GYARAN FUSKA>

Tags

<GYARAN FUSKA>

Asssalamu alaikum barka da warhaka

amare da dama suna fama da matsalar kurajen
fuska musamman farar mace Wanda sune sukafi
fuskantar wannan matsalar
Zanyi bayanin hanyoyi goma Wanda amarya
zatabi don magance matsalar kurajen fuska


(1) Da farko ana so awa biyu ko uku
kafin ki kwanta barci sai ki shafa man
goge baki a fuskarki, musamman
wuraren da kurajen pimples suke da
yawa. Ba kowane irin man goge baki
za ki shafa ba, ana so ki shafa farin
man goge baki ne. Idan kin ga dama
za ki iya wanke fuskarki idan man
goge bakin da kika shafa ya kai minti
30, idan kin ga dama kuma za ki iya
kwantawa da shi har zuwa wayewar
gari. Za ki rika maimata hakan har
zuwa wadansu kwanaki, idan kin yi
hakan za ki ga canji a fuskarki.


(2) Ki kasance mai yawan shan
ruwa.yawaita
shan ruwa ba wai zai sanya miki
laushin fata ba ne kawai, a’a, zai
taimaka miki wajen yaki da kurajen
pimples din da suke fuskarki. Haka
yana da kyau ki guji yawan cin
abincin gwangwani, kasancewar
suna dauke da wasu sinadarai da za
su rika sanya kurajen fuska. Ya
kamata ki yawaita cin ‘ya’yan
itatuwa da suka hada da su abarba
da lemu da ayaba da kankana da
sauransu.


(3) Ki rika amfani da abin shafawar
da ake kira ‘(Antiodident spray) irin su
(Jane Iradale) da (Neutrogenia Rapid Clear) da
(Acne Eliminating Spot Gel)
da sauransu, hakan zai taimaka miki
wajen daidaita man da ke fatarki,
wanda masana fata suka ce idan ya
yi yawa yakan haifar da kurajen
fuska.


(4) Ki kasance mai amfani da man
(Cornmeal) a fuskarki, yakan sanya
kurajen fuska su motse sannan a
hankali su bace, misali man shi ne,
(Intagilo Clear Sal Cleanser.) Sannan ki
rika amfani da man da ke hana
yaduwar kwayar cutar bakteriya, irin
wannan man yakan ratsa kofofin da
suke fatar fuskarki da ma jikinki gaba
daya, sannan yana yakar kwayoyin
cutar da suke fatarki, a lokaci guda
ya daidaita miki yawan man da yake
fitowa daga fatarki. Zai kuma cire
miki kwayoyin halittar da suka mutu
a cikin fatarki. Misalinsu; (Phytomer Gommage)
da Luffa-0.

(5) Yana da kyau ki ware wata rana
ko wadansu ranaku a cikin mako ba
tare da kin shafa kayan kwalliya a
fuskarki ba, hakan zai bai wa fatar
fuskarki samun ‘yancin shigar da
kuma fitar da iska ta kofofinta ba tare
da wani cikas ba. Haka idan za ki
shafa kayan kwalliyar a fuskarki, to ki
yi amfani da kayan kwalliyar da ba
sa toshe kofofin fatar fuska.

(6) Ki kasance mai shafa mai domin
fatar fuskarki ta kasance cikin danshi,
kasancewar wadansu kurajen fuskar
sun fi bata fuska idan fuska tana
bushe.

(7) Yi amfani da man (Tea Tree’)
domin ba wai kawai yana baje
kurajen fuska ba ne, a’a yana rage
karfinsu da kuma kalarsu. Za ki sami
ire-iren wadannan man a shagunan
sayar da kayan kwalliya na zamani.


(8) Ki kasance mai yin taka tsan-
tsan wajen amfani da ire-iren man
shafawar da kike amfani da su a
gashin kanki, ma’ana kada ki sake ya
rika taba fuskarki hakan zai iya haifar
miki da kurajen fuska, kasancewar
wadansu sinadaran an yi su don su
taimaka wa gashin kai ne, don haka
idan suka shiga kofofin fatar fuskarki,
sai su haifar miki da matsala.

(9) Ki kasance mai gasa kurajen
fuskarki: Duk lokacin da kurajen
pimples suka fito miki sai ki samu
wani kyalle mai tsafta, sai ki tsoma
shi a ruwan zafi, ba wanda ya tafasa
ba, bayan kin tsoma sai ki fito da shi,
sai ki rika dora shi a kan wajen da
kurajen suke, sannan ki rika gogawa
a hankali, zafin kyallen yakan sa
kurajen su motse daga nan su mutu.


(10) Ki guje yin amfani da hannunki
wajen fasa kurajen da suke fuskarki,
domin hakan yana kara yawansu
hade da sanya fuskarki ta kara
cabewa

AMFANIN LALLE GA MATA

Tags

Asslamu alaikum un ya kk ya gida

AMFANIN LALLE GA MATA
.
.
Lalle dai da farko wani sinadari ne mai dauke da
alfanu iri iri, kuma addini ya kwadaitar da mata
su yi lalle akwai sirrika acikin sa.
.
.
Nafarko dai lalle Kariya ce daga sihiri, Kariya ce
daga aljanu sannan kuma Kariya ce daga
cututtuka da dama, yin lalle a kafa na zuqe cutar
dake kafan sannan yana kula da dumin mace, bi
ma ana yana kiyaye. ni imar mace ba tare da ya
gushe ba, innace lalle wasu zasu dauka zanen
henna nake nufi ko, to lalle dai na gargajiya
wanda muka rabu da yinsa yanzu shi nake
magana akai:
.
.
.
Ga kuma sadaqa ga duk mai infection ta tafasa
lalle inyadan huce sai ki dinga zama a ciki na
sati biyu, in Allah yayarda za ki warke.
.
: Saboda maganin da lalle keyi ma akan iya shan
ruwan lalle cokali daya don wankin dattin ciki
amma banda masu ciki, to yanzu dai zamu dauki
bangare daya daga cikin amfanin lalle muyi
magana akai, wato shine amfanin lalle da kuma
yanda ake amfani da shi don gyaran Fata.
.
.
Lalle dai ba karamin tasiri yake dashi wajen
gyara fata ba, domin shi natural toner ne ba
bleaching yake ba amma yanasa haske mai kyau
kuma yana goge dattin fata, in kina son gyara
fuska tai kyalli, laushi da haske to ki kwaba lalle
da ruwan Kwai amma banda kwaiduwar kwan ki
kwaba ruwa ruwa amma ba sosai ba ki lizimci
shafa shi kullum minti talatin kafin wanka, za ki
sha mamaki in sha Allah:
.
.
Ga masu son hasken fata, ki kwaba lalle da ruwa,
ki shafe a jikinki inya bushe ki dirje da man
zaitun zakiga canji.
.
.
sannan gamai son kamshin fata
: Ki kwaba lalle da turaren ki mai kyau na ruwa
wanda ake durawa ki zuba isasshen ruwa a
bucket ki sa garin lalle ya jika yay já zir sai ki
tsiyaye ruwan ki diga turaren ki mai kamshi ciki
Bayan kinyi wankan sabulun ki sai ki dauraye
jikinki dashi inkin lizimci haka to bake ba rabo da
kamshin jiki in sha Allahu.
.
.
: Sannan ga gyaran duka jiki kuma zaki hada lalle
da sabulun salo da Zuma kina wanka dasu duk
zakiga canjin fata in sha Allah
Sannan ga Amare kuma
Kafin kiyi dilke na aurenki
: fata zatayi laushi, haske da kuma santsi.
Ki samu lalle mai kyau ki kwaba da turaren ki
mai maiko, turaren gargajiya mai mai dinnan to ki
jika kamar botiki ba ruwa ruwa sosai ba Kamar
dai kunu, kullum sai ki shafe jikinki da hadin
lallen nan duka jikin ki, sãi kizo ki saka turaren
wuta a kasko ko burner ki rufu akai ki turara
jikinki hayakin turaren nan ya shiga sosai sai ki
fita kije kiyi wankan ki zakiga canji.
.
.
Daga karshe kuma ga masu fama da pimples, sai
ki hada lemon tsami da lalle kwabi mai dan tauri
amma ba sosai ba kina shafa wa a fuskaar ki,
kuraje zasu mutu sannan tabo bazai zauna ba ga
hasken fuska da laushi.
.
.
Kuma lalle dai ba bleaching yake ba.
.
.
Daga shafin Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyyah.
.
whatsApp 08162600700

Ciwan sanyi

Tags

Assalamu alaikum

Barkanmu da warhaka

zaki hada citta da kanunfari da kirfat da
tafarnuwa kiyi garinsu saiki zuba acikin zuma
sannan ki matsa lemon tsami kullum kinasha
cokali biyu sau biyu cikin sa'o,i ashirin da hudu
(24hours)
Bayan haka saiki hada garin hulba da garin
bagaruwa waje daya kina dafawa kina tace
ruwan kina tsarki dashi lokacinda kikazo
kwanciya kuma ki bare tafarnuwa kiyi matsi da
sala daya
wannan shima yana daya daga cikin fa,idodi dana
bincikowa gameda hanya mafi sauki da mace
zatabi don kawarda ciwon sanyi musamman
wanda yake saka mace zubar ruwa da kaikayi
tareda daukewar sha'awa ki jarraba wannan
kuma ki kasance da wannan gidan.

Kukasance damu

ILLOLIN ZAMA DA MACE DAYA (1)

Tags

Assalamu alaikum


ILLOLIN ZAMA DA MACE DAYA (1)

HADARIN ZAMA DA MACE DAYA!!!

Mal Aminu Daurawa kano.
Zama da mace daya yana kawo illoli da dama ga
magidanci da su mata kansu da kuma
al`umma.

++++++++++++++++++
ILLOLI GA MAGIDANCI.
1:-Yana rage masa nishadin aure.
2:-Yana kawo tsufa da wuri.
3:-Yana saka maigida cikin damuwa
4:-Yana saka wa mace ta rika daga masa kai,
tayi masa yadda taso saboda ta san ba shi da
yadda zai yi.
5:-Yana rage masa samun soyayya da tarairaya
da kulawa da ya cancanta a matsayinsa na
maigida.
6:-Yakan hana shi tantance so na gaskiya daga
bangaren matarsa ko wanin haka.
****
ILLOLI GA SU MATAN.
1:-Yana hana wadansu samun mazajen aure.
2:-Yana dorawa matar gida aiyukan da suka
shige misali kamar, kulawa da maigida, yaran
gida da ita ma kanta.
3:-Yakan hana mace samun isasshen hutu da
kuma lokacin kulawa da kanta.
4:-Yana rage wa mace kuzarin nuna soyayya ga
maigidanta.
5:-Yana saka matar gida cikin tsoro da fargaba
maras yankewa na ko za ai mata kishiya.
6:-Yana haifar da rashin amincewarta ga
maigidanta da dauwamar da tuhuma ta har
abada.
7:-Yana saka mace cikin shirin yaki da
dawainiyar dakon makamai marasa ranar
yankewa na nuna kin ayi mata kishiya.
8:-Yana saka mata yawan zargi ga dukkan matan
da suke da alaka da maigidanta ko ma wace iri
ce koda ma yar uwa ce ko abokiyar
kasuwancinsa.
9:-Yana kara mata zafin kishi da rashin nutsuwa
marasa ranar yankewa.
****
ILLOLIN GA AL`UMMA
1:-Yana haifar da karuwai mata marasa aure.
2:-Yana bunkasa yawan zawarawa acikin
al`umma.
3:-Yana dorawa al`umma karin nauyin kulawa da
mata iyayen marayu da marayun kansu.
4:-Yana bunkasa zinace-zinace a cikin
al`umma.
5:-Yana rage tausayi da son bada taimako da
agaji daga zukatan al`umma.
6:-Yana kara saka fargaba da tsoro a zukatan
iyaye wadanda suke da `ya`ya mata a gaba.
7:-Yana bunkasa kasuwar malaman tsibbu da
bokaye.

Kuci gaba da kasancewa damu akoda yaushe

LET'S TALK ABOUT MAKEUP EPISODE : 10

Tags

Assalamu alaikum yan uwa
iRashyder

LET'S TALK ABOUT MAKEUP
EPISODE : 10
Assalamu alaikum wa rahmatullah. Last week
mun fara magana akan concealer yanda zaki
saya da kuma wanda zai dace dake So, insha
Allah Yau zan gabatar maku da hanyoyi daban
daban wanda zaki iya amfani da concealer dinki
amma kafin nan akwai buqatar in qara tunasar da
mu wannan
YELLOW CONCEALER :- tana fitar maki da even
tone ma'ana zata sa kalar fatar ki ta fito sosai
PINK AND PEACH CONCEALER
Wannan kalar sun fi kyau a shafa su a under eye
wato ina nufin concealer da ake shafawa a qasan
ido
GREEN CONCEALER
wannan kalolin concealer din suna boye
blemishes wasu en chaki chaki pimples, tabo da
duk wasu dabbare dabbaren da suke a fuskar
mutum
ORANGE CONCEALER
Wannan especially mata masu amfani da niqaf
zaki ga zagayen idon su tayi baqi sabda rana tou
idan idonki yana da wannan duhun akwai buqatar
ki yi amfani da orange concealer a idon ki
PURPLE CONCEALER
swannan yana boye chaki chakin fuska
Wannan sune kaloli na concealer da ya kamata ki
mallaka alhmdl ynxn zaki iya samun su cikin arha
da sauki domin anyi su kamar eye shadow idan
kin je siya kawai kice a baki CONCEALER
PLATELET .
YANDA AKE AMFANI DA CONCEALER
Concealer tana da amfani a. Wurare iri daban
daban misali
1 MACE MARAR TABO
Ba dole sai kina da tabo a jiki zakiyi using
concealer ba a'a zaki iya amfani dashi wurin fitar
da asali shape din fuskar da Allah yayi maki
yanda zakiyi shine ki samu concealer kala biyu
mai haske da mai duhu (kamar yanda nayi
Bayani a post dina na last week idan baki gani
ba ki duba a Facebook page mai suna ADO DA
KWALLIYA ) ki shafa mai hasken a T zone dinki
da kumatun Ki mai duhun kuma ki shafa a
sauran sassan fuskar ki zuwa wuya sannan kiyi
Blending ki shafa powder.
2 MACE MAI TABO KO PIMPLES
ke kika fi chanchanta wurin amfani da concealer
sai ki sayi concealer na boye tabo ki shafa a kan
tabon kadai a duk fuskar ki ba fa! ki bari ya dan
sha iska kamar 5mins sannan sai ki dauko asalin
concealer din ki kalar skin naki ki shafa akan
green concealer din sannan ki shafa powder.
Idan baki da concealer zaki iya amfani da
foundation amma idan ki shafa sai kin jira
30mins ya yi kauri sannan ki shafa powder akai
PIMPLES A BAYA KO QIRJI
idan kina da pimples ko tabbai da yawa ko kadan
a jikin ki kuma kina sou ki sa kayan da dole sai
sun fito.....
Ki dauki normal concealer dinki kalar jikin ki sak!
Ki shafa a wurin amma fa tabon da pimples din
kadai zaki riqa rufe wa ba wai duk wajen zaki
yiwa fenti ba. Idan kin gama sai ki yi amfani da
brush ko soson pauda ki shafa pouda mai gari a
wajen sama sama ake shafawa ba da qarfi ba .
MARAR SON KWALLIYA / STUDENTS
Man shafawar ki ta fuska zaki dangwali kadan ki
shafa a bayan hannun ki hada da concealer da
foundation ki kwaba ki shafa a fuskar ki at once
ki shafa powder amma fa kadan kadan kar ki
cika idan kikayi haka kin hada TINTED
MOISTURIZER kenan amma baza ki iya hadawa
da yawa ki ajiye ba.
CONCEALER A QASAN IDO
- Hanya Mafi dacewa idan zaki shafa concealer a
kasan idon ki shine kiyi shape din triangle dashi
kamar yanda zaku gani a hoton .
- Sannan kar ki manta idan idonki yana da duhu
tou ki riqa amfani da orange, pink ko kuma
peach colour concealer a qasan idon sannan sai
ki rufe shi sama sama da asalin concealer dinki.
- akwai wasu layi layi a qasan idon ki idan kin
gama shafa concealer kinga sun fito sai ki nema
tissue ki rage wa tissue din kauri wajen cire palle
daya a jiki ki sa a qasan idonki zai tsantsame
maiko din.
CONCEALER A GIRA
-zakiyi amfani da concealer brush wurin fitar da
shape din girar ki ta sama da ta qasa sannan kiyi
amfani da yatsar ki ta zobe ki rage wa concealer
din karfi sosai kar ki bari ta fito dau
CONCEALER A IDO
- idan baki da eyeshadow primer zaki iya amfani
da concealer wato zaki dangwali concealer dan
kadan sai ki shafa a saman idonki amma fa kar
bari ya shiga ramin kashin idonki tou bayan kin
shafa sai ko shafa farin eyeshadow akai sannan
ki shafa duk kalar da kike sou hakan zai sa
eyeshadow din yayi kauri kuma ya tsaya a wuri
daya ba tare da wani layi layi ba.
-idan kina shafa eyeliner a ido kika yi mistake kar
ki damu idan kin gama ki sa abun share kunne ki
goge inda aka samu matsalar na San bazai fita
duka ba sai ki shafa concealer a wurin.
-ki fitar da shape din idonki ta hanyar shafa
concealer a saman kwayan idonki sannan ki
tsallake ramin qashin idanki ki shafa a qashin
girar da saqon idonki da ta qasan amma fa ba
yanda za'a gane ba yin hakan na da kyau
musamman lokacin da kika tashi daga barci
idonki luhu luhu.
CONCEALER A BAKI
-idan zaki shafa jambaki mai kala biyu bakya sou
su gauraya su zama daya zua anjima toh ki
shafa concealer a zagayen bakin naki inda zaki
amma banda tsakiya sai ki dan yi blending dinsa.
-idan kuma kina sou bakin ki yayi kauri kamar
mai shirin yin kiss tou zaki yi amfani da
concealer wurin fitar da shape din kiss a tsakiyar
bakin ki sai kiyi Blending sannan ki shafa jambaki
a hankali
-amma idan kina sou ki fitar da shape din bakin
ki ne tou wannan zaki shafa concealer a gaba
daya labban ki sannan ki shafa jambaki idan kin
gama sai kiyi amfani da concealer brush wurin
qara fitar da shape din bakin naki ta inda jambaki
ya bata.
CONCEALER A QASHIN WUYA
yanda zaki fitar da sexy night time look da
qashin wuyan ki shine ki samu concealer kala
biyu mai haske da mai duhu sai ki daga kafadun
ki sama ki shafa mai duhun a aljuhun da sukayi
mai hasken kuma a qashin saman sai kiyi
Blending dinsu yanda ba za'a gani ba.
Wannan sune da yawa daga cikin abubuwan da
nasan anayi da concealer don haka nike ganin
Gaskia ya kamata ki mallaki concealer kala kala
iri iri daban daban amma dai ki tabbatar kin fara
shafa foundation kafin concealer ba wai shafa
concealer a kasan foundation bashi da kyau bane
a'a sai dai yana buqatar kwarewa. dan Allah duk
wacce ta ji dadin abun da na rubta ta taya ni
addu'a bukatun mu na alkhairi Allah ya biya
mana Amin
Wslm
AdoDaKwalliya

LET'S TALK ABOUT MAKEUP EPISODE : 9

Tags

LET'S TALK ABOUT MAKEUP
EPISODE : 9
Assalamu alaikum, previously munyi Bayani akan
makeup foundations da yanda ya kamata ayi
amfani da su. Yau insha Allah zamu tattauna
akan concealer.
CONCEALER
Amfani da abu mai kyau wanda ya dace da fatar
ki shine Babban abin lura a gurin kwalliya
Concealer mai kyau itace wadda take qara wa
fuska kumari ta batar da tabboi dabbare dabbare
acne da sauransu. Sannan itace wacce zata
daidaita akan foundation dinki tare da taimakawa
wajen fitar maki da even skin tone naki
AMFANIN CONCEALER
Kafin mu kai ga siya da shafa concealer yana da
kyau mu San amfaninsa da kuma muhimmancin
sa
Da farko dai ita concealer ana amfani da ita ne a
qananan wuraren da hasken su ya dashe a fuska
( kamar qasan ido, saqon hanci, tabo da acne)
sannan ba'a yi sa Don ashafa dole da foundation
ba amma yafi kyau idan aka shafa saman
foundation din.Zaki iya shafa concealer kafin ko
bayan shafa foundation amma ya danganta da
yanda kike Son boye tabban fuskar ki. Masana
kwalliya sunce idan kina da tabo sosai a fuska
yafi dacewa ki shafa concealer kafin ki dora
foundation wasu kuma suna ganin foundation yafi
dacewa a qasan concealer tou ko ma dai yaya
ne sai ki gwada duk biyun ki zabi wanda yafi
dacewa dake. Sai dai baza ki shafa concealer a
saman foundation mai kamar powder ba (ina
nufin powder or cream to powder foundation idan
baki ga post dina na foundation ba zaki iya
dubawa a Facebook page dina mai suna Ado Da
Kwalliya)
ZABAN CONCEALER
A lokacin da zaki sati concealer yana da kyau ki
dage wurin zaben wanda ya dace da fatar ki
(skin type) don haka idan dry skin Gare ki tou
kada ki sayi concealer na LIQUID KO MATTE
FINISHED domin zai sa fuskar ki ta dada
bushewa kenan yafi dacewa da oily skin domin
zai taimaka wajen rage maiqon fuskar
Amma mai Oily skin Da kuma wanda ramukan
jikin sa suke da girma (ina nufin kafan gashin
jikin ki) tou bazai amfani da CREAMY KO STICK
CONCEALER ba. Sabda zai shiga cikin ramin
gashin ya qarawa ramukan girma sannan irin
wannan concealer din suna qarawa fuskar mutum
maiko kenan yafi dacewa da dry and normal skin
amma ba masu open pores ba (kafan gashi a
bude)
Idan kuma kina da yawan tabbai a fuskar ki yana
da kyau ki sayi concealer da aka sanya masa
Medium coverage
Sannan yana da kyau ki siya concealer guda biyu
wato wanda zaki riqa shafawa a qasan idon ki da
kuma wanda zaki riqa shafawa sauran wuraren
yanda kuwa zaki banbance su shine misali
FOUNDATION. # COLOR3
CONCEALER. #COLOR3/2
UNDER EYE CONCEALER # COLOR1/2
Ana so kalar foundation dinki da concealer su
zama daya wato akwai kala mai sanyi mai dumi
da kuma mai haske (warm, cool and bright
colours) idan foundation dinki mai kalar sanyi ne
tou concealer din ma ya kasance haka.
TYPES OF CONCEALER
LIQUID CONCEALER
yafi dacewa da normal, combination, oily,
sensitive skin Da kuma fuska mai chaki chaki
sannan idan zaki sayi under eye concealer tou
yana da kyau ki sayi liquid zakiyi setting dinsa da
ko wane kalar pouda
CREAM CONCEALER
Yafi dacewa da dry skin normal skin combination
da kuma sensitive skin sannan idan kinyi amfani
da shi tou akwai buqatar ki shafa loose powder
(powder mai gari )
STICK CONCEALER
Normal, dry, da kuma sensitive skin sannan
bayan kin gama akwai bukatar kiyi setting dinsa
da powder mai gari
CREAM TO POWDER CONCEALER
Yafi dacewa da normal combination da kuma
sensitive skin wannan ba ya buqatar ki shafa
masa powder idan kin gama sannan idan kina da
acne tou zai qara maki yawan su don haka masu
pimples da dry skin ku guje sa
COLOUR CORRECTING CONCEALER :
Shi wannan ba sai nayi wani dogon Bayani ba
domin dai suna zua ne kala daban daban Kamar
da purple , pink da sauran su functions dinsu
daya da na primer masu colour dan haka idan
xaki siya concealer mai colour sai ki duba post
dina na primer dan ganin amfanin ko wane kala
Wannan sune nau'o'in concealer kuma ko wanne
daga cikin su yana da kyau Sosai abu mai
mahimmanci dai kawai ki zabi wanda yafi
dacewa da skin type dinki next episode zamu
koyi yanda ake amfani dashi insha Allah wslm.....
AdoDaKwalliya

LET'S TALK ABOUT MAKEUP EPISODE : 8

Tags

LET'S TALK ABOUT MAKEUP
EPISODE : 8
Assalamu Alaikum previously muyi Bayani akan
Primer yau Zamuyi Bayani akan foundation insha
Allah
FOUNDATION
Foundation wani sinadari ne daga cikin sinadaran
kwalliya wanda yake da matsayin tushen kwalliya
(Makeup base) yana taimaka wa wajen daidaita
kalar fatan fuska ta zama daya tare da batar da
duk wani dabbare dabbare sannan shi din baya
batar da kuraje da manyan tabbai don haka mu
daina kwaba foundation a fuska please rashin iya
ado ne. Sannan tana sa fuskar ki tayi fresh (idan
baki maka da yawa ba kenan) kuma tayi sumul.
Akasarin fuska ana rufe ta ne da foundation idan
za'a yi makeup za'a shafa foundation da
foundation brush daga fuska zuwa wuya domin
kada kamanninsu su banbanta da juna.
Foundation ya kasu kala kala kamar haka
1) LIQUID FOUNDATION
Wannan zaki gansu akasari a cikin tube ko kuma
cikin kwalba mai bakin pampo basu da kauri
sosai kuma sun fi sauqin amfani suna bin fata
sosai sannan zasu sa face naki tayi sumul tayi
kyau. Shima din ya kasu kashi biyu akwai
a) OIL BASED FORMULA LIQUID FOUNDATION
Yana da kauri sannan baya mutstsikua da
sauri.Wannan shi yafi dacewa da DRY SKIN kuma
fata mai tattarewa wato WRINKLED SKIN
(alamun tsufa) sabda sinadaran dake Ciki.
b) WATER BASE FORMULA LIQUID FOUNDATION
Wannan bashi da kauri kamar oil base sannan
yana da sauqin amfani. Yafi dacewa da OILY
SKIN da NORMAL / COMBINATION SKIN domin
yana dauke da sinadarin man silicon wanda zai
taimaka wajen daidaita maiqon fuskar ki.
2) CREAM FOUNDATION
Zaki ganshi kamar cream an sa a abun jambaki
(container) amma bai da tauri sosai ko a abin
powder ko kuma tube. Shima saboda kauri sa
yana boye blemishes din fuska.
Yafi dacewa da EXRA DRY SKIN saboda
moisturising properties dinsa
3) CAKE OR STICK FOUNDATION
Zaki gana a containa kamar ta jambaki ana fito
dashi ana maidawa sannan yana da tauri sosai
fiye da wancan kuma yana saurin bushe wa idan
aka shafa a fuska sannan ya bada MATT finish
zaki iya amfani da shi a matsayin concealer (in
baki da ita) yana batar da kananan tabo amma
an fiso kiyi amfani da ita lokacin buki, dauka
hoto, ko wani sha'ani sabda qarfin ta.
Wannan foundation din tafi dacewa da OILY SKIN
sabda saurin bushewar ta Sam! Bata da maiko.
4) POWDER FOUNDATION
Zaki gansa kamar powder mai gari (loose
powder). Akwai mai kama da pressed powder
(wato powder irin mai mudubi da Soso aciki
amma ba mai gari ba) bashi da maiqo kamar
powder yake
a)LOOSE POWDER FOUNDATION
Yana dacewa da mace wacce bata cika son
kwalliya ba domin zai taimaka wajen bata
NATURAL LOOK . Sannan ana amfani da shi
wurin gyara qalliya yafi dacewa da OILY SKIN
b) PRESSED POWDER FOUNDATION
kamar yanda nayi Bayani a sama shi ba mai gari
bane kamar. Ko wane irin skin type zasu yi
amfani dashi amma yafi dacewa da oily skin
5) WATER PROOF FOUNDATION
Yana zuwa a yanayin liquid ko na cream anma
zaki ga an rubta masa waterproof ajiki. Mutane
sun fi son wannan especially lokacin zafi ko na
damuna domin shi rua ko zufa basa bata sa.
Ko wani SKIN TYPES zasu yi amfani da shi sai
da ki duba wanda aka rubta misali for dry skin ko
oily ko combination da sauran su
6) MINERAL FOUNDATION
Wannan anyi su ne da sinadaran da ake tonowa
daga qarqashin qasa kuma yafi dacewa da
SENSITIVE SKIN saboda magunguna da ya quna
8) SPRAY FOUNDATION
Zaki gansa kamar turare fesawa zaki riqa yi a
maimakon shafawa yana da matuqar kyau amma
idan kin iya fesawan idan baki iya ba ki fesa a
makeup brush dinki ki shafa ana amfani da shi
ne idan an San kwalliyar zata dade misali idan
zaki je office ko sch kuna baki sou kiyi kwalliya a
chan. All skin types akwai sai ki nemi daidai da
skin dinki
9) CREAM -TO-POWDER / LIQUID -TO-POWDER
Zaki ganshi kamar powder (compact powder) ba
mai gari ba ana shafa shi kai tsaye kamar
powder yana da maiko kadan sannan yana da
saurin bushewa yafi dacewa da COMBINATION /
NORMAL SKIN
10) TINTED MOISTURIZER
wannan Moisturiser ne da foundation a waje daya
duk da cewa wasu basu dauke sa matsayin
foundation ba shima yana gyara fuska sosai
kuma yafi dacewa da DRY SKIN.
MOUSSE /WHIPPED FOUNDATION
Zaki ganshi liquid ko cream a cikin gwangwani ko
spray sannan shi dan kadan ake shafawa
Kowane skin type zasu yi amfani da shi sai dai
yafi dacewa da DRY SKIN Da kuma TSOHUWAR
FATA kamar shakara 30
Yanda zaki gane kalar foundation dinki shine ki
shafa daga saman gemun ki zua wuyan ki idan
kika ga foundation din ta bace to kalar ki ce
amma idan kika ganta baro baro to NO! Lastly
yana da kyau mu riqa sayan kayan makeup masu
dauke da sinadarin SPF sabda kariya daga rana
bye sai mun hadu A NEXT EPISODE insha Allah
AdoDaKwalliya

LET'S TALK ABOUT MAKEUP EPISODE : 7

Tags

Assalamu alaikum

LET'S TALK ABOUT MAKEUP
EPISODE : 7
Assalamu alaikum, previously munyi Bayani akan
makeup brushes da uses dinsu sannan mun fadi
cewa a kiyaye tsabtar sa domin kare fuska daga
yawan kuraje pimples da sauran su tou yau insha
Allahu zamu cigaba.
4 ) PRIMER
Shi primer kamar foundation yake sai dai shi
bashi da kauri idan kin shafa kamar man shafawa
haka yake amfaninsa shine;
Yana riqe foundation sannan yasa kwalliyar ta
dade ba tare da ta lalace ba. Yana batar da
alamomin tsufa a fuska (wrinkles ) yana batar da
fine lines wato layin da suke fitowa a fuskar ki
bayan kin gama kwalliya musamman layin da
yake fitowa daga saqon hancin ki zua bakin Ki
idan kinyi murmushi (yana bata ado)
Sannan wasu daga ciki suna rage maikon fuska
(idan kin siya na oily skin kenan)
Sai dai yanxn salon ya chanza domin anyi prima
ne ta kaloli daban daban kuma kowane aikin sa
daban don haka ku taho kar a barmu a baya.
CLEAR PRIMER
duk abinda na lissafa a sama yana yi sai dai shi
baya boye tabo da sauran su amma zai daidaita
maki zaman foundation dinki
GREEN PRIMER
Yana batar da jajayen tabo na kuraje da pimples
in har kina da jajayen tabo ko kuraje tou wannan
zai dace dake
So idan kina da jajayen kuraje a fuskar ki gwada
wannan:
Physician’s Formula Mineral Wear Correcting
Primer in Green ko kuma Clinique Superprime
Color Corrects Redness
BRONZE / GOLD
Ya da kyau ga bakar fata da kuma fata wacce
take da duhu ba mai haske sosai ba
YELLOW PRIMER
Wannan yana da lightening effect don haka zaki
yi amfani da shi idan fatar ki tana da alamar
quna ko dabbare dabbare sannan yana boye tabo
shima wannan yafi dacewa da baqar mace da
kuma tsaka tsaki.
PURPLE PRIMER
Wannan yafi dacewa da farar fata shima yana
boye chaki chakin fuska.
PINK PRIMER
Wannan yana karawa fuska kala mai kyau sannan
yana dacewa da ko wane kalar fata zaki iya
jaraba wannan Revlon PhotoReady Colour
Correcting Primer
ORANGE PRIMER
Wannan amfanin su daya da pink amma shi yana
boye tabo ki gwada
Revlon Photo Ready Color Correcting Primer ko
kuma Clinique Super Prime Colour Corrects
Discolorations
MULTI PRIMER
Wannan ga mai son amfani nau'i daban daban na
primer sai ya siya wannan domin yana dauke da
nau'in kaloli a cikin sa sai ki lura da irin colors
din da ke ciki kafin ki saya
YANDA AKE AMFANI DA PRIMER
bayan kinyi cleansing fuskar ki kinyi toning da
moisturising sai ki jira kamar minti 5 sannan ki
shafa primer dinki shi ba'a shafa shi da makeup
brush yafi kyau ki shafa shi da hannu domin
tamkar mai yake
Amma idan na kuraje zaki shafa tou zaki shafa
ne kawai a kan kurajen.
Zamuyi Bayani akan hakan a gaba.
Masu pimples da chaki chakin fuska ku gwada
wannan.
BareMinerals bareVitamins Skin Rev-er Upper ko
kuma Smashbox Photo Finish Blemish Control
Primer
OILY SKIN
Boots No7 Beautifully Matte Makeup Base ko
kuma BareMinerals Primetime Foundation Primer
DRY SKIN
Palladio Primer ko kuma Laura Mercier Hydrating
Foundation Primer
SENSITIVE SKIN
Ulta Professional Hydro Primer ko kuma Lorac
I’m So Soothing Face Primer
Da wannan muka zo karshen wannan episode din
zamu cigaba daga Inda muka tsaya a NEXT
EPISODE insha Allah duk mai tambaya tayi a
comment box ko kuma ta private
AdoDaKwalliya

LET'S TALK ABOUT MAKEUP EPISODE : 6

Tags

iRashyder
LET'S TALK ABOUT MAKEUP
EPISODE : 6
Assalamalaikum, last episode munyi Bayani akan
abubua da mutum ya kamata Ya mallaka game
da kayan Kwalliya sannan mun fara Bayani akan
wasu daga ciki wato CLEANSER, TONER and
MOISTURIZER tou gaskia yana da kyau ki kiyaye
yin hakan kullum da safe da kuma dare zai gyara
maki fuska sosai ki kiyayi kwanciya da makeup a
fuska.
3) MAKEUP BRUSHES :
Da yawa sun dade yana amfani da makeup
brushes ba tare da ganin amfanin su ba har ma
kina tunanin cewa hannun ki ya fi. Tou ba haka
bane matsalar shine ba masu kyau kike saya ba.
YANDA ZAKI GANE MAI KYAU SHINE idan kika je
siya tou ki dora a hannun ki idan ya durmushe
wato yana da laushi sosai tou ba mai kyau bane
amma idan kin daura kinga ya tsaya chak! Kuma
yana da laushi bai chake ki kamar tsintsiya ba
Tou shine mai kyau din.
Yanxn zan kawo kadan daga cikin makeup
brushes da yanda zakiyi amfani da su
FOUNDATION BRUSH
Wannan brush din zakiyi amfani dashi ne wurin
shafa foundation da smoothing dinsa
KABUKI BRUSH
Zakiyi amfani da shi wurin shafa bronzer / blush
wato dan sama kadan da qashin kumatun Ki
POWDER BRUSH
Zakiyi amfani da shi wurin shafa powder mai gari
bayan kin dangwali powder din sai ki dan
kakkabe kadan sannan ki shafa daga goshin ki
zua hanci da gemun ki
ANGLE BRUSH
Zakiyi amfani da shi wurin fitar da shape din
fuska wato daga saqon hancin ki zua kunne
wurin sajen ki
CONCEALER BRUSH or COMOFLAGE
Zakiyi amfani da shi wurin shafa concealer a
qasan idon ki da saqon da ke tsakanin idonki da
hanci sannan zaki iya amfani da shi wurin gyara
shape din bakin ki da concealer bayan kin shafa
jan baki.
ALL OVER EYE SHADOW BRUSH
Zaki yi amfani dashi wurin yin smoky eyes wato
dashi zakiyi amfani wurin shafa eyeshadow a
idonki ta qasa.
BLENDING BRUSH
Zaki yi amfani da shi wurin fitar da shape din
qashin idon ki ta sama (wato tsakanin idonki da
girar ki) crease .
SPONGE APPLICATOR
zaki yi amfani da shi wurin shafa eyeshadow
SMUDGER BRUSH
zaki amfani dashi wurin rage ma kwalliyan idon ki
karfi especially eyeliner
ANGLE EYELINER BRUSH
Idan eyeliner dinki bana ruwa bane wato mai
maiqo kenan tou dashi zakiyi amfani wurin lining
idonki
LASH BROW /COMB
Zaki yi amfani da shi wurin tace gashin gran ki
da gyara shi
FAN BRUSH
Wannan zaki yi amfani da shi wurin share datti a
fuskan ki a lokacin da kike kwalliya misali idan
kin sa eyeshadow burbudin sa ya zuba maki sai
kisa fan brush din ki sharce amma sama sama
kar ki danna
BEAUTY BLENDER
zakiyi amfani da wannan wurin daidaita yawan
foundation da concealer din da ke Fuskar ki
yanda zakiyi shine bayan kin gama kwalliya kafin
ki shafa powder sai ki sa beauty blender din kina
dan daddana wa a fuskan ki har sai kin ga fuskar
ki tayi sumul zaki iya sa shi a ruwa ki matse da
kyau sannan ki fara daddana wa din hakan zai sa
face dinki tayi sumul kuma makeup din zai fi
dadewa.
Lastly ki riqa yawan wanke makeup brushes dinki
saboda bacteria yin hakan zai kare fuskar ki
daga yawan kuraje da pimples. Sai mun hadu a
NEXT EPISODE insha Allah
WomenOfJannah

LET'S TALK ABOUT MAKEUP EPISODE : 5

Tags

iRashyder
LET'S TALK ABOUT MAKEUP
EPISODE : 5
Assalamalaikum, previously munyi Bayani akan
abun da mutum zai fara yi kafin Ya fara makeup
shine sanin skin type dinki da yanda Zaki kula
dashi. so, yanxn ina ga lokaci yayi da zamu shiga
kasua domin siyan kayan Kwalliya
Kina Bukatar Abubua Kamar Haka:
1 ) Cleanser + Toner
2 ) Moisturiser
3 ) makeup brushes
4 ) primer
5 ) foundation
6 ) concealer
7 ) beauty blender
8 ) setting powder
9 ) contour kit
10 ) bronzer / blush
11 ) Eye pencil
12 ) brow powder
13 ) Eye shadow primer
14 ) Eye shadow
15 ) Eye liner
16 ) mascara
17 ) lip balm
18 ) lip liner
19 ) lip stick / lip gloss
20 ) spray
Wannan sune abubuwan da kike bukata Idan
Kika shiga kasua domin siyan kayan Kwalliya
amma Idan baki da hali tou ba dole sai kin siya
dukan su
Ba sai dai akwai wanda suka zama dole kamar
su:
Moisturiser, foundation, Concealer, setting
powder
, eye pencil, eye Shadow, mascara, eye liner,
lipstick, makeup brushes da beauty blender.
YANXN ZAN KAWO KO WANNE DA YANDA
ZAKI YI AMFANI DA SU
1 ) CLEANSER : wannan amfanin sa shi wanke
fuska yanda zakiyi amfani da shi kuwa *zaki tsiya
a hannunki sai ki dan sa masa ruwa kadan
sannan ki mutstsika ki shafa a fuska amma fa ba
da Soso ba! sai ki wanke saqon hancin ki da
sama wajen gashin ki da rain idon ki domin sun fi
koma boye datti a fuska. Sannan ki dauraye da
ruwa ki sa towel mai kyau ki dan riqa daddana
fuskar ki a hankali har ki gama goge ruwan (ya
kamata ki siya karamin towel musamman dan
fuskar ki kuma ki riqa wanke shi kullum saboda
bacteria yana rage yawan kurajen fuska)
TONER : shi toner yana gyara maki fuska
musamman idan fuskar taki ta kasance mai
yawan quraje , pimples, ko kuma mai kala biyu
da sauran su yanda zaki yo amfani da shi shine
bayan kin wanke fuskan ki da cleanser sai ki
samu auduga mai tsafta ki tsiyaye toner din a jiki
ki goge fuskar ki lungu da saqo har si kin ga
babu sauran dauda sannan ki qara sa wani har
sai Kinga kin goge amma audugan bai chanza
kala ba (ban ce ki je kiyi ta durza fuskar ki ba
komai a hankali zaki yi).
2) MOISTURIZER : wannan ba wai ina nufin
Moisturiser da kike amfani da shi a jiki bane a'a
ina nufin FACE MOISTURIZER na musamman
zaki saya yanda zaki yi amfani da shi kuwa *
bayan kin goge face dinki da toner zaki bari ya
bushe (banda gajin hakuri) sannan ki dakko
Moisturizer dinki ki mutstsika a hannu sannan ki
fara tafa hannun ahankali a fuskar ki ko ya ko
ina kamar kina marin kanki amma fa a hankali!
Kamar kina taba kwai haka zakiyi tayi har sai
man ya shafu (hakan da kike yi zai sa pores
dinki silk bude yanda man zai saurin yin aiki a
fuskan ki) NOTE ba ko wane mai akeyi wa haka
ba wani zaki ga an rubta ajiki cewa ki shafa in
circular motion
Lastly duk abin da zaki siya ya zama Skin type
dinki ne in dai kina son jikin ki da kwalliyar taki
tayi kyau
Sai mun hadu a NEXT EPISODE insha Allah
WomenOfJannah

LET'S TALK ABOUT MAKEUP EPISODE : 4

Tags

iRashyder
LET'S TALK ABOUT MAKEUP
EPISODE :4
Assalamalaikum, previously munyi
Bayani akan dry, oily, combination
And dehydrated skin tare da remedies
Dinsu. Yau insha Allah zamu cigaba daga
Inda muka tsaya
SENSITIVE SKIN
Alamomin sa sune yawan bushe wan
jiki har da na wuce misali
2 ) yawan kuraje
3 ) pimples barkate
4 ) quna (zaki ga kamar kin kone )
5 ) tattare wan fata
6 ) kumburi
7) yawan yin maruru a fuska mai kama
Da pimples da sauran su.
Duk wannan alamomin sun fi nuna wa
A fuska da hannu sometimes da qafar ki
8 ) yana faruwa a ko wane irin skin type
Especially dry skin
REMEDY
1) Ki fasa kwai ki Cire york din ki
Yar ki zuba zuma chokali biyu a
Farin ki kwaba ki shafa a fuska
Idan ya bushe ki dauraye da
ruwan dumi weekly
2) ki kiyaye yawan yin kwalliya
3 ) ki daina kwana da kwalliya a
Fuskar ki kenan ki wanke face
Dinki tsab ki shafa masa vaseline
Idan zaki kwanta idan kin tashi
Ma haka
4) ki lura da abubuwan da jikin ki
Baya so ki chanxa (kamar su mai,
Body spray, pauda, foundation,
Cleanser da sauran beauty products
Dinki )
5) ki yawaita tsaftace jikin ki domin
Fatar ki mai raki ce ba komai take
So ba
6) duk abin da kika saya kika ga ya qare
Ki tou ki rike ingredients din dake
Ciki kina siyan makamantar su haka
Ma wanda bai amshe ki ba ki karanta
Domin guje wa makamantar su
7) ki daina yawan shiga rana ki riqa
Amfani da niqaf idan zaki fita da rana
8) lastly ki riqa yawan Shan rua idan zai
Yiwu ma kina tafasa ruwan ki sa a fridge
Idan yayi sanyi ki riqa sha .
Kuma banda yawan daye ciwo da
Pimples banda kuma yawan dora hannu
Akan fuska
RECOMMENDATIONS
Ki riqa amfani da kayan Kwalliya wanda
Aka rubta FOR SENSITIVE SKIN
kamar su :
OLAY Foaming wash for sensitive skin
BURT'S BEES sensitive eye cream
NEUTROGENA skin sunscreen for
Sensitive skin Da sauran su
NORMAL SKIN
Alamomin sa sune shi ba a bushe ba
kuma ba mai maiqo ba yana da kyau
Sosai
CONCLUSION
wannan sune skin types gaba daya kuma
Ya kamata ku San cewa idan dry skin
Gare ki to gashin ki ma dry hair ne don haka
kayan gashin ki kamar su Shampoo
zasu zama for DRY FRIZZY HAIR
haka Ma sauran skin types din. Allah
ya sa mu dace. Sai mun hadu a NEXT
EPISODE insha Allah
WomenOfJannah

LET'S TALK ABOUT MAKEUP EPISODE : 3

Tags

iRashyder

LET'S TALK ABOUT MAKEUP
EPISODE 3 :
Jiya munyi magana akan dry skin Da effects
dinsa da kuma irin yanda zamu
Magance sa. Sai dai bamu fadi abubua
Da ya kamata mai dry skin ya riqa ci ba
Tou gaskia ya kamata mai dry skin ya riqa
Yawan cin fatty acid kamar Omega-3 da
Omega-6 daga nau'in abinci daban daban
Kamar su kifi, man waken suya, gyada,
da aleho (spinach ) da sauran su wannan
Kenan a yayin da mai oily skin ya kamata
Ya rage cin abubua da suka gaji maiqo.
DEHYDRATED SKIN
Wannan is somewhat type of dry skin Sai dai
shi xai iya Kasancewa a ko wane irin skin type
domin shi yana faruwa ne saboda illar karan cin
rua a jikin dan adam wanda idan hakan ya
kasance
Tou akwai matsala alamomin sa sune
Bushe wan wani bangare na jiki kamar fuska,
kalan fitsarin ki zai chanza zua orange maimakon
yellow, ko kuma kiji fatar ki tayi taurin,
Yawan ciwon kai da sauran su
REMEDY
Wannan ba skin type bane ke kika gayyato sa
Don haka maganin sa mai sauqi ne matuqar zaki
Kiyaye domin idan baki kula ba zai ja maki
manyan
Cututtuka abinda zaki yi mai sauki ne
1) yawaita shan ruwa kofi 6 ko 8 a rana ( ba dole
sai ruwa zallan zai cika kofi 6 ko 8 din ba kamar
tea, coffee, kunu da sauransu )
2) ki daina yawan amfani da beauty products
(Kayan shafa wanda basu karbi fatar ki ba)
3) ki riqa yawan Shan fruits
COMBINATION SKIN TYPE
Yanda zaki gane kina da skin combination shine
your T zone wato tsakanin goshi, ido, hanci, baki
da gemun ki suna da maiqo especially idan kikayi
kwalliya amma kumatun
Ki da sauran jikin ki basu da matsala tou wannan
combination skin gare ki
REMEDY
1) ki sai madara (kar kiyi amfani da skimmed
milk ko semi skimmed milk ) ki sa a wuta yayi
tausa ki ajiye a gefe ya huce idan yayi sanyi zaki
ga kamar leda a saman sa sai ki sa chokali ki
yade shi ki sa a wani kwano
2)ayaba guda daya ki raba shi uku ki dauki daya
ki nuqa yayi laushi sai ki fasa masa kwai daya da
zuma rabin chokali ki
3)sannan ki dakko wannan man da kika yade ki
hada a cikin hadin ayaban ki dama shi da kyau
ya hade sannan ki shafa a fuskar ki idan ya
Bushe ki dauraye da ruwa mai sanyi kar ki goge
fuskar ki barshi ya Bushe a haka
ki fasa kwai ki Cire na cikin ki bar farin ruwan
sai kiyi ta kada wa har sai yayi kumfa yayi kauri
kamar zakiyi cake sai ki barshi Ki zuba yoghurt
chokali daya ki kwaba ki sha a fuskar ki for
15-20mins sai ki wanke da ruwan dumi .
Ki samu rose flower guda daya sai ki tsinke
petals din shi guda 6 kiyi squashing dinsa cikin
rose water chokali daya ki sa zuma rabin chokali
da yoghurt rabin chokali juya yayi laushi ki shafa
a fuskar ki for 6-10 mins ki dauraye da ruwan
dumi
Finally ki riqa siyan face lotion daban (man
shafawa na fuska kadai ) wanda aka rubta for
COMBINATION SKIN thanks sai mun hadu A
NEXT EPISODE insha Allah
WomenOfJannah

LET'S TALK ABOUT MAKEUP EPISODE : 2

Tags

LET'S TALK ABOUT MAKEUP
EPISODE 2 :
Previously munyi magana akan oily skin
Da irin yanda za'a gyara sa sai dai na
Mance ban fadi yanda zaki cire tissue
paper din a fuskar ki ba. Well, idan ya
Bushe zaki cire ki dauraye fukar ki
da ruwan sanyi sannan idan kina wanka
so biyu a rana tou daya ya
zamana na zallan Sabulu ne ba tare da
Soso ba kuma ruwan ya kasance mai
Zafi sosai amma fa ba ta yadda zai
qona ki ba.
Also zaki iya busar da bawon lemu sai
Ki yi blending yai laushi (gari) ki hada
Da madara ki shafa a fuska in circular motion
Idan ya bushe ki dauraye da ruwan sanyi
DRY SKIN TYPE : alamomin sa sune yawan
bushe wan jiki especially lokacin iska,
farfashewan baki, kyasbi (eczema) , jiki ya riqa
yawan yin saba (body pealing) , fuskar mutum
tayi fari pat kamar yayi dambe da gari, yawan
qaiqayi (itching , rashes, tsufa da sauran su
Actually irin wannan skin din ya fi kowane skin
type bukatar gyara domin duk wanda ya Taba ki
a ji zai kamar ya riqe ice ba a bushe kawai
amma kada ki damu everything will be alright
insha Allah amma sau kin dage
REMEDY
1 ki daina wanka da ruwa mai zafi domin yana
taimaka wa wajen tatse maiqon da ya saura
gareki
2)ki daina zama a cikin rana mai zafi
3)komai naki ya kasance mai tsaftace kuma mai
laushi especially kayan sawa
4)ki daina yawan exposing jikin ki (bayyana jiki a
waje ) ki na sa kaya masu dumi especially
lokacin iska
5)bakin Ki ko da yaushe ya kasance cikin mai ko
vaseline ko lip gloss mara kala ki ki yayi Jamba
ki na wani dan lokaci ko kuma daga kin gama
abun da zakiyi da Jamba kin ki goge ki sa lip
gloss DINKI
6)idan zakiyi brush da safe ki wanke har da lips
dinki domin zasu yi laushi kuma dead folicles din
zasu fita amma fa bane ki dirza da qarfi ba
7)ki riga yawan shafa yoghurt a fuskar ki ko
madara idan ya Bushe ki dauraye da ruwan sanyi
sosai
8)kada ki riqa yawan durge fuskar ki kuma kada
ki yawaita amfani da Sabulu da yawa
9 ki riqa yawan using products masu APRICOT
aciki most especially a gashin ki
10)ki siya QUAKER OAT ki niqa shi yayi laushi
sosai idan zakiyi wanka sai ki Diba chokali daya
ki zuba a kofi daya na ruwan zafi ki juya idan ya
narke sosai sai ki zuba a ruwan wankan ki juya
da kyau (ruwan wankan ki ya zama dalam dalam
komai sanyi
11)I dan kin gama kada ki goge jikin ki ki bare
skin naki yayi absorbing ruan zaki iya zuba
madara a cikin ruwan hade da oat din idan kin ga
dama (optional ).
12) Avocado (piya) ki cire bawon ki yar sai ki
dama yayi laushi ki shafa a fuskar ki in circular
motion (kina lailaya fuskarki a hankali) idan ya
Bushe ki dauraye da ruwa mai sanyi sosai
13)ki raba ruwan wankan ki biyu idan dan ki
gama wanka da daya sai ki shafa vaseline ko
man kade sannan ki watsa sauran ruwan a jikin
ki still in kin fito zaki shafa wani man
14)ki yawaita shafa wa fuskar ki da hannu da
qafar mai duk bayan ko wace salla domin sun fi
komai bushe wa a jikin ki
15)idan zaki shafa mai a fuska ki bayan ki sa
man a hannun ki kin mutstsika sai ki fara tafa
hannun ki duk biyun akan fuskar ki a hankali ko
ta ina har sai man ya shafu a haka
FINALLY
Ki na siyan beauty products wanda aka rubuta
FOR DRY SKIN ko kuma FOR ALL SKIN TYPES
kuma idan da hali ki riqa amfani da SHOWER
GEL maimakon Sabulun wanka
Kada kiyi treatment sau daya so biyu ki bari wai
ke baki ga changes ba a'a you need to give it
your all because without your skin you ar useless
sannan shekarar ki nawa kike da dry skin mayb
tun da aka haife ki don haka kar kiyi expecting
zai tafi da wuri amma I promise you in har kika
daure zai matuqar ragu ke kanki zaki ji dadin
kanki
Sai mun hadu A NEXT EPISODE insha Allah.
Women Of Jannah

NOW LET'S TALK ABOUT MAKEUP Episode : 1

Tags

iRashyder

NOW LET'S TALK ABOUT MAKEUP
Episode 1:

First of all kafin ki fara kwalliya akwai
bukatar NATSUWA sannan akwai
Bukatar LOKACI ina nufin enuf tym
Don haka ki tabbatar duk abun da zai
dauke maki hankali kin gama da shi.
Sannan akwai Bukatar sanin SKIN
TYPE of course ya kamata ki San skin
Texture dinki kafin ki fara siyan kayan
Kwalliya ko in ce kayan shafa ma gaba daya.
YANDA ZAKI GANE SKIN TYPE NAKI
OILY SKIN : ko da yaushe zaki ga
Fatar jikin ki tana da maiqo sannan
Kuma daga kinyi kwalliya zata narke
Ta lalace kiyi ta qyalli tou wannan ki
Riqa yawan yin facial mask da kwai
i mean ki samu tissue paper ki rufe
Fuskar ki da shi sai ki fada kwai ki
Cire york din kiyi amfani da blusher
(Makeup brush) dinki kina dangwalar
farin kwan kina Shafawa a saman
tissue papern da ke Fuskar ki.
2) kina yawaan goge fuskar ki da
lemon Ko lemun tsami before and
after makeup Also idan kina sou jikin
ki yayi laushi Yayi kyau zaki samu
farar shinkafa ki Nika yayi laushi kina
amfani dashi a matsayin scrub kafin ki
shiga wanka zaki jiqa da madara kafin
ki gama wanka ya dan yi laushi kadan
sai ki dauka ki cude jikin ki da shi
after 20mins Sai ki dauraye da ruwan
sanyi ko na dumi Dalam dalam ki sa
Soso ki dirje jikin Ki ba tare da kin sa
Sabulu ba.
3) ki kasance duk man da zaki saya
Ko Ince any body product dinki ya zama
An rubuta FOR OILY SKIN ko kuma
FOR ALL SKIN TYPES ba wai kawai
kamshin sa ya maki dadi ba ko Kuma
dan shi ake yayi ba also ba dan wance ta siya ko
yana da tsada ba
Lastly duk abun da na fada a wannan episode din
is for oily skin type idan jikin ki is not oily kar kiyi
amfani da ko wani remedy din nan sai mun hadu

A NEXT EPISODE insha Allah

Gyaran Jikin cikin sauki

Tags

Assalamu alaikum un uwa


ADO DA KWALLIYA
Assalamu alaikum wa rahmatullah. Last week
mun fara magana akan Ado inda aka ce idan
mutum na so yayi ado to Abu na farko da ya
kamata Ya fara gyara wa ita ce zuciyar sa.
zuciya kua ita ce halin mutum domin idan zuciyar
ki bata da kyau zai nuna a halayen ki da dabi'un
ki komai daren dadewa wanda alokacin kyawun ki
bazai amfanar da ke komai ba.
Haka nan kuma idan kikayi wa zuciyar ki ado da
alkhairi komai tsanar da mutum zai maki dole
akwai sashi na zuciyar sa da take mutumta ki
shakkar ki da kuma daraja ki kuma take kishin ki
tana Jin dama itace ke domin halayen ki bana
mutanen banza bane. Allah ya sa mu dace Amin
ADON GANGAR JIKI
Uhmm..... Mata akwai aiki!
Kada ki zauna tibis! Wai ke kin iya makeup
(kwalliya ) sabda haka ke baki da matsala no no
no no! Natural beauty matters alot in fada maki a
matsayin ki na mace yana da matuqar
mahimmanci a iya banbance fatar ki da ta namiji
a kallo daya, amma mu kam sai a slow walh
wata ma da za'a samu makaho a miqa masa
hannun mace da namiji sai yace mijin ne macen
tou yaji abu kamar katako Jiki duk tabo.. qafar
nan tayi kwatsa kwatsa, gashin kan nan nata
kamar ka bude masai, haqora ba kyawun gani
kumba tayi baqi fuskar nan tata....... Haba yar
uwa yanxn baki da wani excuse birni ko kauye
da zai hana ki gyara jikin ki.
Sai aikin kallon idian films American films da
sauran su basa amfanar dake komai.... tou wai
ance maki a banza suke sa qananan kaya su bar
jikin su a waje? Me yasa ke idan kin sa baya yi
maki kyau? Shin kou kin taba ganin stretch Mark
(nankarwa) a jikin su? Kin taba ganin tabbai
barkatai a jikin su? Ko kuwa dai basa gyara
gashin kansu ne? Qafar su yaya take? Hannayen
su yaya suke? Tumbin su fa? Shin kin taba ganin
ance muguwa ita taci riba a film? Koda zata ci
riba tou kuwa sai ta chanza hali. Haka nan idan
kazamiya ce sai ta zama mai tsafta no be so?
Tou kema ki dauka kullum film din kike yi amma
ta hanyar Allah da Manzonsa.
Don haka akwai abubua da kike buqata kafin kiyi
wa jikin ki Ado
ABUBUWAN BUQATA
idan kina sou ki gyara gangar jikin ki abu ne mai
sauqi amma kuma mai matuqar wahala sannan
yana buqatar hakuri da naci farkon abinda zaki
fara yi shine
1) ki yarda cewa KE MAI KYAU CE
duk abinda mutane zasu fada game da kamannin
ki kada ki damu ke dai kawai ki yarda cewa ke
din kyakkyawa ce domin Allah baya abu Marar
kyau ko ba haka ba? Kar ki yarda wani ko wata
su kira ki da mummuna ki amsa domin ke ba
mummuna bace. Don haka ki yarda da kanki sai
mutane su yarda da ke domin dai yanxn duniya
yanda ka dauki kanka haka mutane zasu dauke
ka
2) ki kasance mai SON KI
Hakan ba wai ina nufin ki kasance mai son kai
bane a'a... Ina nufin ki qaunace kanki sosai duk
abin da kika San zai cutar da jikin ki komai dadin
sa ki guje sa haka nan duk abin da zai amfani
jikin ki komai rashin dadin sa In dai bai saba wa
Allah da Manzonsa ba Tou ki rungume sa. Am
telling you zaki ji dadin hakan.
Wannan sune abubuwan da kike bukata kafin ki
fara gyaran jiki kar ki zama mace wacce komai
ta samu bakin ta kawai ta sani babu aji acikin
yin hakan ba zai amfanar da ke ga komai ba.
Yanxn zamu lissafa abubuwa wa'enda suke
buqatar gyara a jikin mu domin dai kullum tsufa
muke yi ba zama yara ba.
ABUBUWAN DA GYARAN JIKI YA QUNSA
Gyaran GASHI
Gyaran FATA
Gyaran FUSKA
Gyaran BANGAREN JIKI TA SAMA
Gyaran TUMBI
Gyaran BANGAREN JIKI TA QASA
Insha Allahu next Zan fara Bayani akan ko wanne
daga cikin abun da na lissafa tare da remedies
dinsa (yanda zaki Kiyaye sa) idan so samu ne
ma har da videos. Wslm
AdoDaKwalliya

GYARAN GASHI

Tags

iRashyder
ADO DA KWALLIYA
GYARAN GASHI
Kafin ki fara gyaran gashi akwai buqatar sanin
kalan gashin ki ina nufin type dinsa ba wai fari ne
ko baqi ba
DRY HAIR
Zaki ganshi ko da yaushe a bushe daga kin shafa
mai nan da kwana daya ya bushe fatar kanki fari
tas sometimes yana sa dandruff mai gari idan
rashin kulawar tayi yawa sanna gashin baya
tsawo yana saurin kakkaryewa. Wannan gashin
yafi kowane buqatar gwata sai kinyi da gaske in
har ba sou kike ki zama kwakwido ba at least
koda gashin bazai karu ba dai tou ba'a so ya
ragu
OILY HAIR
Zaki ganshi ko da yaushe cikin maiqo sannan
yana saurin jiqewa idan kin shiga rana irin
wannan gashin wari yake yi idan ba'a yawan kula
dashi especially idan akwai amosari ko kuraje
akan... Domin idan ciwo ya shiga cikin gashin
nan ruwa yake yi wanda hakan ke sanya wa
gashin wari
NORMAL HAIR
Wannan bashi da wani matsala zaki ganshi ba a
bushe ba kuma ba'a jiqe ba yana da kyau sosai
very fresh
COMBINATION HAIR
Wannan gashin yawanci zaki same sana qasan
(wato daga keyan ki xua kasa) yana da maiqo ta
saman kuma abushe ko kuma normal shima
wannan gawhin sosai yake buqatar gyara.
SENSITIVE HAIR
Wannan gashin bashi da kyau sam... Kuma rashin
gyara ne yake kawo shi tare da too much iyayi
komai kika samo ki laftawa gashin ki sai yazo ya
lalace kullum yay ta karyewa ga yawan kuraje da
amosari wani lokacin ma gashin zai zama dai dai
dai dai kamar dai mutum ya zauna ya irgasu.
Hakan yana faruwa a kowame launin relaxer na
lissafa a sama.
Wadannan suna kalolin gashin da muke dasu
gaba daya wanda akwai hanyoyi da yawa da zaki
gane irin su gareki da kuma yanda zaki magance
sa cikin sauki amma fa zai dauki lokaci sannan
kafin ki fara akwai buqatar ki san wannan
BANBANCIN SHAMPOO DA RELAXER
Mutane da yawa sun san banbancin su kazalika
mutane da yawa basu sani ba dan haka akwai
buqatar ayi masu uzuri.
SHAMPOO kamar sabulu ne na ruwa wanda ake
wanke kai da shi baya qara komai baya rage
komai sai dai idan anyi shi mussamman dan yayi
din. Wanda idan hakan ya kasance zaki ga an
rubta a jiki.
RELAXER wannan kuma wani mai ne mussaman
da aka kirkire sa don gyaran kai musamman ga
baqaqen fata mai gashi a cushe idan suna
buqatar gashin su ta kwanta tayi kyau kamar na
fararen fata sai suyi amfani da ita.
NATURAL HAIR
Idan akace natural hair ana nufun wadanda basa
sa relaxer (famin ko kumfar los.. Mama jugu jugu
da sauran su). Sabida rashin lokaci yau zanyi
bayanin yadda mai natural hair zata kula da
gashin ta idan Allah ya kaimu next week sai muyi
na masu sanya relaxer.
Da farko dai shin gashin mu na baqaqen Africa
gashi ne wanda yafi na ko wane ginsi kyau
lisabab... yana buqatar gyara sosai sabda
adunkule yake wanda hakan ke hana asalin
maiqon dake fatar kanki (natural sebum) wazuwa
har bakin gashin ki rashin faruwan hakan kuma
yana taimakawa wajen kakkarye gashin wato
sabo na fitowa tsoho na karyewa.
SHAMPOO
Zai dace ki bar amfani da ko wane irin shampoo
musamman wandanda suke dauke da sinadarin
SULFUR.. PETROLEUM DA SODIUM domin suna
dauke da sinadarin busarwa irim wanda ake
amfani da su a sabulan wanki omo da sauransu
don haka duk lokacin da zaki saya sai ki duba
ingredients din idan kuma yq zama dole sai kinyi
amfani dashi tou sai ki surka shi da ruwa daidai
adadin sa. 50-50 kenan ko kuma ki nemi MILD
SHAMPOO wannan bashi da chemicals masu zafi
sosai. Amma organics is the best option
ORGANICS
abun da ake nufi da organic shine natural abu
wanda ba'a yi amfani da wani harsh chemicals
(kemikal masu qarfi) wurin sarrafa su ba kamar
dai wasu nau'ika da nau'in abinci da ake
sarrafawa acire wani abu daga cikin sa
Yafi dacewa abun da ya kama daga man
shampoo conditioner man kitso da duk wani abun
da zakiyi amfani dashi a kanki ya zama natural
ko kuma organic Domin duk man da kika shafa a
fatan kanki yana shanyewa sannan jini ya tafi
dashi zuwa hantar ki daga nan kuma ya cigaba
da wanzuwa ko ta ko ina don haka yake da
matuqar mahimmanci kisan irin abubuan da zaki
na sawa a kanki saboda tsaro.
CONDITIONER
Shi conditioner ana amfani dashi ne dan a dawo
da taushin da aka rasa na gashi. Yanda ake
amfani dashi kuwa shine bayan kin gama
shampoo kin dauraye tas! Sai ki shafa
conditioner tun daga qasan gashinki zuwa bakin
sannan ki samu leda ki rufe gashinki ki daura
dankwali ki barshi na tsawon lokacin da suka
rubta a roban. Bayan nan sai ki wanke ki
tabbatar baki barko kadan a cikin gashin ki ba
don kar yayi maki illa.
Amma sau daya ake yin hakan a wata daga nan
du ranar da zaki wanke kanki baza ki sha shi a
fatar kanki ba gashin kawai musamman karshen
gashin (ina nufi. Inda kike kamawa da ribon)
Ga wadanda suke wanke gashim su kusan kullum
yana da kyau ya kasance duk lokacin da zaki sa
ruwa a kanki to kiyi amfani da conditioner ki
dauraye hakan zai sa gashin yayi maintaining
moisture dinsa sannan idan ya bushe sai kiyi
oiling (oiling yana nufin shafa mai lungu da saqo)
COMB
ki riqa amfani da qaton kum mai manyan haqora
ko kina da gashi ko baki dashi domin karamin
kumb yana tuge gashi
Sannan ki sayi daya safaya ki ajiye wajen sa da
ban saboda baki idan ba haka ba kullum aikin ki
baya xai riqa dawowa duk wani abun fa kike
amfani dashi a gashi ya zama naki ke kadai ko
ke da yaran ki. (Idan kina kula da gashin kansu
kenan)
OILING
Yanda zaki fiqa shafa mai akan ki shine ki riqa
sagawa kanana kina shafa mai daga fatar kanki
zuwa qarshen gashin har ki gama sannan ki
zauna kiyi ta massaging gashin kamar kina susa
kaikayi amma a hankali dan man ya natsu a ciki
idan na tsawon minti 30 ko awa daya ma idan
kin gama ki tace sannan ki qara shafawa bakin
gashin mai sosai.
Rashin shafa mai a bakin gashi shi yake kawo
karyewan gashi sabo na fitowa tsoho na karyewa
gashi baxai taba yin tsawo ba kenan.
PROTIEN TREATMENT
Yana da kyau ko wani wata ki riqawanke kanki
da kwai misali bayan kin wanke kai kin tsane
ruwan tas ya fara alaman bushewa sai ki fasa
kwai wasu suna amfani da farin ne kawai wasu
kwaiduwan (york) wasu kuma both duk dai wqnda
kika zaba sai ki shafa bayan awa daya ki wanke
ki dauraye da conditioner zai sa gashinki shining
(kyalli) da kyau . zaki iya hada kwan da ayaba da
madara wannan ma yana da kyau sosai ya kuma
qara bakin
Gashi. Amma fa kar kiga ya qarbe ki kije kiyi tayi
toh ba ruwana idan ya kakkabe gashin..... Sau
daya tak! A wata
SALOON
Ki dainq yawan zua saloon ana kona maki gashin
ki abanza yana karyewa gara kina gama wanke
kanki kiyi kalaba ki barshi yabushe washe gari ki
tsefe ki shafa masa mai
Idan kuma ya zama miki jiki amfani da kayan
wuta a gashi don warware gashi tou gara ki shiga
dryer (draya) yafi sauqi da rqwhin karya gashi
sannan kuma ki siya HEAT PROTECTION
SHAPOO, MOISTURIZER, SPRAY KO KUMA
SERUM ki fara sawa a gashinki kafin a fara
qonawa.
Ya kamata mu tsaya anan zan cigaba next week
insha Allah wslm.
AdoDaKwalliya

@arewashow

Gyaran jiki, da Hannu da Kafa

Tags

GYARAN JIKI, HANNU DA KAFA

Assalamu Alaikum muna godia da yabawa da
wannan gudummua da ake bamu Allah ya saka
da alkhairi ina son kayan gyaran jiki hannu da
kafa pls.

iRashyder
Wa'alakumussalamu warahmatullah....

GYARAN JIKI

Da farko dai shi gyaran jiki yana matukar bukatar
kulawa tare kuma da daukan lokaci. musamman
idan akace jikin is very dry. amma hausawa
sukace hakuri da dauriya shi ke kai mutum ga
samun nasara.

duk da cewa a farko zaki ga
kamar baya aiki amma duk inda kika dauki wata
daya, wata biyu, kina yi dole sai an ga chanji a
tare da ke.

akwai hanyoyin gyaran jiki kamar
haka

1-RUWA
Kamar yanda nasha fada shan ruwa da yawa yafi
komai muhimmanc ga rayuwan dan adam. rashin
ruwa a jiki yana sa jikin mutum ya bushe ya
tattare da wuri. rashin ruwa a jki yana sa saurin
tsufa da saurin kamua da cututtuka masu dama.

dan haka muke shawartan mutane da su rika
shan ruwa akalla kofi takwas zuwa goma a ko
wacce rana. sannan ruwan ya kasance
tsaftatacce.

2-WANKA
Yin wanka sau biyu a rana na daya daga cikin
manya manyan hanyoyin gyaran jiki
• Tsaftataccen ruwa, soso mai laushi, sannan a
yayin zaben sabulun wanka mutum ya nemi na
kalar fatar sa wato dry skin oily, normal skin ko
kuma for all skin types.

3- TAUSHIN FATA ( EXFOLIATE )
Yin wannan sau biyu zuwa uku a sati yana
kankare dattin jiki tare da kankare matattun cells
din dake saman fatan mutum wanda hakan ke
haifar da taushi tare da santsin fata. Zaki same
shi a shagon kayan kwalliya dauke da suna
kamar haka EXFOLIATING CREAM KO BODY
SCRUB sannan zaki iya hadawa a cikin gida
kamar haka:-

GA MASU YAWAN MAIKO A JIKI KO FUSKA
• Lemun tsami
• Suga ko gishiri
• Ki kwaba ruwan lemun tsami da suga kafin
sugan ya gama narkewa ki riqa deba gina goge
fuskan dashi.
• bayan minti 30 ki dauraye da ruwan sanyi. Sau
daya zuwa biyu a sati

GA MASU YAWAN BUSHEWAN JIKI
• Suga ko gishiri gwangwani daya
• Man zaitun ko almond ko man cika gida (castor
oil) rabin gwangwani
• Zuma kwatan gwangwani
• Lavenda oil ko wani mai kamshi chokali daya
• Ki hada su wuri daya bayan kin gama wanka ki
shafa shi ki dan dirje jikin ki dashi sannan ki jira
minti biyar ki dauraye da ruwa ki fito
• Wannan hadin zai kai tsawon sati biyu ba tare
da ya lalace ba.

GA WADANDA JIKIN SU IS NORMAL zasu iya
amfani da kowanne daga cikin wadannan biyun.

4-YAWAITA SHAFA MAI
Muatane da yawa basa son shafa ma ajikin su
suna ganin cewa ba wata damua to akwai
damuwa kokuma a shafa a kafa da hannu da
fuska kadai shi yasa lokuta da dama sai kaga
jikin mutum yayi dabbare dabbare ko ina kalarsa
daban. Please mu riqa amfani da man shafawa
masu kyau ban a bleeching ba. Idan kinyi amfani
da wannan baki ji dadin sa ba kar ki kuma sayan
irinsa ki nemi wani har sai kin samu wanda kka ji
dadin sa daga nan sai ki cigaba da siyan irinsa.

Sannan ya kamata mu san wannan:-

• BODY CREAM KO BODY LOTTION wannan a jiki
kadai ake shafawa banda fuska shafa shi a fuska
zai iya kawo matsala kamar na kunan rana,
kuraje, da sauran su.

• FACE AND BODY CREAM\LOTTION wannan
zaki iya amfani dashi a jiki da kuma fuska baki
daya.

• FACE \ FACIAL CREAM wannan fuska kadai
• Da sauran su. Al muhim dai mutum ya karanta
jikin mai sosai sannan ya duba kwanan watan da
man zai lalace wato expiring date kafin ya saya.

5-KARE JIKI DAGA RANA
Rashin shiga rana yana daga cikin abinda yasa
jikin yara yake da taushi da sheqi. Don haka duk
lokacin da mutum zai fita ya riqa yawan amfani
da sun protecting cream (SPF) ko kuma ki sanya
nikabi.

Musamman ga mata masu amfani da man
bleachin rana zai iya kona fuskar ta zama ja idan
basa neman kariya daga rana.
BONUS RECIPES

SANTSI DA SHEKIN FATA
• Aloe vera gel chokali daya
• Kurkum rabin karamin hakali
• Zuma chokali daya
• Madara chokali daya
Ki kwaba su gaba daya ki shafa daga fuska zuwa
wuyan kin a tsawon minti 20-30 ki wanke da
ruwan dumi.

NA BIYU ZAKI SAMU
• Gwanda ko kabewa dan kadan
• Garin sandal karamin chokali
• Zuma chokali daya
Ki kwaba sosai ki shafa na tsawon minti 20-30 ki
wanke da ruwan sanyi.

NA UKU ZAKI SAMU
• Ruwan rose (rose water)
• Bayan kinyi wanka da safe da daddare ki rika
shafa shi yana bushewa ajikin ki kafin ki shafa
mai

YANDA AKE HADA ROSE WATER

• Zaki samu fulawan rose ki tsitsigeta ta kai
kaman kwatan kofi sannan ki sa ruwa sama
sama ki dauraye ta

• ki dauko tafasashen ruwan ki da ya huce rabin
kofi ki tace ki zuba a roba mai tsafta

• sannan ki zuba furen acikin ruwan ki rufe ki
lullube shi ckin kaya mai duhu na tsawon kwana
uku

• ki juye a tukunya mai tsafta ki dafa har sa
kinga kalar furen ya bace sannan ki sauke ki
tace ruwan.

Ki bari yayi sanyi sannan ki fara amfani dashi.
Wannan hadin zai kai tsawon wata daya baiyi
komai ba matukar an hada shi da ruwa mai kyau.

A gaba zamuyi bayani akan amfanin rose water
inshaa Allah.

GYARAN HANNU DA KAFA
TAUSHIN HANNU
Ki nemi hand cream mai kyau ko kuma

• ki nemi man kwakwa ki ajiye a kusa duk lokacin
da kika gama wani akin gida ki daraye hannun ki
ki sha da daddare ma haka kafin ki kwanta.

• Ki nemi man zaitun ki kwaba da suga ko gisiri
ki riqa goge hannunki da shi sannan ki shafa mai
ki sa safan hannu ki fara aikin ki.

TAUSHIN KAFA

• Ruwan dumi kisa man kwakwa kadan a ciki ki
tsoma kafarki bayan ruwan ya huce sai tsame
kafar ki sa dutsen goge kafa sama sama kid an
goge fatar da suka taso sannan ki dauraye ki
goge da tawul ki shafa man kade ki kulle da leda
ki sa safa (musamman ga masu kaushin kafa)

• Yawaita shafa wa kafar mai har tafi zai taimaka
wurin lausasa ta.

ALLAH SHINE MASANI………. ALLAH YASA MU
DACE AMIN.

AMFANIN MAN TAFARNUWA DA IZININ ALLAH

Tags

DAGA WANI BAWAN ALLAH FISABILILLAH*******√

AMFANIN MAN TAFARNUWA DA IZININ ALLAH

1. Yana yaki da kwayoyin cututtuka masu shiga
jikin 'Dan Adam. Kakkarfan Anti Biotic ne.
2. Yana maganin MIYAGUN ALJANU masu shiga
jikin Mutane.
3. Yana maganin ciwon daji (Cancer) na ciki da
waje.
4. Yana maganin Maruru da kuraje ko gyambo
daga jikin Dan Adam.
5. Yana hana MAITA tasiri ajikin 'Dan Adam.
6. Yana maganin Gyambon ciki (ULCER) da
ciwon Qoda da Appenditix.
7. Yana Zabgewa Cholesterol daga jikin Dan
Adam.

8. Yana maganin Sanyin Qashi, da Zazzabin
Qashi, da Kumburin Jikin Dan Adam.

9. Yana maganin ciwon Ido Musamman irin
wanda ya dade bai warke ba. Idan ana digashi
acikin ido yayin da za'a kwanta.

10. Yana maganin Qaikayin jiki, Kyasbee,
Amosani, da sauran cututtukan fatar jikin 'Dan
Adam.

Wassalatu Wassalam 'ala Rasulillah (saww).

Amfanin Dabino (Date fruits)

Tags

AMFANIN DABINO (Date fruits)

***************
Dabino yana daya daga cikin
kayan itacen da Annabi (saww) ke so.

1. Yana saurin narkarda abinci
2. Yana Sanya kuzari yayin Ibadar Aure
3. Yana taimakawa wajen kara jini
4. Yana taimakawa Ma'aurata maza/mata
5. Yana Maganin Basir Mai sa tsugunni a bayi. 6.
Yana karawa Ido lafiya
7. Yana Rage Nauyin kiba da teba.
8. Yana Maganin Gudawa
9. Yana Saurin Saukarda Hawan jini
10. Yana taimakawa kwakwalwa wajen Samun
basira..
11. Yana kariya daga Sihiri
12. Yana taimakawa Mata masu ciki dan samun
sauqi wajen
haihuwa.
13. Yana kariya daga Sihiri.

**YADDA ZA'AYI
AMFANI DA DABINO.

CIWON NONO GA WACCEN DA TA
HAIHU;
Anacin dabino guda 7 asha man
tafarnuwa karamin cokali sau 1
arana kwana uku.

**DOMIN SAMUN NI'IMA GA MA'AURATA;
Ana daka dabino a zuba cikin madara (freesh
milk) sannan a saka Zuma a ciki a sha awa daya
kafin a kwanta. GA MATA MASU JUNA BIYU;
Ana cin dabino kwara bakwai kullum da safe idan
anyi kusan haihuwa Wannan yana hanawa
macce yawan zubar jini lokacin haihuwa da iznin
Allah.
**GUDAWA;
Ana daka garin dabino a saka a
ruwan zafi a sha In shaa Allahu
yana tsayar da gudawa.

**SAMUN KUZARI;
Ana cin dabino guda ukku a sha zuma cokali 1
da safe da yamma.

**SAMUN LAFIYAYYAR FATA;
Ana hada garin dabino da zuma da man zaitun a
shafa a fuska awa
daya sai a wanke fuskar da ruwan zafi wannan
yana saurin gyara fuska.

Bin cike ya nuna Yawaita cin dabino na hana
kamuwa da ciwon
CANCER ko wacce iri.
**Haka Kuma MANZON ALLAH (saww) YACE
DABINO AJWA YANA MAGANIN DUKKAN
CUTATTUKA, KUMA DUK RANAR DA
KACISHI,BABU WATA
CUTA DA ZATA SAMEKA AWANNAN RANA, KO
KUMA SAMMU KO SIHIRI.

Wasu MALUMMAN MUSULUNCI kuma sunce
Annabi (saww) Yana
nufin kowanne dabino ba wai sai
Ajwaba (Wallahu A'alam)

SIRRIN GYARAN JIKI BY MAMAN SAFWAN

Tags

Bismillahirrahamanirrahim

(Wasallallahu ala sayyadina maulana Muhammad annabiyul ummiey wa ala alihi wasallam)

Barkan mu da kara kasancewa awannan shirin

SIRRIN GYARAN JIKI BY MAMAN SAFWAN
NIDAI YAKAMATA NAKARANTA DOMIN
GYARA JIKINA
KEMA YAKAMATA KIKARANTA DOMIN GYARA
JIKINKI

_Yar uwa ki wanke aya ki shanya ta bushe ki
gyara ridi shima ki shanya sai ki goge kwakwa ki
shanya ta bushe sannan ki samu mazarkwaila ki
hada su waje daya ki dake su ki dinga diba kina
sha da madara ko nono.....yar uwa zaki bada
mamaki

_*HADIN ZUMA*_

Zuma
Hulba
Habbatus sauda
Yar uwa ki samu zumar ki,ki hada da garin
habbatus sauda da hulba ki kwaba sosai sai ki
sha safe da yamma ni'ima kam ba'a cewa komai
zaki ga abinmamaki
_*Yar uwa ta ga wani sirri*_

_*TSAKIN KUKA*_

_Ki samu tsakin kuka ki dinga tsuguno dashi
wato ki samu gaushi ki zuba a kaskon wuta ki
samu tsakin kuka ki barbada sai ki tsuguna akai
yana matse gaban mace sannan yana hana warin
gaba da hamami_

_*BAGARUWA*_

_Ki samu bagaruwa ki nika ta tayi tausi sosai sai
ki samu zuma da almiski ki kwaba sai ki dinga
matsi dashi zaki sha mamaki yar uwa ta_

_*LALLE*_

_Ki tafasa lalle sai ki dinga zama a ciki kiyi
kamar minti goma ko sha biyar zaki matse_

_*SAIWAR KANUNFARI*_

_Ki tafasa shi sai ki dinga tsarki dashi amma da
dumin shi_

_*HULBA DA GAYAN MAGARYA*_

_Ki tafasa su sai ki dinga zama a ciki kiyi kamar
minti goma ko sha biyar a ciki yana matse gaban
mace sosai kuma babu illa sannan kuma yana
maganin infection_

*_GANYEN NA'A NA'A_*

_Ki dinga tsuguno dashi yana hana warin gaba da
kuma infection_

_*HULBA DA HABBATUS SAUDA*_

_Ki samu garin hulba da habbatus sauda mai
laushi sosai ki kwaba su da zuma ki dinga matsi
dashi_

_*GARIN ZAITUN*_

_Ki samu garin zaitun mai laushi ki kwaba da
mankade ki dinga matsi dashi zaki sha mamaki
yar uwa_

_*DABINO DA KANUNFARI*_

_Ki bare dabino yar uwa ta ki samu kanunfari sai
ki jika su a gora ko roba ki bari su jiku sosai sai
ki dinga sha safe da yamma wannan hadi yana
saukar da ni'ima sosai_

*_GANYEN MAGARYA DA MADARA_*

_Ki samu garin magarya ki zuba a madarar ruwa
ki sha zaki samu ni'ima sosai_

*GYARAN JIKIN AMARYA*

_*GYARAN FATA*_

_*GA YANDA ZAKIYI*_

Idan kamar saura wata guda kiyi

*AURE*

sai ki
rage yawan shiga rana dan kuwa da wuya ki dai
na shiga rana gaba daya idan kamar saura sati
biyu bikin ki to yar uwa ta sai ki samu *Kurkur*
*Madara*
*Kwai*
*Dilka*
*Zuma*
*Lemon tsami*
*Majigi*
*Turaren gaf gaf*
Yar uwa ki hada kurkur da madara da kwai ki
kwaba su waje daya sai ki shafe duk jikin ki
dashi sannan ki barshi yayi kamar awa biyu sai ki
samu hankici me kyau ki samu ruwan dumi ki
goge fuskar ki a hankali sai ki shiga wanka da
ruwan dumi ki wawatsa ruwa a jikin ki amma kar
kiyi amfani da soso da sabulu in kin fito sai ki
samu dilka ki zuba ruwan zafi ya narke sosai
sannan ki zuba zuma ki kuma matse lemon tsami
a ciki ki shafe duk jikin ki da shi sai ki turara jikin
ki da turaren gafgaf zuwa minti talatin sannan
kuma ki shiga wanka da sabulu babu soso haka
zaki dinga yi kullum har zuwa lokacin bikin ki
zaki ga yadda jikin ki zai goge yayi matukar kyau
daga.

TASKAR MAMAN SAFWAN
MUNA SAIDA MAGUN GUNA INGANTATTU
DOMIN,

GYARAN JIKINKU MATA,

KAMARSU
;MAGANIN GYARAN NONO CIKOWARSU,

GIRMA
NSU DA KUMA TSAIDASU,MAGANIN
MATSI,

TSUMI,AYU,ZUMA,DILKE HUMRA,DAKA
NA MATA GUMBA DA DAI SAURAN SU.DUK MAI
BUKATA YA TUNTUBI WANNAN LAMBAR;


@www.arewashow.tk

Call or whatsapp 08184879701

HausaNovel: KE DUNIYA Complete

👉🏻 🌎 *KE DUNIYA* 🌎👈🏻




*Written &  story by*
*Zee Elkaseem (Mmn khady)* 😘




page 1---5



*Just a short story*




*Amincin Allah ya tabbata A gareku masoyana Aduk inda kuke* 🙏🏻

💃🏻 *Allah yanufeni nayi dawowa dawata tsaraba dan faranta Ranku masoyana*❤





✍🏻 Zaune take kan kujera a faffad'an tsakar gidanta ta buga uban tagumi da hannu biyu, ba abinda take tunani sai yanda Halin mijinta ya canca cikin kwanakin dabazasu wuce kwana 30 ba,

Maganar arzi'ki bata had'asu kullum cikin tashin hankali suke, fitinar yau daban ta gobe daban, duk iya 'ko'karinta na ganin ta kaucema rigimarsa amma abin yaci tura.

"Assalamu Alaikum" 'yan'matan suka had'a baki gurin yin sallama, ganin Maman tasu tsakar gida zaune kuma bata amsa sallamarsuba, bai basu mamakiba, dan sunsan cikin halin damuwar datake ciki.

Hafsa ce tanufi d'aki dan ajiye jikkar islamiyyarta, tare da cire zundumemiyar hijab d'inda ke jikinta, itama Amina bin bayanta tayi Al'qur'anin dake hannunta ta ajiye itama ta cire hijab d'inta tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, suma 'yan'matan kallo d'aya zakayimasu ka tabbatar da suna cikin damuwa.


Tare suka fito zuwa tsakar gidan har yanzu mamansu tana inda suka barta, wannan karon hawayene sharkaf a fuskarta,

Cikin tsananin tashin hankali suka iso gareta, suna gogemata hawaye, Hafsa cikin muryar kuka take magana "Mama kiyi ha'kuri dan Allah, ki d'auki wannan amatsayin kaddara, kuma inshaAllah kome zai wuce kamar ba'ayiba"

Girgiza kai mamantasu tayi tare da jawo 'ya'yan nata ajikinta ta rungumesu hawaye na suntiri akan fuskarta cikin sheshshekar kuka tace  "Hafsa nagaji da Halin mahaifinku, nayi bakin 'ko'karina na ganin na kaucema duk wani rashin jituwa da zai shiga tsakanina dashi amma abun kullum gaba yakeyi, yau harta kai ga mahaifinku ya d'aga hannu ya dokeni,"
s
Su duka d'ago Kansu sukayi a firgice suka kalleta, sai lokacin suka lura da yanda fuskarta dukta kumbura alamar buguwa, "Innalillahi Amina tari'ka maimaitawa, " mama yanzu babane yamaki wannan dukan, munshiga ukku suka fad'a tare da fashewa da kuka,

Kuka sukacigaba  dayi suduka ba mai rarrashine wani saida sukayi mai isarsu, sannan sukayi shiru dan Kansu,

Jin anata kiraye-kirayen sallar azahar yasa suka tashi suka d'aura Al'walla suka shiga d'aki,
'Katuwar dadduma suka shimfid'a sukayi sallah sundad'e suna kwararo addu'a akan Allah yayi masu maganin matsalar dasuke ciki sannan suka tashi.

Hafsa da Amina kuwa kitchen suka nufa dan wata fitinanniyar yunwa sukeji,
Basu samu wani abunciba a kitchen d'in haka yasa suka dawo d'aki dan tambayar mamansu.

Halin dasuka isketa cikine yayi masifar d'aga hankalinsu, Dan kwance take tanata magowa ta dafe 'kirjinta da hannu biyu,

Da sauri suka isa gareta tare da tallabo kanta suna kuka, suna fad'in innalillahi wa,inna'ilaihirraji'un" Hijab dinda ke 'ko'karin sha'ke wuyanta saboda yanda take magowa suka ciremata, lokacin ta had'a wata uwar zufa kamar anmata wanka da ruwan zafi, wani yunkuri tayi mai 'karfi tare dayin Amai.

"Innalillahi" suka furta atare lokacin da saukaga aman da mamantasu tayi jinine hada gundari.

Da gudu Amina tafita tana Neman taimako, cikin sa'a kuwa tasamu makwabcinsu Alh shu'aibu mutumin kirkine duk unguwar ana yabonsa saboda kyawawan halayensa,

Shitagayama halinda mamansu take ciki, cewa yayi taje gida gashinan zuwa, matarshi Haj Zainab yafara turawa dan taimakama marar lafiya.

Tana shiga ta iske halinda Halima take hankali tashe ta kamata suka fito lokacin Alh shu'aibu ya fiddo mota suka sanyata sai *federal medical center* dake cikin garin Emergency aka nufa da ita, saida aka d'auki kusan awa 5 da ita a emergency sannan tad'an dawo hayyacinta I.c.u aka maidata dan har yanzu jikin nata sai ahankali.







Comments dinku shine zai 'karfafamin gwiwa, amma idan babu comments zan dakata 🤷🏻‍♀
👉🏻 🌎 *KE DUNIYA......* 🌎👈🏻
       



*Written &  story by*
*Zee Elkaseem (Mmn khady)* 😘




page 5---10



*Just a short story*




Hafsa da Amina kuwa tunda aka fita da mamansu zuwa Hospital suketa rizgar kuka kamar ransu zai fita.

Da misalin 'karfe Hud'u na yamma Alhj Sani yayi sallama yashigo gidan, bai ko kalli d'akin matar tashiba yawuce d'akinshi dan yanzu baya 'kaunar ganinta ko kad'an.

Jin sheshshekar kukan dake tashi a gidan yasa yaji wani kududun bakin ciki ya turni'kesa dan a zatonshi Halimace matarshi ke kuka dan yasan duk randa ya6ata mata rai yini take kuka.

Cike da bala'i yafito daga d'akinsa zuwa d'akinta da niyyar ya saukemata kwandon bala'i,

A sukwane ya isa ya yaye labulen  yafad'a cikin d'akin.

Da sauri Amina da Hafsa suka d'aga jajjayen idanunsu suka kalleshi, shima wani fad'uwar gaba yaji ganin yanda 'ya'yan nashi suka fita hayyacinsu cikin 'kan'kanin lokaci.

Tambayarsu yayi zuciyarsa cike da fargaba,

Aminace tayi 'karfin halin gayama Baban nasu Halinda mamarsu take ciki.

Hankali tashe yakira Alhj shu'aibu ya tambayeshi Asibitin dasuke,

Da Sauri ya watsa ruwa ya canja kaya, yacema su Hafsa zaitafi hospital d'in.

Suma mi'kewa sukayi suakace "baba Dan Allah kaje damu"

Kallonsu yayi cike da tausayawa yace "to Ku shirya mutafi" cikin minti 5 sun shirya

Mintuna da basu wuce 15 ba suka sadasu da Asibitin da aka kwantar da halima, suna zuwa kai tsaye d'akin da aka kai Halima suka nufa Dan Alhj shu'aibu ya gayamasu tana I.C.U


Wani matsanancin kuka Hafsa da Amina sukeyi lokacin dasuakyi arba da mahaifiyarsu kwance kan wani gado jikinta duk na'ura hatta da babban yatsanta na hannu an ma'kala na'ura, wani irin kuka suke mai ban tausayi, Alhj Sani kuwa duk illahirin jikinsa kyarma yake hankalinsa tashe ganin halinda matarsa take ciki.


Hajiya Zainab kau matar Alhj shu'aibu ha'kuri kawai takebasu, dan ko ita kanta ta tsorata da halinda Halima take ciki.


Wani yunkuri Halima tafara sai aman jinin take, dagudu Amina da Hafsa suka nufi gurinta suka rungumeta suna kuka, shima Alhj Sani kukan yake kamar 'karamin yaro,

Hajiya Zainab ce tayi 'karfin halin kiran likita ta shaidamashi abinda ke faruwa, da Sauri likita ya shigo d'akin umartarsu akayi dasu fita, amma Hafsa da Amina basuda niyyar fita kuka kawai suke suna kara rike mamansu da kyar aka fiddasu aka rufe,

Nanfa likita yafara aikinsa yi yake, amma ina abun ba sau'ki, wani salati Halima tayi da 'karfi Wanda duk wani Wanda ke kusa yaji salatin, sannan rai yayi Halinsa.





Fad'in tashin Hankalin da Hafsa da Amina suka Shiga bai misaltuwa Alhj Sani kau kamar wani zautacce haka Yakoma, Hajiya Zainab ma tayi kuka dan tayi rashin ma'kociya tagari.

Haka aka d'auki gawar Halima zuwa gida akayimata wanka aka kaita gidanta na gaskiya, dan ko 'yan uwanta basu samu halartar jana'izartaba sakamakon nisa dake akwai, sai washe Gari suka samu isowa.

'Kanwar Halimar sai yayarta Hajiya Asabe, sai yayyenta maza guda 3, haka akayi zaman makoki bayan kwana ukku mazan suka tafi bayan anyi addu'a sukabar matan dansu sunce sati zasuyi.





*             *             *          *




Bayan sati d'aya Zazzaune suke kowanensu yayi jugum, Alhj Sani kuwa shima zama yayi yana sauraron abinda Hajiya Asabe zata gayamashi dan ita tasa aka kirashi.


Cikin tsananin jimami da *Alhini* Hajiya Asabe tafara magana "to Alhj sani mudai gobe tunda asuba mukeso mud'au hanyar gida, saboda haka nake ro'konka dan Allah kabamu Hafsa da Amina mutafi dasu gurinmu muri'kesu badan muna tunanin zaka gaza dasuba, a'a"


Gyara zama Alhj Sani yayi sannan yace "Hajiya dan Allah kuyi ha'kuri bazan iya rabuwa da yarana ba, dan muddin narabu dasu abin zemin yawa dame zanji da rashin mahaifiyarsu koda rashinsu" yana kaiwa nan yafashe da kuka, kamar wani 'karamin yaro, ganin haka yayi bala'inba Hajiya Asabe tausayi, dole suka ha'kura suka barmashi yayanshi.

Washe gari tunda asuba suka d'au hanya,  Hafsa da Amina kuwa a ranar wani sabon kuka suka dasa.






🤒😎
👉🏻🌎 *KE DUNIYA...* 🌎👈🏻
_(Rumfar kara)_




*Written & story by*
*Zee Elkaseem (Mmn khady)* 😘




Page 10---15



*Just a Short Story* 👌🏻






Hafsa da Amina kuwa sunaji suna gani su Hajiya asabe suka tafi suka barsu, harga Allah sunso subi dangin mahaifiyarsu, amma ba yanda zasuyi tunda mahaifinsu bai aminceba.

Wani sabon kuka suka dasa kamar yaune mamarsu tabar DUNIYA,
Alhj sani daga d'akinsa yake jiyo sautin kukansu har cikin ransa yakejin kukan nasu, ba kamar Hafsa, waccs yake masifar so da 'kauna.

Zuwa yayi yajawosu ya rungumesu jikinsa, shima kukan yake kamar wani 'karamin yaro,

Ahankali ya zame Amina daga jikinsa ya 'kara 'kan'kame Hafsa yana maida wani irin numfashi,
Matseta yayi sosai a 'kirjinsa yana d'an bubbuga bayanta Alamar rarrashi, ita kuwa Hafsa tsorone ya mamaye zuciyarta jin wani Al'amari Wanda bata ta6a jiba,

'Ko'karin kwatar kanta tafarayi lokacin dataji wani abu na tokareta, amma Alhj Sani ya ri'keta gam duk illahirin jikinsa kyarma yakeyi.

Da kyar Hafsa ta kwace kanta tanufi d'aki da gudu tafad'a kan gado tare da faahewa da kuka mai cin rai,
Rarraahinta Amina tari'akayi dukda itama hawaye ne kwance a idanunta.

Alhj Sani kuwa d'akinsa yanufa jikinsa duk ba kuzari, zama yayi gefen gadonsa tare da rafka uban tagumi.


*Asalin su*

Alhj Sani da Halima sunyi auren saurayi da budurwa, inda Alhj Sani yahad'u da halima a 'kasarsu ta Niger babban birni yamai, lokacin daya raka abokinsa sayen wasu kaya.

Soyayya mai 'karfi tashiga tsakaninsu,

Lokacinda Halima ta gabatar da Alhj Sani amatsayin mijin datakeson aure gurin babban yayansu Wanda yakasnce shine uwa da uba agaresu itada yayarta hajiya Asabe da 'kanwarsu, bayan rasuwar iyayensu.
'Kin amincewa yayi dan yana ganin Nigeria yayi nisa.

Amma Halima tadage akan ba Wanda takeso sai Sani, haka aka ha'kura aka auramatashi

Alhj Sani cike da farinciki yataho da matarsa zuwa gida Nigeria a garin katsina karamar hukumar musawa.


A babban gidansa ya tare wanda ya kasance mallakinsa, 'katon gidane  Wanda idan kashigo wata haraba zaka iske mai d'auke da shuke² hadda shukar banana, daga nan zaka shiga 'karamin zauren dazai sadaka da tsakar gidan wanda ke d'auke da tsararrun d'akuna guda hudu, wanda ukku suke rukuni d'aya, yayinda d'aki daya yake gefe Wanda ya kasance shine d'akin mai gidan.

Gefe guda kuma kitchen ne kusadashi kuma madai-dacin store, sa daga can gefe sosai kewaye guda 2 dana wanka dana bahaya.

Alhj Sani da matarsa Halima suna zaune cikin mutunci da mutunta juna saboda Halima macece mai matu'kar ha'kuri shiyasa ko cikin Unguwa batada abokin hayaniya

Cikin Shekara takwas da aurensu Allah ya azurtasu da yara biyu mata Hafsa da Amina Hafsa Nada shekara hudu aka haifi Amina daga lokacin kuma basu kuma samun haihuwaba.

Haka suka rugumi 'yayansu suna matu'kar nuna masu soyayya.

Bayan shekara sha hud'u Hafsa nada shekara sha tara yayinda tayi shekara d'aya da kammala secondary dinta, Amina kuwa wannan shekarar tagama tanada shekara sha shidda.

Hafsa takanse kyakkyawa ajin farko dan duk wata sura ta mahaifiyarta ta d'auko,  tanada cikakkiyar Halittar da duk namijin daya ganta dole ya kwad'aitu da ita, Amina ma ba daga bayaba, sai dai ganin Hafsa baisa aga dirin jikinta duka fatarta tafi ta Aminar Haske.

Halima duk lokacin data kalli Hafsa gabanta yakan fad'i tari'ka tunowa da gwagwarmayar datasha da maza saboda sura da dirin jikin da Allah yabata, to gashi Hafsa tabiyota sak harma tanaso ta zarceta, dan Hafsa tanada Breast sosai.

Hakan yasa ta tunkari Alhj Sani da shawarar yakamata su aurar da Hafsa tunda harta shekara da gama makaranata kuma ga 'kanwartama ta gama wannan shekarar kuma Alhmdlh sun sauke Al'qur'ani.

Shuru yayi na wani lokaci sannan ya sauke ajiyar zuciya "kibari zanyi shawara.








Kucigaba da kasancewa dani yanzu lbrn yafara 🤝🏻
👉🏻🌎 *KE DUNIYA...* 🌎👈🏻
_(Rumfar kara)_




*Written & story by*
*Zee Elkaseem (Mmn khady)*😘





Page 15---20





*Just A Short Story* 👌🏻





Yau kimanin wata hud'u kenan da Halima tayima Alhj Sani magana kan a aurar da Hafsa Amma tunda yace sai yayi shawara har yanzu bai 'kara tada zancenba.

Itako halima kullum hankalinta tashe yake ganin yanda Hafsa ke 'kara bun'kasa hip's d'innan nata sai