Aure sirrii


AUREN SIRRI
    
Bismillahi rahamanar rahim

RADDI ZUWAGA MASU SUKAR MARUBUCIYAR WANNAN LITTAFI, IRINSU MAMAN AISHA KATSINA DA SAURAN DUK MASU MAGANA AKAN LITTAFIN.

Dafarko zan fara da ke maman Aisha katsina da kikecewa wa bahaka labarin ya kama ya kasanceba.

Shin kinsan lokacin da marubiyar ta tsara littafinta har ta fara rubutashi? ko kuma ta nemi shawaranki akan yadda ya kamata littafin ya kasance?
kince banda kishi ba abinda littafin yake koyarwa harda cewa ita Zeenat 'yar gold ce da baza'a mata kishiyaba to kin tsaya kinji karshen littafinne bare ki yanke hukunci.?

Kuma shi novels ai kowa yasan dama wasu abubuwan ba gaskiya bane anayine dan a nishadantar, sannan duk wani mai hankali ai in ya kalli film ko ya karanta littafi bawai komai da yake ciki zai daukaba,
dole akwai taurarin da Zasu taka kyakyawar rawa da kuma wadanda zasuyi akasin haka, saboda haka dan Zeenat tana kishi ba'ace ayi koyi da itaba tunda dama  muna da hankali da tunanin da zamu tantace fari da baki.

Maganar cewa wai baku karu da komaiba acikin littafin ba abin mamaki bane in kin fadi haka saboda mutane dama akwai wadanda basa tunani da kwakwalwarsu wajen tantance abubuwa, balle har su gane abinda zai amfanesu wala alla kina cikinsu.
Amma nidai na dauki darasi aciki daga ciki kuwa:

1-naga yadda Zeenat tayi ta zubar da ciki amma yanzu tana nema ido a rufe amma Allah bai kara bataba, saboda haka nadauki darasi cewa duk lokacin da Allah ya maka ni'ima ka godemasa, in kuwa ka butulce to bashakka zaka dandana.

2- nagane cewa itama Nablah sakamakon bijirewa umarnin mahaifinta shine Allah ya jarabceta da wannan rayuwa ta  Auren sirri da sarkakiya da rashin 'yanci saboda iyaye ba abin wasa bane.

Kadan daga cikin darasin da littafin ya ke koyarwa wanda sai mai hankaline zai gane dama  mai hankali shike gane furfurar farar tunkiya.

Masu cewa za'a bata tarbiyyar yara to kusani daga lokacin da kika baiwa 'yarki waya kin gama bata du wani lasisi na lalacewa tunda kin bata duniya a tafin hannunta, zata shiga duk inda takeso a cikin wayarta, saboda haka amaimakon kuzo kuna hayaniya akan AUREN SIRRI ga shawara tunda har auren sirri zai bata muku 'yaya mai zai hana ku hana yaranku rike waya ko ku hanasu karantawa, ko ku daina sayawa AYSHA A BAGUDO data ko kuma salary da kuke biyanta take rubuta littafin ku daina bata.

Jama'a wannan littafin fa ba'ace dole sai kun karantashiba, amma saikun gama karantawa kuyita kananan maganganu.

Masoya wannan littafin Allah yabar zumunci ya kara dankon kauna.

daga✍🏻MRS SHABAB
wacce na ari bakin marbuciyar naci mata albasa.🤣

Kukasance dawannan shafin Na hausashow.tk