituwa da zai shiga tsakanina dashi amma abun kullum gaba yakeyi, yau harta kai ga mahaifinku ya d'aga hannu ya dokeni,"
s
Su duka d'ago Kansu sukayi a firgice suka kalleta, sai lokacin suka lura da yanda fuskarta dukta kumbura alamar buguwa, "Innalillahi Amina tari'ka maimaitawa, " mama yanzu babane yamaki wannan dukan, munshiga ukku suka fad'a tare da fashewa da kuka,

Kuka sukacigaba  dayi suduka ba mai rarrashine wani saida sukayi mai isarsu, sannan sukayi shiru dan Kansu,

Jin anata kiraye-kirayen sallar azahar yasa suka tashi suka d'aura Al'walla suka shiga d'aki,
'Katuwar dadduma suka shimfid'a sukayi sallah sundad'e suna kwararo addu'a akan Allah yayi masu maganin matsalar dasuke ciki sannan suka tashi.

Hafsa da Amina kuwa kitchen suka nufa dan wata fitinanniyar yunwa sukeji,
Basu samu wani abunciba a kitchen d'in haka yasa suka dawo d'aki dan tambayar mamansu.

Halin dasuka isketa cikine yayi masifar d'aga hankalinsu, Dan kwance take tanata magowa ta dafe 'kirjinta da hannu biyu,

Da sauri suka isa gareta tare da tallabo kanta suna kuka, suna fad'in innalillahi wa,inna'ilaihirraji'un" Hijab dinda ke 'ko'karin sha'ke wuyanta saboda yanda take magowa suka ciremata, lokacin ta had'a wata uwar zufa kamar anmata wanka da ruwan zafi, wani yunkuri tayi mai 'karfi tare dayin Amai.

"Innalillahi" suka furta atare lokacin da saukaga aman da mamantasu tayi jinine hada gundari.

Da gudu Amina tafita tana Neman taimako, cikin sa'a kuwa tasamu makwabcinsu Alh shu'aibu mutumin kirkine duk unguwar ana yabonsa saboda kyawawan halayensa,

Shitagayama halinda mamansu take ciki, cewa yayi taje gida gashinan zuwa, matarshi Haj Zainab yafara turawa dan taimakama marar lafiya.

Tana shiga ta iske halinda Halima take hankali tashe ta kamata suka fito lokacin Alh shu'aibu ya fiddo mota suka sanyata sai *federal medical center* dake cikin garin Emergency aka nufa da ita, saida aka d'auki kusan awa 5 da ita a emergency sannan tad'an dawo hayyacinta I.c.u aka maidata dan har yanzu jikin nata sai ahankali.







Comments dinku shine zai 'karfafamin gwiwa, amma idan babu comments zan dakata 🤷🏻‍♀
👉🏻 🌎 *KE DUNIYA......* 🌎👈🏻
       



*Written &  story by*
*Zee Elkaseem (Mmn khady)* 😘




page 5---10



*Just a short story*




Hafsa da Amina kuwa tunda aka fita da mamansu zuwa Hospital suketa rizgar kuka kamar ransu zai fita.

Da misalin 'karfe Hud'u na yamma Alhj Sani yayi sallama yashigo gidan, bai ko kalli d'akin matar tashiba yawuce d'akinshi dan yanzu baya 'kaunar ganinta ko kad'an.

Jin sheshshekar kukan dake tashi a gidan yasa yaji wani kududun bakin ciki ya turni'kesa dan a zatonshi Halimace matarshi ke kuka dan yasan duk randa ya6ata mata rai yini take kuka.

Cike da bala'i yafito daga d'akinsa zuwa d'akinta da niyyar ya saukemata kwandon bala'i,

A sukwane ya isa ya yaye labulen  yafad'a cikin d'akin.

Da sauri Amina da Hafsa suka d'aga jajjayen idanunsu suka kalleshi, shima wani fad'uwar gaba yaji ganin yanda 'ya'yan nashi suka fita hayyacinsu cikin 'kan'kanin lokaci.

Tambayarsu yayi zuciyarsa cike da fargaba,

Aminace tayi 'karfin halin gayama Baban nasu Halinda mamarsu take ciki.

Hankali tashe yakira Alhj shu'aibu ya tambayeshi Asibitin dasuke,

Da Sauri ya watsa ruwa ya canja kaya, yacema su Hafsa zaitafi hospital d'in.

Suma mi'kewa sukayi suakace "baba Dan Allah kaje damu"

Kallonsu yayi cike da tausayawa yace "to Ku shirya mutafi" cikin minti 5 sun shirya

Mintuna da basu wuce 15 ba suka sadasu da Asibitin da aka kwantar da halima, suna zuwa kai tsaye d'akin da aka kai Halima suka nufa Dan Alhj shu'aibu ya gayamasu tana I.C.U


Wani matsanancin kuka Hafsa da Amina sukeyi lokacin dasuakyi arba da mahaifiyarsu kwance kan wani gado jikinta duk na'ura hatta da babban yatsanta na hannu an ma'kala na'ura, wani irin kuka suke mai ban tausayi, Alhj Sani kuwa duk illahirin jikinsa kyarma yake hankalinsa tashe ganin halinda matarsa take ciki.


Hajiya Zainab kau matar Alhj shu'aibu ha'kuri kawai takebasu, dan ko ita kanta ta tsorata da halinda Halima take ciki.


Wani yunkuri Halima tafara sai aman jinin take, dagudu Amina da Hafsa suka nufi gurinta suka rungumeta suna kuka, shima Alhj Sani kukan yake kamar 'karamin yaro,

Hajiya Zainab ce tayi 'karfin halin kiran likita ta shaidamashi abinda ke faruwa, da Sauri likita ya shigo d'akin umartarsu akayi dasu fita, amma Hafsa da Amina basuda niyyar fita kuka kawai suke suna kara rike mamansu da kyar aka fiddasu aka rufe,

Nanfa likita yafara aikinsa yi yake, amma ina abun ba sau'ki, wani salati Halima tayi da 'karfi Wanda duk wani Wanda ke kusa yaji salatin, sannan rai yayi Halinsa.





Fad'in tashin Hankalin da Hafsa da Amina suka Shiga bai misaltuwa Alhj Sani kau kamar wani zautacce haka Yakoma, Hajiya Zainab ma tayi kuka dan tayi rashin ma'kociya tagari.

Haka aka d'auki gawar Halima zuwa gida akayimata wanka aka kaita gidanta na gaskiya, dan ko 'yan uwanta basu samu halartar jana'izartaba sakamakon nisa dake akwai, sai washe Gari suka samu isowa.

'Kanwar Halimar sai yayarta Hajiya Asabe, sai yayyenta maza guda 3, haka akayi zaman makoki bayan kwana ukku mazan suka tafi bayan anyi addu'a sukabar matan dansu sunce sati zasuyi.





*             *             *          *




Bayan sati d'aya Zazzaune suke kowanensu yayi jugum, Alhj Sani kuwa shima zama yayi yana sauraron abinda Hajiya Asabe zata gayamashi dan ita tasa aka kirashi.


Cikin tsananin jimami da *Alhini* Hajiya Asabe tafara magana "to Alhj sani mudai gobe tunda asuba mukeso mud'au hanyar gida, saboda haka nake ro'konka dan Allah kabamu Hafsa da Amina mutafi dasu gurinmu muri'kesu badan muna tunanin zaka gaza dasuba, a'a"


Gyara zama Alhj Sani yayi sannan yace "Hajiya dan Allah kuyi ha'kuri bazan iya rabuwa da yarana ba, dan muddin narabu dasu abin zemin yawa dame zanji da rashin mahaifiyarsu koda rashinsu" yana kaiwa nan yafashe da kuka, kamar wani 'karamin yaro, ganin haka yayi bala'inba Hajiya Asabe tausayi, dole suka ha'kura suka barmashi yayanshi.

Washe gari tunda asuba suka d'au hanya,  Hafsa da Amina kuwa a ranar wani sabon kuka suka dasa.






🤒😎
👉🏻🌎 *KE DUNIYA...* 🌎👈🏻
_(Rumfar kara)_




*Written & story by*
*Zee Elkaseem (Mmn khady)* 😘




Page 10---15



*Just a Short Story* 👌🏻






Hafsa da Amina kuwa sunaji suna gani su Hajiya asabe suka tafi suka barsu, harga Allah sunso subi dangin mahaifiyarsu, amma ba yanda zasuyi tunda mahaifinsu bai aminceba.

Wani sabon kuka suka dasa kamar yaune mamarsu tabar DUNIYA,
Alhj sani daga d'akinsa yake jiyo sautin kukansu har cikin ransa yakejin kukan nasu, ba kamar Hafsa, waccs yake masifar so da 'kauna.

Zuwa yayi yajawosu ya rungumesu jikinsa, shima kukan yake kamar wani 'karamin yaro,

Ahankali ya zame Amina daga jikinsa ya 'kara 'kan'kame Hafsa yana maida wani irin numfashi,
Matseta yayi sosai a 'kirjinsa yana d'an bubbuga bayanta Alamar rarrashi, ita kuwa Hafsa tsorone ya mamaye zuciyarta jin wani Al'amari Wanda bata ta6a jiba,

'Ko'karin kwatar kanta tafarayi lokacin dataji wani abu na tokareta, amma Alhj Sani ya ri'keta gam duk illahirin jikinsa kyarma yakeyi.

Da kyar Hafsa ta kwace kanta tanufi d'aki da gudu tafad'a kan gado tare da faahewa da kuka mai cin rai,
Rarraahinta Amina tari'akayi dukda itama hawaye ne kwance a idanunta.

Alhj Sani kuwa d'akinsa yanufa jikinsa duk ba kuzari, zama yayi gefen gadonsa tare da rafka uban tagumi.


*Asalin su*

Alhj Sani da Halima sunyi auren saurayi da budurwa, inda Alhj Sani yahad'u da halima a 'kasarsu ta Niger babban birni yamai, lokacin daya raka abokinsa sayen wasu kaya.

Soyayya mai 'karfi tashiga tsakaninsu,

Lokacinda Halima ta gabatar da Alhj Sani amatsayin mijin datakeson aure gurin babban yayansu Wanda yakasnce shine uwa da uba agaresu itada yayarta hajiya Asabe da 'kanwarsu, bayan rasuwar iyayensu.
'Kin amincewa yayi dan yana ganin Nigeria yayi nisa.

Amma Halima tadage akan ba Wanda takeso sai Sani, haka aka ha'kura aka auramatashi

Alhj Sani cike da farinciki yataho da matarsa zuwa gida Nigeria a garin katsina karamar hukumar musawa.


A babban gidansa ya tare wanda ya kasance mallakinsa, 'katon gidane  Wanda idan kashigo wata haraba zaka iske mai d'auke da shuke² hadda shukar banana, daga nan zaka shiga 'karamin zauren dazai sadaka da tsakar gidan wanda ke d'auke da tsararrun d'akuna guda hudu, wanda ukku suke rukuni d'aya, yayinda d'aki daya yake gefe Wanda ya kasance shine d'akin mai gidan.

Gefe guda kuma kitchen ne kusadashi kuma madai-dacin store, sa daga can gefe sosai kewaye guda 2 dana wanka dana bahaya.

Alhj Sani da matarsa Halima suna zaune cikin mutunci da mutunta juna saboda Halima macece mai matu'kar ha'kuri shiyasa ko cikin Unguwa batada abokin hayaniya

Cikin Shekara takwas da aurensu Allah ya azurtasu da yara biyu mata Hafsa da Amina Hafsa Nada shekara hudu aka haifi Amina daga lokacin kuma basu kuma samun haihuwaba.

Haka suka rugumi 'yayansu suna matu'kar nuna masu soyayya.

Bayan shekara sha hud'u Hafsa nada shekara sha tara yayinda tayi shekara d'aya da kammala secondary dinta, Amina kuwa wannan shekarar tagama tanada shekara sha shidda.

Hafsa takanse kyakkyawa ajin farko dan duk wata sura ta mahaifiyarta ta d'auko,  tanada cikakkiyar Halittar da duk namijin daya ganta dole ya kwad'aitu da ita, Amina ma ba daga bayaba, sai dai ganin Hafsa baisa aga dirin jikinta duka fatarta tafi ta Aminar Haske.

Halima duk lokacin data kalli Hafsa gabanta yakan fad'i tari'ka tunowa da gwagwarmayar datasha da maza saboda sura da dirin jikin da Allah yabata, to gashi Hafsa tabiyota sak harma tanaso ta zarceta, dan Hafsa tanada Breast sosai.

Hakan yasa ta tunkari Alhj Sani da shawarar yakamata su aurar da Hafsa tunda harta shekara da gama makaranata kuma ga 'kanwartama ta gama wannan shekarar kuma Alhmdlh sun sauke Al'qur'ani.

Shuru yayi na wani lokaci sannan ya sauke ajiyar zuciya "kibari zanyi shawara.








Kucigaba da kasancewa dani yanzu lbrn yafara 🤝🏻
👉🏻🌎 *KE DUNIYA...* 🌎👈🏻
_(Rumfar kara)_




*Written & story by*
*Zee Elkaseem (Mmn khady)*😘





Page 15---20





*Just A Short Story* 👌🏻





Yau kimanin wata hud'u kenan da Halima tayima Alhj Sani magana kan a aurar da Hafsa Amma tunda yace sai yayi shawara har yanzu bai 'kara tada zancenba.

Itako halima kullum hankalinta tashe yake ganin yanda Hafsa ke 'kara bun'kasa hip's d'innan nata sai